Hausa Novels and Stories

Fulani Page 12 Hausa Novel

Sponsored links

Ya karasa yana daure zariyar wandonsa karen sigari a bakinsa. Kamar wacce tai arba da mutuwarta haka ta nufi inda bokin ruwan yake ta dauka da sauri jikinta har rawa yake ta shiga dakin da suke kwana ita da naja ta dauko hijabinta ta saka ta dauki bokintin ta fice daga gidan tana ala ala kar ma tai numfashi da karfi mahaifinta ya ji.

Sai ta fito daga cikin gidan sannan ta shara hawaye, ina zata je debo ruwa yanzu cikin dare? Ta san ko wane gida a yanzu sun rufe rijiyarsu, gashi babu wuta balle taje bohol domin idan babu wuta to bohol din baya aiki.

Hanya ta mike tana tunanin wace rigiyar zata dosa, hawaye na ziryo mata, da karfi da yaji dazun Umma ta hana ta deban ruwan ta wanke mata surfe amman ta bar Naja yar gata tai wanki da ruwan yanzu kuma sai ace ita ce zata je ta debo wasu. Hawayen idonta ta share ta nufi gidansu kawarta Khadija, tun a bakin kofar gida take sallama amman babu wanda ya amsa ta sakamakon kure volume da sukai da wakar fitattacen mawakin nan da Falmata tafi kauna fiye da komai da kowa a duniyar nan, wato Sirleem M2. A take ita ma ta bi sahu cikin yaran makota da suke zaune bakin kofar dakin Maman Khadija suna kallo, ba ta ko bi ta kan neman Khadija ba ta zauna saman bokitin ta fara bawa idanuwanta abinci, a take murmushin ya gauraye fuskarta ranta yai fes kamar ba ita ba, daman can haka take indai tai arba da wakarsa ko hotonsa wani irin dadi take ji saboda burgeta yake kaf a mawakan duniya babu wanda take so irin Sirleem har wani shauki take ji idan ta tuno wakarsa.

“Ke”

Khadija ta dafa ta aje butar hannunta da ke nuna cewar daga bandaki ta fito.

“Ina kika fito da bokita da daren nan?”

Falmata bata kula ta ba sai da wakar Sirleem ta kai karshe kaf sannan ta juyo tana kallon kawar tata kamar wacce ta dawo daga hayyacinta.

“Me kike cewa?”

“Oh na shiga uku ni Khadija wato tsabar son wakar M2 har baki ji abunda nake fada ba”

Dariya Falmata tai.

“Wallahi ina son M2 sosai Khadija ya iya waka sosai yai ta hausa yai ta turanci har kasashen waje ance yana zuwa yai waka kuma kin ga dan Yola ne ai dole mu so shi ko?”

“Ke dai kike sani, dan yana dan Yola aka ce miki zama suke a garinsu ne, yawanci kasashen turawa suke zuwa ko Abuja su zauna”

“Khadija kin san me? Da ace na yi boko na iya rubutawa da karanatawa ko? Da nima na rika koyon wakokinsa ina yi”

Cewar Falmata tana dariya har kyakyatawa.

“Lallai Falmata abun na ki babba ne, ina zaki je da dare ke da ba a barin kina fita?”

A take yanayinta ya canja murmushi da far’ar dake fuskarsa ta gushe tunawa da duniyar kuncinta, cikin rashin kuzari ta labartawa Khadija abunda ya faru sannan ta dora da.

“Dan Allah muje ki kara ni idansu Binta tun da kawarki ce kila Mamanta zata yarda na debi ruwan ko maya biyu ce dan Allah”

“Gaskiya dai tsakani da Allah Falmata Umma tana cutarki, shi kuma Baba ya zama wani iri duk abunda tace shi yake amfani da shi, yadda fa iyaye suke da hakki akan yayansu su ma yayansu suna da hakki akansu, ni kam da ma ke aka kai kauye aka bar kanenki nan wannan wahala ta miki yawa Falmata

Ta zaro ido.

“A a ke idan su Aisha n suke nan ai wahala za su sha sosai tun da su kanana ne, kara dai ni da nake da girma yanzu ni dai muje ki rakani

“Ga ruwa can a jarka je ki deba ki yi uku da bokitin ki”

Kamar ta dauki kawar tata ta goya haka ta ji dan dadi, da sauri taje ta bulbula ruwan ta cika bokinta ta kai gida ta sake dawowa ta kara wasu har sai da tai bokiti uku sannan ta hankalinta ya kwanta. Bayan ta aje bokitin a mazauninsa ta nufo kofar dakin Tumba kamar mai labe ta tsaya daga bakin kofa murya can kasa tace.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button