Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 36

Sponsored links

Shigar Malikat Bushirat sashen Tajwar da yanayin data fito ya sake zama wasu ƙananun maganganu a masarautar, musamman ga masu ikon faɗa aji. Dan ta ko’ina suna da masu leƙen asiri a cikin hadimai da masu tsaron gidan kamar yanda itama Malikat ɗin ke dasu a kowanne sashe. Ga hadimai dai babu damar yin faɗa da kuwwa sai ƴar ƙus-ƙus, ƙus-ƙus ɗin ma sai ka samu wanda kafi yarda da shi kuɗan zanta gudun karka faɗa tarko.

Tun barowarta sashen Tajwar ta kasa zaune ta kasa tsaye. Abubuwane birjik ke faman mata kaikawo a zuciya. A karo na farko kenan da zuciyarta ta fara rawa akan al’amarin dake faruwa tun daga randa aka ɗora tilon ɗanta karagar mulkin kujerar Shahan-shan. Anya kuwa ba’akwai lauje cikin naɗi ba a wannan al’amarin?. Sannan ba zaton wuta a maƙera sukema komai ba alhalin yana a masaƙa?. Ta rumtse idanunta da sukai matuƙar ja da ƙarfi, saboda zuciyarta ke hasaso abun, amma ƙirjinta ne keci da wutar ƙunar dangantashi da abinda tafi so fiye da komai a duniya. Sai dai ya zatai, hakan kamar dole ne a gareta kodan rashin samun wani bakin zare har yanzu….

 

Kalmar bakin zare data faɗo a tunaninta ce ta sata buɗe idanu da sauri, sai kuma ta jawo ɗaya daga cikin wayoyinta da dan tsumar jiki tana gyara zama. Danne-danne tai tare da kaiwa kunnemta. Daga can akai sallama tun kafin ita tayi. A taƙaice ta amsa da faɗin, “Jasrah ina buƙatar hadiman nan yanzun nan”.

“An gama Akia”.

Jasrah ta amsa mata da girmamawa. Mikewa tai itama ta hau shirin fita fadarta. Sai dai komai tana yinsa ne a tsanake amma yanayinta tattare da matsananciyar damuwa. Fitowarta dai-dai da shigowar Ghazi, ya zube ƙasa yana mai miƙa gaisuwa a gareta. Hannu kawai ta daga masa bayan ta kai zaune. Jasrah ma dake zaman jiran fitowar tata tai mata sannu da fitowa. Kai ta jinjina mata da maida hankalinta ga Ghazi dake gurfane kansa a risine. Itama Jasrah hankalinta ta maida kansa.

“Ghazi ya naganka kai ɗaya?”.

“Ranki ya daɗe an samu matsala ne”.

“Matsala kuma? Kamar ya kenan?”. Ɗan jimm yay na jimamin faɗar abinda ke bakinsa. Sanin Malikat Bushirat bata buƙatar kawane-kwane a magana ya sashi girgiza kansa idanunsa na canja kala zuwa ja sosai. “Ranki ya daɗe gawar uku daga cikinsu kawai muka samu, tare da hadiman dake tsaron inda aka killace sun su duka biyun. Diwa da ta rage ma bana zaton zata kai labari, kuma da alama yanzu-yanzu aka aikata ta hanyar madarar da aka basu matsayin abincin rana.

Ba ƙaramar zabura Jasrah tai ba, yayinda Malikat ta rumtse idanu da sauri ƙirjinta yay wata irin harbawa da ƙarfi tamkar zai buɗe dan firgici. Amma a zahiri miskilancinta da ƙasaitar mulki bazai taɓa haska maka komai ba daga yanayin nata…..

★Kamar yanda labarin mutuwar hadiman nan ya isa kunnen Malikat Bushirat haka ya karaɗe kunen kowa a masarautar. Yayinda likitoci suka rufu akan Diwa da itama gab take da rasa tata rayuwar. Wasu kuma sun duƙufa ne akan binciken madarar da suka sha ta ƙarshe duk da kowa ya san daga cikinta ne akama zuba musu ko minene…….

Yayinda ake tsaka da jimamin rasa hadiman da sukai sanadin shigar Iffah a mawuyacin halin da take ciki, ita kuma waraka ALLAH ya saukar a gareta bayan duƙufar Baba yaro akanta da maganin da aka amso a wajen Kaka. Tun a mata hayaƙin farko jinin dake fita a jikinta ya tsaya. Hakan ya basu hope ɗin cigaba da bin dokokin da kaka ya kafa na maganin daki-daki har ALLAH yasa aka dace ta kawo wani nannauyan numfashi da ambaton sunan ALLAH.

“Ruwa!”.

Shine abinda ta ambata na biyu. Cikin sauri Daneen Ammarah ƙanwa ta biyu ga marigayi Tajwar Haysam da ayanzu ke tare da ita ta zabura da kanta ta ɗauka ɗaya daga cikin bottle water dake a ɗakin ta ɓalle murfin ta kafa mata a baki. Cikin mawuyacin hali Iffah take zuƙar ruwar, sai dai kasancewar shine abinda tafi buƙata a ƙanƙanin lokaci ta shanye sa tas. Yumma da itama dai uwa ce gasu Daneen Ammarah ɗin, sannan matsayin Kaka ga Tajwar Eshaan dan ƙanwace ga Malikat Haseena ta sake ɓalle wani ta zuba a hanunta ta shafa a goshin Iffah dake jiƙe sharkaf da gumi. Ajiyar zuciya ta sake ja a hankali tare da buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi. Kaɗan ta buɗe ta maida ta rufe. Alhmdllh suka shiga ambata da mata sannu, yayinda Daneen Ammarah cike da zumuɗi tai kiran Malikat Bushirat. Ita ta fara sanar mawa kafin mahaifiyarsu Malikat Haseena duk da tana cikin halin ciwon ƙafa da bata iya ko miƙewa sai da taimakon wheelchair dama ga tsufa…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button