Abban Sojoji Chapter 24
Waro ido waje aunty babba tayi tana faɗin “Shikenan komai ya ƙare, Hafsat kada ki ɗaga kiran nan, katse shi kwai , a rude take magana, Hafsat tace “Mommy how can i reject his calls ! Idan zuwa zai fa ? ba kwara na ɗaga naji mai zai ce ba, don mu son yadda za’ae mu dakatar dashi ba…..’ ta ƙare maganar tare da ɗaga kiran ta ƙara a kunnanta tana Zabga sallama,
Hankali atashe aunty babba ke cewa “Kisa wayar handsfree,” cikin hanzari hafsat ta mayar da kiran handsfree don aunty babba tasamu damar jin abunda Marshal Omar ɗin zai ce,
Bayan ya amsa mata sallama yace “Zan Shigo kd yau insha Allah ki sanarwa Mommynki,” yana faɗin hakan ya katse kiran since bfr hafsat tace wani abu,
Cikin tashin hankali Hafsat ta janye wayar daga kunnanta,a wani slow tana kallon mommynta wadda itama kallon nata take yi ido azare,
Murya tamkar zatayi kuka tace “Mommy duk ke kika ja mana wannan bala’en da muke ciki, gashi nan daga ni har ke ba wanda ya runtsa daren jiya rabon mu da abinci ma tun jiyan, yanzu kuma gashi Ya Omar zaizo, Ina fata kin tanadi bayanin da zakiyi masa game da Twins ɗinsa da kika Faffasa ma fuska, ki ka canza musu kamanni, nayi imanin kema Ya omar bazai barki ba, sai ya Canza miki kamanni, don Allah naushi ɗaya zai ma kumatun nan naki Mommy sai an neme su an rasa a fuskarki,’
Tuni ido ya raina fata, aunty babba tace “hafsat ki daina mun waɗan nan suratan naki ki barni inji dakaina, yakamata musan abun yi before Omar ya diro garin nan,’
Zama su kayi zugum kowa zuciyarsa na bugawa daram daram, kowa da irin idea dake zuwa masa akai,
Jahad kuwa na a ɗakin da aka kwantar da hosana dama gado biyu ne aciki, itama doctor sai da ya duba ta, baccin wahala kawai take yi saboda allurar da dr yayi mata don tasamu bacci, duk inta farka sai ta ambaci sunan Hosana saboda itace aranta, so take tama fi ƙarfin allurar da dr yayi mata, don ƙoƙori take ta tashi da ƙarfin gaske don taje ma hosana wadda ke kwance magashiyyan rai hannun Allah 😥
______________________________________
Bayan Omar ya kammala wayar fitowa yayi daga bedroom ɗinsa ya zauna a palor saman sofa yana yin breakfast ɗinsa anatse, wayarsa ce ta shiga ringing wadda ya ajiye agefensa, kai idonsa yayi ya duba Gwaggon katsina ce ke kiransa, murmushi yasaki don kusan kullum saita kira layinsa ta tambayesa ina Ƴa’ƴan Abusufyan ɗinta ya basu su gaisa, hannu yakai ya ɗauki wayar ya kara a kunnansa yana faɗin “Gwaggona kenan fatan kin tashi lafiya,”
Daga can 6angaren gwaggon katsina tace “Allah sarki Omar jiya ko isasshen bacci ban samu ba saboda tunanin ƴa’ƴan abusufyan ɗina, Jiya zuciyata tayi ta bugawa inaji kamar wani abu ya same su, dan Allah Omar karka bari a cutar dasu,
Sai faman zuba take masa a waya sam taƙi bari yace wani abu har sai da ta gaji ta dakata da maganar sannan Omar yace “Ki kwantar da Hankalin ki goggo na, Ƴa’ƴan abusufyan ɗinki suna nan cikin ƙoshin lafiya,”
Ajiyar zuciya tasaki kafin tace “Suna tambayata ko? Suna atare da kai Omar? Ka basu dan Allah muyi waya mana,”
Kamar tana agabansa ta zabga salati
tana cewa “La’ila ha illallah Mahammadar rasulillah Omar ! dama gidan Ishaq ka kaisu? Gidan wannan matar Shuwa mai ƙirar samudawa sam matar nan bata da Imani, zuciyarta irin ta kafuran farkon ce wlh, shikenan ni Allah kaɗae yasan wane hali ƴa’ƴan abusufyan ɗina suke ciki . ……fashe masa da kuka goggon katsina tayi,
Sam omar ya gaza gane ma goggon tasu, a tunaninsa haukan nata ne ya tashi, in ba haka ba ina matar ishaq keda aibu har haka, gashi kuma ta fashe mashi da kuka, cikin rarrashi yace “Calm down your mind Goggona, ƴa’ƴan abusufyan ɗinki suna cikin ƙoshin lafiya, yau ma nake shirin zuwa in dubo su
,’ Cikin shessheƙar kuka tace “To shikenan amma dan Allah Omar nidai nafison su bar gidan matar nan, adawo mun dasu nan in basu kulawa kamar yadda na kula da mahaifinsu tun yana yaro,”
Murmushi Omar yasaki sannan yace “Insha Allah my aunt don’t worry ur self abt them, suna Lou and insha Allah in naje zan basu waya ku gaisa kiji muryarsa may be u will be calm,”
“Shikenan Omar kada ka manta sai na jika,”
Ya amsa mata da cewa “Insha Allah”
daga bisa ni su kayi sallama ya ajiye wayar yaci gaba da Cin breakfast ɗinsa,
Acan ciki kuwa tuni Sehrish ta shirya kayan mazan ne ajikinta tunda su ke gare ta, hijab kawai tasanya ajikinta brown colour, azmee kuwa dama atampa ce ajikinta, Mayafi kawai ta lullu6a a jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba, suna a babban falon sai ga junaid shima ya sauko
“Gsky junaid bazan iya jerawa dakai ba, Irin wannan kyan haka,” sehrish ta faɗi tana nuna shi da hannu,
Ƴar dariya junaid yasaki kafin yace “duk kyan da zanyi bazan fi ki ba, ke fa maca ce, ni kishi ma nakeyi don nasan yanzu zaki fara ɗaukar wanka da zarar munyi Siyayyar nan,”
Murmushi sehrish tasaki ita kanta har ta hango ta cikin Gown ta gayu wow, azmee ma murmushin take saki, atare suka jera suka fuce, a cikin Motar Junaid haɗaɗɗiyar gaske, Shi ke driving yayin da sehrish ke a gefensa sai faman fira suke suna zuba, azmee na a back seat tana sauraron su wani lokacin ma tana sa musu baki suna firar atare, suna ta tiƙar dariya abinsu gwanin burgewa, har suka isa katafaren shopping mall ɗin mai matuƙar girman gaske