Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 21

Sponsored links

Shigowarta dai-dai dayin sallamarsa waya manne a kunensa. Zaune takai a bakin gadon dake ɗakin dan inba haka ba zata iya zubewa ƙasa saboda yamutsawa da jininta ke mata. Jin sunan Baba da Babiy ya ambatane ya sata maida hankali garesa itama. Komai sai da Babiy ya zayyanema Kaka kafin yay shiru alanar saurarensa.

 

 

Daga can Baba yaja nannauyan numfashi bayan gama sauraren surukin nasa mijin ƴarsa tilo data rage masa a raye. Sai kuma yay murmushin ƙarfin hali mai sautin daya isa har cikin kunnen Babiy. “Ni ma ina goyon bayan maganar Fareedatu. Da ace wani rai nada ikon hana tabbatuwar wasu daƙiƙu na gaban rayuwarsa masu tafe da ƙaddara da mutane da yawa sunyi rigakafi kafin cikar adadin waɗan nan daƙiƙu Muhammadu Zayyanu. Amma inaso ku tuna muɗin talakawansu ne, masu rayuwa a ƙarƙashin mulkinsu, bamu da wani ƙarfin iko akan hukuncinsu garemu ko kan ƴaƴanmu. Dan haka ku bita da addu’a kawai itama.”

Tamkar yana gabansa ya jinjina masa kansa, tare da ƙoƙarin danne hawayen da yake na zuciya da ƙunarsu gara ace a zahiri suke zuba bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. “Shikenan Baba, amma furucin Iffah ya girgizani, ina tsoron kar zuciya ta ingizata tai yunƙurin aikatawa. Kisa fa! Koda bata aikata ba fitar wannan furucin zuwa kunen wani bayan mu ba ƙaramar magana bace”

“Kar komai ya dameka Muhammad Zayyan. Ta faɗane kawai saboda raɗaɗi da takeji da kuma ƙuruciya, kai dai ka sanar dasu ka amsa daga nan zuwa kwanaki uku. Zan zo a amsa kuɗin auren da ni dama wasu a cikin zuri’an ka insha ALLAHU………

Iffah taci kuka matuƙa da ko maƙiyinta ya dubeta sai ya tausaya mata. Sai dai kuma iya juyawa su Babiy sun mata akan su gudu ta kafe akan itafa ta yarda zata aura *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majeed_*. Sosai hankalinsu yake ƙara tashi da tirjewarta. Gashi gaba ɗaya ta bikice musu ko isashen lafiya babu a tare da ita. A cikin wannan halin Babiy ya sake samun saƙon kira daga masarauta. Yana shirin tafiya sai ga Kaka. Duk sunyi matuƙar mamakin zuwan nasa, dan abune mai wahalar gaske a garesa zuwa inba da wani dalili ba. Sun tarbesa kamar yanda suka saba matsayinsa na uba. Bayan gama gaisawa ya kai dubansa ga Iffah dake kwance cikin bargo duk ta rame ta sake komawa fayau da ita, dama tun rasa ƴan uwanta ɗan jikinta ya zube, dan sam ba siririya bace. Iffah nada jiki murjajje daba za’ace mata siririya ba kuma babu mai sakata a sahun masu ƙiba. Duk da shekarunta har yanzu sunada ƙaranci ALLAH ya bata jiki na manyan mata da’a yanzu komanta yake ciff dai-dai da halittarta. Kaka ya ɗauke idanunsa a hankali tare da maidasu ga Babiy.

 

“Muhammadu Zayyanu ka sakama ranka nutsuwa ka cire batun barin gidan dan bashine mafita ba. Hasalima tun randa ka amsa kiran masarauta wannan gidan zagaye yake da dakarun daular ruman harta inda baka zata ba. Ko’a tunaninka zasu tunkareka da wannan maganar su baka damar kanka sannan su koma gefe da tunanin kai bazakayi wani yunƙuri ba”.

Daga Babiy har Ummu da Hanash kallon tsoro da mamaki sukema Kaka. Ya ɗan jinjina kansa alamar tabbatarwa. “Karku damu da yanda akai nasan wannan, kai dai kawai kaje ga kiran da sukai maka. Karka kuma nuna wani ja’inja kace ka amince musu suzo neman auren”.

 

Kuka Ummu ta fashe da shi tana kallon mahaifin nata. Yay ɗan murmushi da ɗauke kansa tamkar bai fahimci mitake nufi ba. Ganin haka Hanash da idanunsa sukai jajur cikin cinkushewar harshe yace, “Amma kaka miyasa ka zaɓa itama mu sake rasata? Wlhy nayi alƙawarin in har itama ta salwanta sai na salwantar da ran Shahan-shan da wannan hanun nawa wajen ɗaukar fansa koda nima za ai gunduwa gunduwa da naman jikina!!”.

 

“Ba kai ne zaka salwantar da ruhinsa ba, ni nan Fareedah bint Zayyan nice zan karya ƙarfin ikon azzalumi da hannuna, zan masa shaƙa irin wadda har sai ya mutu yana mai kallon tsakkiyar cikin ƙwayar idanuna Hanash Akhi”.

Su duka zuba mata idanu sukayi, dan a yanda take maganar babu alamar tana a cikin hayyacinta. Babiy zaiyi magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai yaje kawai….

★Kamar yanda Kaka ya umarci Babiy ya amsa kiran masarauta kasancewar a wannan karon an bashi damar zuwa ne shi kaɗai batare da dakaru sun taho da shi ba. A yanda ya samu tarba zai tabbatar maka dama a jirace ake da zuwansa. Kamar ko yaushe a wannan karon ma baiga Tajwar ba, amma dai a karon farko na tarihin rayuwarsa an kaisa har cikin fadar Shahan-shan. Inda yaga tsantsar dukiya da ainahin karagar mulki ta Shahan-shan da akayita da zallar zinare. Hakan ba’abin mamaki bane ba, saboda girman Shahan-shan koda da diamonds akai kujerar mulkinsa bazai zama wani babban al’amari ba, sannan zinare arziƙin ƙasar su ta ruman ne da bare ma kanzo ya ci balle su ƴan ƙasa musamman Shahan-shan. Karo na farko da Babiy yaga karramawa daga dattijan daular ƙasar ruman. Waɗan da ko’a mafarki bai taɓa tunanin gani ba dan su ɗin ma ba’abune mai sauƙi ga duk wani talaka ganinsu ba kai tsaye haka. Duk da a birkicen da yake ALLAH sai ya saka masa nutsuwar yi musu bayani babu ko rawar harshe a tare da shi. Sun masa godiya da tabbacin a gobe idan ALLAH ya kaimu masu neman aure zasu zo. Karramawar da sukai masa ta matuƙar basa mamaki da tsayawa a ransa, sai dai ta wani gefe na zuciya ya tabbatar da sabuwar hanyar yaudarace kawai. Cikin danƙareriyar mota aka maidasa har gida badan yaso haka ba, yayi shiru ne kawai domin bin unarnin mahaifin matarsa, dan duk da bai taɓa ambatawa ba ga kowa ya jima da tsanar duk wani abu daya shafi masarautar daular ruman..

A wannan dare Babiy yayi zaman kuka irin wanda ake kira kuka a zahiri da baɗinin rayuwa. Har yanaji bazai iya cigaba da yima kaka biyayya ba shikam, zai ɗauke Iffah su gudu daga ruman koda daga shi sai ita ne. Sai dai wani ɓangare na zuciyarsa na tunatar da shi maganar Kaka, yasan gaskiya ya faɗa, dan daular ruman bazata zuba ido na barinsa sakakai ba. Ajiyayyun dakarun dake a ƙofar gidansa ma kawai tabbaci ne….

A ɓangaren Ummu ma bata runtsa ba, sai dai saɓanin Babiy ita kwana tai tsaye tana gayama UBANGIJI damuwarsu da roƙonsa kariya da kuɓuta ga yarinyarta. Shi kuwa Hanash kwana yay ƙulla ta yanda zai halaka Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da kansa. Hakama Iffah nata shirin nada alaƙa dana Hanash. Ta gama yankema kanta koda zata mutu itama sai dai su mutu tare da Tajwar Eshaan. In yaso a binne gawarta a tsakiyyar ruman matsayin tarihin da za’a dinga tunawa…….

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button