Hausa Novels and Stories

Dare Daya Hausa Novel Page 9 – 10

Sponsored links

Sam bata hanata kukan ba kuma bata ɗago ta ɗaga jikinta ba saima shafa bayanta data shiga yi a hankali tanajin son MAHELET har cikin zuciyarta tanajin babu wanda ya isa ya raba su a duniyar nan sai Allah, jin tayi shiru sai ajiyar zuciya datake saukewa yasa ta dagota ta share mata hawayen da suka ɓata baby face dinta tana cewa shikenan is okay gobe tare zamu fita nasan shine kike yiwa kuka, girgiza mata kai tayi hannunta ta dauka akan haɓarta ta ɗaga kanta sama alamun tunani tana cewa uhmmm mm yauwa kinaso na canza miki waya ƙara girgiza mata kai tayi tana ƙoƙarin komawa jikinta da sauri ta tareta tana cewa to gayamin menene? Ƙafe fuskar momma din tata tayi da kallo kafin ta buɗa baki cike da shagwaɓa tana goge hawayen da ke sauko mata tace A’a momma Mia Dan Allah ki bari muringa kwana tare murmushi momma tayi tana cewa MAHELET you are no longer a child fah you are a big gal now, okay so tell me are you scare of this room

Ƙafe Momma din tayi da ido tana kallonta kafin a hankali ta dauke idonta tana girgiza kai alamun a’a ba tsoro take jiba, zame jikinta tayi Takoma ƙasan carpet murmushi momma tayi ita ta girgiza kai batasan Meyasa takeso su ringa kwana tare bah alhalin tun tana yar shekara biyu ta dena kwana da ita a ɗaki daya Meyasa sai yanzu data girma 17yrs zata sa rigimar gun ta takeso ta ringa kwanciya Hmmmm okay MAHELET dago kanta tayi suka haɗa ido da momma a hankali tace to shikenan ki haɗa kayanki ki mayar da rabi a ɗakina rabi kuma saiki barsu anan wani uban ihu ta saki tayi tsalle ta faɗa jikin momma tana kissing din face dinta tana dariya Aucchhh MOMMA BABY so kike ki karyani girgiza mata kai tayi, murmushi tayi ta kama hannunta tana cewa oya muje yau nida kaina zanyi feeding dinki haka taja hannunta suka sauka zuwa daningtable daidai Abbi na fitowa shima daga ɗakinsa sai murmushi yake sbd ya hango abar ƙaunar sa tare da daughter dinta da bata haɗa ta da komi bah a duniyar nan Yana isa darning Area din suma suna isa ABBI ina wuni lfy yarinyar Momma yana magana yana jan kujera ya zauna momma tayi service dinsu ABBI kowa ya fara cin nasa cikin natsuwa ABBI sai santi yake Daughter Momma ta iya girki sai aure, shiya fara tashi ya koma ɗakinsa ita kuma momma MAHELET sai rigima take zuba mata saida suka ɓata more than 1hrs a darning Area kafin su rabu. Momma ta nufi ɗakin ABBI ita kuma ta nufi ɗakinta tayi wanka ta dawo ɗakin momma ta kwanta Bata tadda momma a ciki bah kuma bata damu data nemeta bah tana kwanciya sai bacci. Washe gari kiran sallar farko ta farka bakinta dauke da addu’a ɗaki ta kalla sama da ƙasa kafin ga zuru santala santalan cinyoyinta ƙasa, kwaɓe fuska tayi kamar zatayi kuka sbd yanda taga babu momma a ɗakin sai ita ɗaya fadawa tayi toilet tayi wanka kafin ta dauro alwala sbd yanda taga jikinta ya bace da maniyi kamar tayi mafarki tana wanka tana tsaki tana cewa wannan wace irin jarabawar rayuwa ce.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button