Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 6

Sponsored links

Cikin ƙaton gidan mahaifin Zainab Alhaji Idiris Mai kwano Dattijon arziƙi Mutumin ƙwarai mai taimako Domin Allah Ba domin duniya ta yaba mashi ba.

Ƙaton Falo ne wanda ya sami damar lashe manyan saitunan Kujerun Royal har Guda Biyar Babbar Mace Zaune A saman One seater tana danna wayar dake Hannunta Hajiya Zahra Kenan Uwar Gida kuma amaryar Alhaji Idiris mai kwano Haifaffiyar Jahar sokoto Mahaifiya Ga Zainab Wadda Zainab Ɗin kaɗai Allah ya basu a kaf Duniya Duk yawan arziƙin su da tarin Dukiyar su Basu da wani ɗa inba zainab ba wadda suka ɗauki Son duniya suka ɗora mata.

Daga Alhaji Idi har hajja zahra mutanan sokoto ne kasuwanci ya kawo Alhaji idi kano wanda yake zaman sa anan Jambulo ya gina ƙaton gidan shi, Wanda kullum gidan baya rabo da jama’a da yake taimakawa Haka zalika matar shi Hajiya zahra bata da matsala ko kaɗan matsalarta ɗaya shine taga ƴarta Zainab Cikin damuwa.

 

 

 

Zainab Itama bata da wulaƙanta Mutane tana da kirki matiƙa haka in kaga tana wasa da masu aikin su sai ka rantse Ba ƴar gidan bace gaba ɗaya karatunta Na likitanci tayi shine a ƙasar Indiya yanzu haka tana a matsayin Cikakkiyar likitar mata a asibitin Malam Aminu Kano Zainab tana da Mugun kuɗi in ka cire na mahaifanta itama kanta mai kuɗin kanta ce

Zainab bata da wata damuwa Ko Matsala a rayuwarta sama da Aikin ta Na asibiti da take dan tana masifar son aikinta , Sai kuma Ahmad wanda ta ɗauki son duniya ta ɗora mishi tana mai wani irin maitar So wanda ji take kamar ta lashe shi ta mayar dashi Cikinta,In kaga zainab tai kuka akan Ahmad ne in kaga Zainab tai dariya akan Ahmad Ne tana Masifar son shi tana mugun jin tsoron shi bata da dama akan Ahmad, Zainab tana da ƙawaye sosai ƴaƴan manya kasancewarta Mace mai son jama’a da kwashe kwashen ƙawaye Shiyasa bata rabo da su ko gida ko Office matsalar Zainab ɗaya ce tana da mugun Zargi Daidai da ruwa ka bata in bata yarda dakai ba bata sha mace ce mai zargin gaske sai dai Duk zargin nata akwai ta da saurin ɗaukar shawarar ƙawaye kasancewarta Ita kaɗai a gidan su bata da abokin shawara sai Hajiya Babarta wadda take masifar son ƴar tata tamkar tsoka ɗaya a miya, Da wuya kaga Zainab taiwa Hajiya laifi sabida bama cika zaman gidan tayi ba sai week end.

Ita ma Hajiyar da wuya kaga taiwa Zainab faɗa sai dai in tai abun da baya cikin tsari wannan tana ƙoƙarin kai son nesa tai mata faɗa amman ba sosai ba.

Cikin sauri Zainab ta fito daga Cikin ƙayataccen ɗakinta harta tana Tuntuɓe Ta nufi wajan Hajiya mahaifiyarta Jikin zainab sanye ike da riga iya gwiwa da dogon wando kanta babu ɗankwali Doguwa ce fara siririya mai far’a da Sakin Fuska

A jikin Hajiya ta zauna tana Tura bakinta gaba kamar wata ƙaramar yarinya Duk da Zainab ba yarinyar Bace don zata kai shekaru talatin da Biyu aduniya ( 32 ) amman tsabar Hutu da gogewa ya hana a gane yawan shekarunta.

Hajiya Ahmad Ne ina ta kiran shi bai ɗauka ba Kodai yana tare da wata Ne?”

Da sauri Hajiya ta ƙwaɓe mata baki tare da cewa.

“Kull kada na kuma ji kina zargin Mijin da zaki aura, Dan Allah Abu ki dinga rage kishin nan da zargi kina son ɓata imanin ki babu fa mai yi sai Allah babu kuma mai hanawa sai Allah”

Kuka Zainab tasa.

“Amman Hajiya danna ce masa zanje nai week end wajan sa zai hauni da masifa dan yaga ina son shi”

Salati Hajiya ta soma tana tafa Hannu

“Ah dole ya hau masifa yace miki Kin haukace ai a garinku na Shasha shai aka ce ana zuwa wajan wanda ba’a aura ba a kwana ko? tashi ki bani waje wadda bata da girma sai na jikinta”

Zainab ta Rumgume Hajiya tana cewa.

“Hajiyata ban da fushi mana Allah ya Huci Zuciyarki”

Hajiya tace.

“Na kasa gane kanki akan yaron na dan Allah ki dinga kama kanki Ina gudar Miki wulaƙancin Ɗa Namiji idan ya gane mace ce tafi damuwa dashi akan shi”

Kuka Zainab tasa tana Birgima a ƙasa wai Hajiya tai mata Baki Ahmad ya wulaƙantata…….

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button