Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 16

Sponsored links

Kuka! ne ya kuma ƙwace mata duk da Ummah mahaifiyarta ce amman ta cuceta cuta mafi Muni arayuwa yau ga ranar nadama tazo mata.

Maganar Alhaji ce ta kuma katse mata kukan.

“Saboda taga ɗan uwanmu bashi da lafiya alokacin yana kwance tagama ɗibar mana albarka tai gaban kanta kamar ke ɗin ƴar mace ce sannan Kuma tazo ta Bimu da zage zage da Cin zarafi duka to yanzu gashi nan wa gari ya waya?”

Amatullah tace.

“Ni Alhaji sabida Ummah har tafi son Imran akaina nima alokacin duk yadda naso na fahimtar da ita illar Hakan taƙi daga ƙarshe tace zata tsinen In ban bi umarnin taba to Alhaji yaya zanyi? ƴan uwanta suna jin tsoron gaya mata gaskiya kaikuma da kake babba acikin mahaifan mu bata ga girman kaba, Alhaji dukkan abubuwan danai a wancan Lokacin wallahi ba laifi na bane ummah ce ta mini barazanar tsinuwa”

Tsananin tausayin yarinyar ya kama Alhaji babba lallai dace da iyaye nagari sune tushen samuwar al’ummah ta gari Yarinya ƙarama Hadiza nason jefa rayuwarta Cikin garari yanzu meye amfanin auren? ko shekara ba’aiba ta haihu gashi kuma Miji ya korota batare da ansan taka maiman Iyayen shiba bare aje a neme su.

“Wuce gida Allah ya kawo mana mafita”

Ya faɗa mata hakan da tausayawa.

A raɓe ta shiga sashin su ta tura ƙofa tai sallama da yake lokacin ruwa ya ɗan tsagaita yasa Ummah dake zaune tana wa Baba firfita tace.

“Waye ne?”

Amatullah ta bankaɗa labule ta shiga cikin ɗakin tana mai cewa.

“Ummah nice”

A zabure ta ɗago tana cewa.

“Daga ina? a wannan dare kar dai kice Kin kaso auren ki munafuka? daman Imran ya gayan duk irin baƙin halin da kike masa har kina hana shi halal ɗinsa to wallahi inma auren ki kika kaso ba’a………

Da sauri baba yace.

“Hadiza kada ki rantse dan ba gidan ki bane gidana ne kada kika ina kwance kice zaki ciwa ƴata Mutunci inke bakya son ta ni ina son kayata”

Kuka Ummah tasaka tana cewa

“Sha’aibu ni zaka gayawa haka akan Amatullah? shekara nawa kana naɗe ina hidimar ka kai kashi na kwashe kai fitsari na kwashe sannan kazo kana mani wasu maganganu Wanda ƴaƴan naka kawai haihuwar su kai mai ka sani nasu? shine dan ta kaso aurenta a inda nake dandalar arziƙi zaka Min maganar banza”

Da sauri Amatullah ta zaro ido tana kallon Umma wace irin mace ce Ummah ta manta sanda Baba keda Kuɗi yake musu Komai dan Allah ya jarabce shi shine har zata na waɗannan maganganu lallai rayuwa babu tabbas.

“Daga yau ki daina dukkan abin da kike min Kiga idan Allah baze Mini ba, Kinga yarinya cikin dare babu ba’asin komai Kinzo kina mata faɗa akan wasu maganganu can na son zuciya daya gaya Miki Hadiza kada ki fusatani fa ko waccen Lokacin da kikai gaban kanki dan bani da lafiya ne ban san inda kaina yake ba

Baba ya faɗa a matiƙar fusata.

Ummah tace.

“Oho dai kaima ai kaci arziƙin auren nata bada ban Mijin nata ba da tuni kana kwance kai ba gawa ba kai ba mai rai ba kuma ke buɗe kunnen ki kijini da kyau”

Ta faɗa da ƙarfi tana kallon Amatullah……….

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button