Hausa Novels and Stories

In Bani Complete Hausa Novel

Sponsored links

yace “haba Umma, to kibari nai magana mana, nace kiyakuri babu inda zaki, kiyakuri kinji” kwafa tayi tawani juya ido tana karkada kafa tace “nayi, yi maganan ka” kallon matar yayi datai shiru tana kallonsu, anatse yace “Halimatu ina Hamida taje?” ahankali tace “wlh Alhaji nima bansani ba, bansan inda tayiba, ina fama da jama’an biki ban masan bata gidan ba saida Ihsan tazo ta fadamin” cikin fushi da tsananin takaici yace “to kije koma ina take ki nemota kindaisan Umma tace da ita za’akai yayarta chan legas gidan mijinta ko, na fadamiki kinemota ta dawo gidan nan right away” dan ajiyan zuciya ta sauke tana kallonshi kafin ta girgiza kai kawai cike da takaici ta juya zata fita daga dakin saikuma ta juyo ta kalleshi da idanunta da sundan chanza kala tace “amma Alhaji kasan matsalan yarinyar nan batun yauba ko, batun yau mukasan matsalan Hamida na Agoraphobia ba, batasan mutane, tanada tsoron shiga taro, tun tana yarinya haka take, yanz…” cikin fushi ya katseta ta hanyar cewa “yanzu yarinya ce? Me amfanin ki amatsayinki na mahaifiyanta? Kinga kisan yanda zakiyi kinemo Hamida kindaiga ran Umma abace yake kina kara bata lokaci ne karfe biyar za’a zo daukan Habiba yanzu karfe uku harda kwata” juyawa tayi ahankali tafita daga dakin, da kyar ta iya saita fuskanta ta amsa gaisuwan da mutanen tsakar gida ke mata amatsayin ta na uwar amarya ta wuce ta shiga bangaren su inda falon ma ke cike da jama’a makil, corridor su tayi tabude wani daki ta shiga mace dayace a zaune a dakin tana hada kayan akwatin amarya data ciro kana ganin matar kaga kamaninta da matar data shigo, maida kofar tayi ta rufe ta shigo ta zauna kan gado dabas da sauri tasa hannu tana goge kwallan daya zubo mata, da sauri matar dake hada kaya a akwati ta saki kayan hanunta tazagayo tazo ta gabanta tace “menene kike kuka Maman Ayush?” share idanunta tayi tanadan nishi alamun kuka nacinta tace “Yaya narasa yanda zanyi da Hamida, kullum, kullum dakika sani saita jamin cin mutunci daga wurin Alhaji da Umma, laifinane Yaya? Nina hallice ta? Munanan dake ai inata trying number ta baya shiga, natura yan uwanta duksunje makota kiramin ita ba’a ganta ba, Yaya ya zanyi? Narasa yanda zanyi na chanza Hamida, narasa wace irin yarinya ce, imagine fa Yaya yau bikin yar uwarta ma ta gudu tabar gidan, ni yanzu a ina zan ganta, yaya zanyi da raina?” takarashe maganan cikin daga murya sosai hawaye na gangarowa daga idanunta, da sauri Yayar tata mai suna Yaya Lami wacce take her only sister a duniya ta rungumeta ta daura kanta acikinta tana shafa bayanta tace “ya isa, ya isa dena kukan, bari na gwada kiranta kozai shiga, is okay.”

Babban train station ne that has been abandoned for years yanzu, ba’a amfani dashi sabida sabon da aka bude, wajen shiru babu mahaluki ko daya sai wani tsoho baba mai gadi dake kwance kan wata yar katifa yakafa babban radio dinshi a kunenshi yaja antenna waje yana sauraran labaran rana.

 

 

 

Zaune take akan dan danddamalin dake kusada railway, tana sanye da bakin hijabi har kasa daya rufe har takalmin kafanta, gefen fuskarta nake hangowa, farace sosai tana sanye da farin eye glasses, gashin idanunta bakin kirin dogaye, lips dinta kananu sunyi pink sosai sun bushe danko mai bata shafa akansu ba, gefenta wani karamin black and white jakane na MK sai wasu duwatsu yan kanana dake gefenta da akalla zasukai guda hamsin, ahankali ta zare hanun damanta dake cikin hanun hijabi data kankame ajikinta ta daura hanun akan duwatsu, farine hanunta sol da dogon yatsun ta sirara inda farcenta ke dauke da jan lalli, ahankali tai picking one stone tana kallon railway ta sauke ajiyan zuciya mai sauti cikin wata irin siriruwan murya nai bala’in dadi tace “Kakan mu!” jefa dutsen tayi akan railway tabi dutsen da kallo harya sauka akasa dutsen ya hargitsa duwatsan wajen ahankali tace “dutsen nan is just like Kakan mu, duk inda take saita hargitsa komi, Kakan mu! Kaman zakaran dawaki ce kukanta ba na alheri bane, Kaka! she’s the definition of Iska ba nauyi gare kiba sai kada itace” wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu ahankali tace “wanan ne Baba, duk inda Kakan mu take yana wurin, baya tsalleke abinda tace, in kana neman sa kanka a bala’i a wurin Abba ka batama Kaka rai, hausawa sunce, Allah ya sauwake wahala, tsohuwa ta ga ajalinta ya kusa” wani dutsen ta dauka ta jefa ya sauka kusa da wanda ta jefa dazu tace “Mama! Mamana! My everything” shiru, ahankali tace “Mama kaman rake take, tanada zaki amma batada tau…” shiru tayi sabida ringing din da wayarta yafara dake cikin jaka.

 

_🌹IN BANI🌹_

ahankali ta zare hijabin ta ijiye akan gadon, kyaykyawan yarinya ce Hamida bana wasaba, gawani irin shape da Allah yamata mai bala’in kyau tana sanye cikin simple riga da skirt na wani poker dot silk material skirt din yabi jikinta yafito da fine curve hip dinta rigan ma yakamata yay mata shegen kyau, kitson shiku ne akanta manya manya dabaza su wuce guda gomaba, gashinta dogon gaske yay tsufa gashi ya kwanta akan goshinta sosai, babu dan kunne a kunenta,looking naturally beautiful, sake goge hawayen daya zubo mata tayi Mama Lami tace “Ya isa kukan haka wuce kije kiyo wankan ki kinji Hamida” gyadamata kai tayi ta wuce tabude bayin dake nan dakin Mama ta shiga bata wani jima sosai ba tafito daure da zani kayanta dasu Zainab suka kawo Anty Lami ta nuna mata akan gadon, daukan kayan tayi bayan tagama tsane jikinta ta shirya cikin kayan doguwan rigan itama aka mata kaman na Zainab bakaramin kyau dinkin yamata ba yafito da shape dinta sosai, zama tayi kan gadon tana wasa da yatsu Anty Lami tace “tashi zakiyi kiyi kwalliya kije kakan ku na kiranki” gyadamata kai tayi tana kokarin danne kukan datakeji taje gaban madubin Mama ta tsaya, tashafa farin hodan data gani awurin, ta shafa man baki, Anty Lami daketa binta da kallo sabida kyan datayi dudda batai gayuba sosai ba amma tai wani irin kyau tace “bayan kin dawo daga wurin kaka kije dakin ku kihada kayan da zakiyi amfani dashi in kinje Lagos din ance kwana uku zakuyi” hawaye ne suka zubo mata da sauri ta share, hararanta Anty Lami tayi tace “ai kyaji dashi lamarin ki ya tabarbare Hamida wuce kibani wuri danni inzan miki nawa wlh saiyafi na wanda maman ki tamiki, kayan takaici kawai mtsww” taja tsaki, ahankali takoma gaban gadon tadau hijabin ta ta zura, baki Anty Lami ta bude tace “kinsa ashobi ki na yan mata saikin saka hijabi kuma? Lallai Hamida nidai wuce kiyi duk yanda zakiyi kekika sani” ta nuna mata hanyar kofa, ahankali tadau jakanta tawuce tafita daga dakin mutanen data sake gani chaa ana hayaniyan biki yasa taja hijabin ta rufe fuskarta tana tafiya ahankali ko ina na jikinta na rawa, kafin takai falo taci karo da mutane sama da goma sha da kyar tasamu ta fice tai hanyar sassan kaka, karo taci da mutun da sauri tai gaba zata wuce batare data dagokai ba taji an wani irin fizgota, a tsorace tadan dago kai hada ido sukayi da Ya Faruk yadaure fuska kaman baitaba dariya a duniya ba, saukar da idanunta tayi kasa bakinta narawa sosai tace “s…sorry Ya Faruk” wani irin matsiyacin kallo yamata hakan yasa jikinta yadau rawa, cikin wani irin kakkausar murya yace “mahaukaciya kawai” yawani irin turata, ahankali ta dagakai ta kalleshi da idanunta dasuka cika da kwalla shima ita yakema wani kallon tsana, cike da dakewa zuciyarta na tsinkewa sosai tace “niba mahaukaciya bace”.

 

_🌹IN BANI 🌹_

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button