Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 168

Sponsored links

Gaba daya Iffah bawani son hayaniyar take ba yau, dan batajin dadi gaba daya saboda gumurzu sosai tasha da uwa a cikin mafarkinta na daren jiya. Ga yanayin da take ciki na laulayi duk da bata jin wani ciwo kafin jiya da rana. Ta riga su Malikat Haseenat baro kotun ma ita, kai tsaye kuma sashenta ta nufa dan kwanciya kawai take bukata da kadaici, Hannu kawai ta iya dagama hadimanta, kafin a takaice ta shige ta bada umarnin a kawo mata dafaffen madara. Cikin sauri kuwa Amintacciyar hadimarta ta amsa. Ita kuma ta shige cikin takun nan nata sai dai yau tattare yake da kasala.

Da sallama ta shigo dakin da ya sha gyara sai tashin kamshi masu dadi yake. Ta maida kofar ta rufe. Juyowar da zatai gaba dayanta idanunta suka sauka akan Uwa da ke zaune zama irin na izza da kasaita cikin kujerar ta ta gado ko nace ta tsafi tana wani irin cika da batsewa katon hancin nan nata ya sake budewa

Wani irin wawan tsaki Iffah taja mai masifar karfi ta dauke kanta. Babu alamar ko dar tattare da ita ta cigaba da shigowa cikin dakin, kai tsaye gaban mirror din ta ta nufa, dai-dai tana cire bangles din hannunta batare data sake duban inda Uwa ke zaune a harzuke ba ta furta, “A haduwa daya kawai harkin tsorata kin bayyana kanki karamar agwagwa mai wanka da ruwan dagwalon gulbin wasu. Ai nazata karfin ikon naki zaisa ki cigaba da kawomin harin a cikin barci?”.

 

 

“Idan tunaninki ke kin iya to da sauranki”. Uwa ta fada cikin tsananin kaushin murya mai fita da dacin da ke har a kasan ranta. Wata yar dariyar rainin hankali Iffah tai tare da juyowa, ta dan jingina da mirror hannayenta harde a kirjinta. gaba da idanunta sun canja kamanni mai firgitarwa. Sama da kasa take kallon uwa da itama nata idanun ke jazur kamar garwashin wuta.”Tsohuwa iyawa ba yawan shekaru bane ko kwarewa a mishirikanci. Karkiyi wasa da wannan dagwalon tabon dan shi zameki zaiyi ya kaiki kasa wanwar. Da ace iyawar taki ta cika iyawa, da kin iya a gabar da Iffah bata san komai ba sai UBANGIJIN da ya halliceta. Indai har wannan jinjirar yar kwanaki uku da haihuwa zata bacema ganinki da jinki, basirarki ta toshe a gabar da kike gab da isa ga nasararki ki sake dawo da ita a inda karfin ikonta ke a saman naki to ki sake tabbatar da k ba komai bace face batacciya mai jahilin tunani. Ni wlhy da ga lokacin dana san kana gaba daya sai kika kara komawa kasa wanwar a karkashin kasan tsinin takalmana. Ashema ke karamar kwaruwa ce tunda har sai kin jinginu jikin raunin wasu a fagen cimma burinki. Ashe ke ba komai bace face makaskanciya da dan yanzu UBANGIJI yace mutu dole ki amsa kira a shafe babinki kamar yanda aka shafe na uwar data haifeki harta nuna miki wanna hanyar shiga wutar. To wai ni banda ke din jahilar dabba ce a cikin kaskantattun dabbobi a wannan shekarun naki kike tunanin mulkar kasa irin ruman wai harma da duniya. Oh oh lallai kin cika babbar aladiya wih…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button