Hausa Novels and Stories

Aunty Rumaisa Hausa Novel Complete

Sponsored links

Da yake a K’asar Sénégal capital Babban birninsu (Dakar) da mislin karfe Biyar na yamma, Ko ina ka waiga dandazon jama’a ne, matafiya cikin Airport din kowa na jiran lokacin tashin jirginsu yayi. A tsaitsaye suke suna jimamin rabuwa da ita.Matashiyar budurwa ce kyakyawa lumba one tana da wani irin sihirtaccen kyau duk da ita ba fara ba ce amma tana da mutikar, kyaudoguwa ce sam ba ta layin fararen mata haka zalika bata layin bak’ake, wato chocolate colour kenan sanye take da wani yadi na mata irin na Sénégal green colour dinki doguwar riga wanda ya kamata ya mata cif cif surar jikinta mai kyau ta baiyana tana sanye da wani takalmi shima green ne mai tsayi gaske yana da igiyoyi, sai jakarta da take makale a kafadarta ita ma green colour, ta sha kitso mai masifar kyau wani mai wata irin kwana-kwana ta zubo jelar kitson gaba, sauran gaba sauran baya, daga kitson za ka san tana da gashi, ta dan yane kanta da karamin mayafi shi ma green colour, a gaskiya a wannan lokacin duk namiji mai lfy ya ga Rumaisa zai ji yana son ya mallaketa amatsayin matarsa ta sunnah.

Tsaye suke kasancewar an fara sanarwar matafiya Nigeria su shirya, yan uwanta sun baibaye ta, suna kukan rabuwar su da ita dan har yau sun kasa sabawa in dai Rumaisa zata zo Sénégal to idan za ta koma Nigeria cikin kuka su ke rabuwa da dangin mamarta suna koke-koke. Wata dattijuwa ce mai kimanin 60 year, rungume da Rumaisa tana kukan rashin ta da za ta yi na Rumaisa din.Rumaisa ta manne ajikin tsohuwar tana murmushi tana shafa bayan tsohuwar dan Rumaisa ba ta fiye kuka ba, ga shi idan ta ce za ta yi yanzu tsohuwar rikicewa za ta yi.A hankali Rumaisa ta yi magana, da yaran Sénégal, cikin zazzakar muryata, ta ce” grand-mère ki yi hakuri zan dawo shekara mai zuwa in sha Allahu,ki bar kukan, ta kalli Bibata da Umari ta ce”Ku lallaba mun grand mère ai zan dawo, in ko na sami miji sai ku zo biki ko grand mère?”Ta karasa fadar maganar tana ma grand mère chakulkuli.Sai ga ta tana dariya tana dukan Rumaisa, daket ta kwace ta fara gudu grand mère ta bita suna zagaya dan filin da suke tsaye, su Bibata suna musu dariya, jama’a sai kallonsu suke cike da sha’awa, barin Rumaisa yadda jikinta yake motsawa.Saboda akwai ta diri mai kyau da daukan hankali, jigidarta da ta ke daure a k’ungata mai dauke da sinadarai sai cakas-cakas suke, a k’ugunta, Rumaisa doguwa ce chocolate colour dirara mai kirar Coca-Cola akwaita mazauna, masu mutikar daukan hankalin maza, samanta a tsuke k’asanta a bude yake, ba ta da kiba kuma ba ta da rama sosai akwaita da hips na daukar hankali, ga ta da manyan-manyan boobs a tsaye suke cur tandam-tandam, ma su tafiyar da imanin duk wani lafiyayan namiji. Rumaisa tana da doguwar fuska mai dan fada, tana da dogon hanci da manyan idanu farare tas lumsassun idan tana kallonka za ka zaci kallon raini take ma ko kuma tana jin bacci gashin idanunta gazar-gazar ne haka gashin girarta mai kyau ne, sai dai tana da fadin lips sosai irin na yan Sénégal, amma cikin ikon Allah sai ya yi mata kyau mutika lips dinta pink ne, tana da dimple a gefen kumcinta na dama wanda ko magana take lobawa yake bare ta yi dariya, Rumaisa tana da fara’a da son mutane ba ta da raina mutane sai dai ta fiye sanyin hali kuma ba ta cika surutu ba mutum daya yake bata ciwon kai shi ne ya koya mata surutu da Masipa

Shekarunta na haihuwa 26 year amma wlh ba za ka taba cewa Rumaisa tayi 20 year, ba saboda Allah yayi mata kyawun diri da kyan fuska ko ta fadi shekarunta na haihuwa mutane ba sa yarda sai su ce karya take ba za ta yi ashirin ba ma dole take kyalesu saboda ko a makaranta haka ta yi ta fama da kawayanta da malamai kafin su kammala karatunsu na karshe wato law school , wlh har sai da ta fara musu yar masifar da Abdallah ya fara koya mata tukun ta samu kansu, suka rabu da ita suna cewa an kara mata shekaru ne ai.Dole Rumaisa sai dai ta yi dariya ta ce ta ji har suka gama karatun su.Sosai Rumaisa suke zagaya filin suna dariya ita da grand mère, umari sai ya fara hawaye ya tuno da mahaifiyar Rumaisa da ta mutu.Moubarak ne ya isa gurin Rumaisa ya kamota ransa a bace ya ce “wai me yasa kike haka ko baki ga yarda jarababbun maza ba suka zuba miki idanu ko baki san abin na bata mun rai ba wlh dole zan zo Nigeria cikin satinan tunda karatu ya kare Abbie ya bani auranki na dauko abuna mu taho haba ina dalilin jaraba sai kace Rumaisa ce kadai mace.” Ya karasa yana huci.Rumaisa ta kwace jikinta,ta kura masa idanu dan sam ba ta san da zuwan sa ba, cikin sanyin murya ta ce”wai Moubarak me yasa kake da kishi yaushe muka yi da kai zan aure ka wlh har yanzu ban sami kalar namijin da nake so ba in da ina son ire-iren ka da tuntuni ina cikin karatu na yi aure plz ka barni mana mu tsaya zumunci ba wai soyayya tsakanin mu, da wani idanu zan kalli Aliya matarka haba dan Allah.”ta fada tana ja baya.Moubarak kallonta yake cike da mamaki ya ce”wlh a kanki ko sakinta ya kama zan yi wlh idan kika ga ban aure ki ba sai dai wani ikon Allah” grand mère ta fara masa fada ta rungume Rumaisa tace”ki rabu da sakare.”dariya Rumaisa ta yi..za ta yi magana aka fara neman matafiya sai lokacin idanun Rumaisa suka ciko da ruwa ta rungume grand mère suna kuka.Sai da Bibata ta banbare, Rumaisa daga jikin grand mère. Rumaisa ta rungume yan uwan mamarta maza da mata daya bayan daya, Bibata ta ja hannunta ta rakata bakin inda za ta shiga har gun jirgi Moubarak na biye da su hannu ta daga masa dan a rabu lafiya. Haka Rumaisa ta shiga cikin jirgi tana kewar yan uwanta.Tunda Rumaisa ta shiga jirgi ta jingina kanta da kujera ta lumshe idanunta tana safke numfashi tana jin wayarta na ringin ta ki bude idanunta ma bare taga mai kiran, dan ta san bai wace, Abdallah.A can kuwa *Nigeria garin Abuja unguwar Games village* a dai-dai wannan lokacin wani matashin saurayi ne ya fito cike da takun isa da kasaita yake takunsa, yana kalkada makullan mota,yana ciza lips dinsa ya nufi rumfar ajiye motoci da take cikin wannan tamfatsetsan gidan tsarare wanda aka kerasa da kayan zami tamkar a k’asar larabawa babu abin da babu a gidan tsayawa fadar tsarin gidan ɓata lokaci ne, amma ya hadu ta ko ina dan gidan kallo daya zaka masa ka san ya hadu ba karya me shi ya ci ya tada kai da nera.*Abdallah* yana isa rumfar motocin ya yi tsaye jikin wata jibgegiyar Jeep fara kal fuskarsa ba walwala yana latsa zabgegiyar wayarsa iPhone 11 yana jan tsaki da ciza baki.yana sanye da wasu kananun kaya riga da wando masu masifar kyau Ash colour sun yi masifar masa kyau sai zuba uban kamshi yake kayan sun fito da girman kirjinsa saboda yadda kayan suka kamashi, da gan-gan yake zazago wando yayi k’asa amma hakan baya hana kaya su masa kyau, gashin kansa mai tarin suma baka sudik sai walkiya yake iska na kada gashin tamkar na indiyawa harda tilar kunne daya gare shi wacce yasa mata barimar zallar gold sai sheki yake gashin kansa sai walkiya yake saboda bai fiye aski ba shiyasa zaka ga gashin tamkar na wata macan, sai walkiya yake saboda bai fiye aski ba shiyasa zaka ga gashin tamkar na wata macan,Abdallah dan kimanin 23 year dogo mai murdaddan jiki mai zubin karfafa yana da faffadan kirji samansa a bude yake yayin da k’asansa yake a tsuke,fari ne tas kyakyawa ajin karshe a kyau yana da manyan idanu dara-dara da gashin idanu da na gyara masu kyau yana da dogon hanci bakinsa dan karami, jajur da shi tamkar na jarirai wanda hakan ya kara masa kyau ba kadan yana da dimple har biyu, ko magana yake lobawa suke uwa uba idan ya yi dariya, abin da ya ke tafiya da Antynsa Rumaisa kenan tayi ta saka sa dariya tana saka yatsarta ramin tana tabawa. Abdallah ga shi da shegen kwarjini duk girmanka idan kuna magana da *Abdallah* ya tsareka da wannan shanyayyun idanun nasa masu wani sinadari a cikin su na baiwa da ba kowa Allah ya ke ba irin ta ba dole ka ji shakkarsa shiyasa zaka ga har wanda suka girme masa suna shakun sa saboda shi yaro ne jarumin gaske ta ko wane fanni namiji gaske ne shiyasa ko a makaranta abokansa da malamai suke kiransa da Baffa Abdallah babban mutum, shi ko uban son girma sai ya fara bubbude hancin ala dole shi babba ne, Abdallah duk abin nan nasa amma sai ya maida kansa sakare mara wayo a gurin Antynsa Rumaisa ita ko take biye masa tana renonsa tamkar jariri duk da watarana idan ya shakata ta ga iskancinsa yayi yawa fada suke sosai ta yi masa fushi, dan labari dai sai a nan gaba. Kai komo Abdallah ya fara saboda kiran da yake ba’a dauka, ransa a bace ya bude motar ya shiga, cikin daddadan muryasa a yangace can k’asan makoshi ya furta”Wlh My Aunty Rumaisa sai na bata miki rai fiye da yadda kika bata mun yau nine zaki dauka dan

kuka tana cewa wayyo wuyana Yayana ya murde mun wuya bayan marin da ya zuba mun”Rumaisa ranta a mugun b’ace ta mike ta na cewa”wlh ran Baffa sai ya b’aci yau ta “fada tana nufar kofar parlo.Mamie da Abbie da Al’meen suna kiranta ta rabu dashi kar fa suyi rikici dan a sama ya ke ta ce”wlh Abbie sai na wanwanka masa mari yaji idan da dadi ai shima ai ya na da gaba dashi”ta fada tana ficewa daga parlon.Kai tsaye Rumaisa part d’insu Abdallah ta nufa ko ina na jikinta motsi ya ke, tamkar tarwada sai sauri ta ke ta je ta rama ma Na’imah dukan ta.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button