Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 12

Sponsored links

Haka sukai zama kamar na kurame a ɗakin har sanda Imran ya dawo da kaya niƙi Niƙi kayan jaririyar kusan kala Goma sai auduga da su pampers tare da madara haka ya dire Ummah sai faman yi masa sannu take wanda bata ma Amatullah kamar hakan ba, Dan ita ko arziƙin sannun ma bata samu ba sabida takaicin Maganar da Imran ya gayawa Ummah a waya har yau bata saki zuciyarta ba.

Haka Amatullah ta miƙe tare da taimakon Nurse Ɗin ta shiga Toilet ta gyara jikinta ta fito Nurse ɗin ce ta gyara Babyn wajan azahar ya kawo musu abinci mai rai da lafiya ummah sai saka masa albarka ake Kuma babu wanda ta shaidawa Amatullah ta haihu daga Cikin Gidan har zuwa Danginta haka suka kwana a asibitin washe gari aka basu sallama.

Imran yaso Su wuce da ita gidansu amman Ummah taƙi tace tai zamanta a ɗakinta.

“Ummah to waze zauna da ita ke ga marar lafiya?”

Cewar Imran wanda wannan furucin sai da ya bawa Amatullah kunya amman ummah mursisi tai da idanu tace zata dinga asubanci tana zuwa.

Koda suka koma ba laifi ta gyara Amatullah tsaf ta wanke jaririya ita Kuma amatullah daman babu batun wanka amman ta samu gyara mai kyau wajan Ummah koda ta koma gida ma da zata dawo ta zo mata da Maganin wanka wanda zata ke sha.

Sai dai me a kwanaki Biyu Amatullah ta sami sauƙi wajan Imran wanda zai zo su gaisa amman bai taɓa ɗaukar yarinyar ba, Sai dai ya rage mata cin zarafin da yake mata Kuma abun mamaki babu wanda yazo mata barka da sunan ɗan uwan shi.

A kwana na uku ne ya soma tsiro da sabon cin mutunci wanda zai zauna a falo yana zuba mata habaici akan kwaɗayin mahaifiyarta tai kuka ta godewa Allah amman da Ummah tazo sai yayta nan nan da ita yana shirga ƙarya kamar ragowar yaƙi.

Yau kwana Biyar da haihuwa Ameerah tazo gidan sosai takewa Amatullah faɗan cewar ta haihu bata gaya mata ba sai Jiya suka ji wajan Hassan ƙaninta Mamaki Amatullah tayi don laifin Ummah ne ba nata ba wannan zuwan na Ameerah tai mata kitso da ƙunshi sannan suka gyara gidan washe gari Maman su Ya Ahmad dasu Anty suka zo don Mama ce ma taiwa Babyn wanka, Dan ita mama barta da rashin son magana wadda ta zame mata kamar Izzah amman babu ruwanta da Munafurci kamar na sauran matan gidan.

Don tana kallon Anty babar su Ameerah na nuna mama da ido wa Matar kawu, Amman maman bata ɗaga idanu ta dube suba.

A iya zamanta da mama waɗan can Halaiyar nata ta sani amman yanzu taji Ameerah tace tana ɗaga musu kai dan Ahmad zai auri ƴar masu Kuɗi sannan tana danne duk Kuɗin da Ahmad yake turowa.

Ita dai bata san Maman da haka ba amman bata sani ba ko hakan ne tunda Aminiyar Antyn su Ameerah ce, ita daman basa shiri da Ummah saboda Antyn su Ameerah aminiyar mama ce kuma anty tana nuna wa Ummah hassada da baƙin ciki da munafurci a cewar ummah wannan tasa tunda Ummah taga Anty na shigewa jikin mama yasa Ummah ta dena shiga hulɗar su dan ko cikakkiyar magana Ummah bata yi musu.

Sauran matan gida kuma gulma ita kuma Ummah bata gulma barta da son abin duniyarta wannan yasa bata shiri da kowa a gidan take sabgarta ita ɗaya Ita ko Anty maman su ameerah kusan Kullum ma tana sashen mama wadda maman ta ɗauki Anty a matsayin aminiyarta akaf gidan babu wadda mama ta yarda dashi kamar Anty sabida yadda Anty take wa mama Biyayyah tare da nuna mata zahirin ƙauna.

Kawo kayan a saka mata”

Cewar mama bayan ta shafe Jaririyar da mai Da sauri Anty ta miƙe tana bari ta je ta ɗauko kayan a ɗaki wanda Amatullah tasan ba domin Allah ta faɗi hakan ba kawai dan ta shiga taga ƙwaƙwaf ne.

Minti kaɗan ta dawo da akwatin ƴan kayan gaba ɗaya wanda mamaki ya cika Amatullah haka ta zazzage kayan waɗanda ba yawa gare su ba Matan gidan ko wacce tabi kayan da kallo banda Mama data ɗauki Riga mai kyau ta sanyi ta Sinke ƴar.

“Amatu bakya bata Nono hala?”

Da sauri Amatullah ta ɗago tana Bin mama da kallo kamar su da Ahmad har tai yawa sannan taji ta gaya mata sunan da ɗanta yake gaya mata

Mamar ta faɗi.

Da kanta ta miƙe ta haɗowa Amatullah tea mai kauri nan da nan ta rufeta da faɗa tana ce mata.

“Gidan ki babu abin da zaki nema ki rasa cikin sa baza ki ci abinci ba Laifin Hadiza ne ( ummah ) tunda ita ba zata tsaya ta lura dake ba haihuwar fari ce in bata tsaya akanki ba zaki lalace shiyasa nacewa Mijin Hafsa ya kawon abata in watan haihuwarta ya kama”

Amatullah ta amshi tea ɗin ta kafa kai tana sha wanda Anty ta amshe maganar.

“Ai mama yaya hadiza sam ta gyara halinta ace mu ta mayar damu ababan gaba fisabilillahi rayuwar haka zata tafi Ace kaf matan gidanmu sai tazo da kanta taiwa Amatullah wanka”

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button