Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 26

Sponsored links

ido waje aunty babba tayi tana faɗin “Shikenan komai ya ƙare, Hafsat kada ki ɗaga kiran nan, katse shi kwai , a rude take magana, Hafsat tace “Mommy how can i reject his calls ! Idan zuwa zai fa ? ba kwara na ɗaga naji mai zai ce ba, don mu son yadda za’ae mu dakatar dashi ba…..’ ta ƙare maganar tare da ɗaga kiran ta ƙara a kunnanta tana Zabga sallama.

 

Hankali atashe aunty babba ke cewa “Kisa wayar handsfree,” cikin hanzari hafsat ta mayar da kiran handsfree don aunty babba tasamu damar jin abunda Marshal Omar ɗin zai ce,

 

Bayan ya amsa mata sallama yace “Zan Shigo kd yau insha Allah ki sanarwa Mommynki,” yana faɗin hakan ya katse kiran since bfr hafsat tace wani abu,

Cikin tashin hankali Hafsat ta janye wayar daga kunnanta,a wani slow tana kallon mommynta wadda itama kallon nata take yi ido azare,

 

Murya tamkar zatayi kuka tace “Mommy duk ke kika ja mana wannan bala’en da muke ciki, gashi nan daga ni har ke ba wanda ya runtsa daren jiya rabon mu da abinci ma tun jiyan, yanzu kuma gashi Ya Omar zaizo, Ina fata kin tanadi bayanin da zakiyi masa game da Twins ɗinsa da kika Faffasa ma fuska, ki ka canza musu kamanni, nayi imanin kema Ya omar bazai barki ba, sai ya Canza miki kamanni, don Allah naushi ɗaya zai ma kumatun nan naki Mommy sai an neme su an rasa a fuskarki,’

Tuni ido ya raina fata, aunty babba tace “hafsat ki daina mun waɗan nan suratan naki ki barni inji dakaina, yakamata musan abun yi before Omar ya diro garin nan,’

 

Zama su kayi zugum kowa zuciyarsa na bugawa daram daram, kowa da irin idea dake zuwa masa akai,

 

Jahad kuwa na a ɗakin da aka kwantar da hosana dama gado biyu ne aciki, itama doctor sai da ya duba ta, baccin wahala kawai take yi saboda allurar da dr yayi mata don tasamu bacci, duk inta farka sai ta ambaci sunan Hosana saboda itace aranta, so take tama fi ƙarfin allurar da dr yayi mata, don ƙoƙori take ta tashi da ƙarfin gaske don taje ma hosana wadda ke kwance magashiyyan rai hannun Allah 😥

Bayan Omar ya kammala wayar fitowa yayi daga bedroom ɗinsa ya zauna a palor saman sofa yana yin breakfast ɗinsa anatse, wayarsa ce ta shiga ringing wadda ya ajiye agefensa, kai idonsa yayi ya duba Gwaggon katsina ce ke kiransa, murmushi yasaki don kusan kullum saita kira layinsa ta tambayesa ina Ƴa’ƴan Abusufyan ɗinta ya basu su gaisa, hannu yakai ya ɗauki wayar ya kara a kunnansa yana faɗin “Gwaggona kenan fatan kin tashi lafiya,”

 

Daga can 6angaren gwaggon katsina tace “Allah sarki Omar jiya ko isasshen bacci ban samu ba saboda tunanin ƴa’ƴan abusufyan ɗina, Jiya zuciyata tayi ta bugawa inaji kamar wani abu ya same su, dan Allah Omar karka bari a cutar dasu,

 

Sai faman zuba take masa a waya sam taƙi bari yace wani abu har sai da ta gaji ta dakata da maganar sannan Omar yace “Ki kwantar da Hankalin ki goggo na, Ƴa’ƴan abusufyan ɗinki suna nan cikin ƙoshin lafiya,”

 

Ajiyar zuciya tasaki kafin tace “Suna tambayata ko? Suna atare da kai Omar? Ka basu dan Allah muyi waya mana,”

 

omar yace “Goggo kin manta suna a kaduna,ae gidan Yaya ishaq nakai su…”

 

Kamar tana agabansa ta zabga salati

 

tana cewa “La’ila ha illallah Mahammadar rasulillah Omar ! dama gidan Ishaq ka kaisu? Gidan wannan matar Shuwa mai ƙirar samudawa sam matar nan bata da Imani, zuciyarta irin ta kafuran farkon ce wlh, shikenan ni Allah kaɗae yasan wane hali ƴa’ƴan abusufyan ɗina suke ciki . ……fashe masa da kuka goggon katsina tayi,

 

Sam omar ya gaza gane ma goggon tasu, a tunaninsa haukan nata ne ya tashi, in ba haka ba ina matar ishaq keda aibu har haka, gashi kuma ta fashe mashi da kuka, cikin rarrashi yace “Calm down your mind Goggona, ƴa’ƴan abusufyan ɗinki suna cikin ƙoshin lafiya, yau ma nake shirin zuwa in dubo su,’

 

Cikin shessheƙar kuka tace “To shikenan amma dan Allah Omar nidai nafison su bar gidan matar nan, adawo mun dasu nan in basu kulawa kamar yadda na kula da mahaifinsu tun yana yaro,”

 

Murmushi Omar yasaki sannan yace “Insha Allah my aunt don’t worry ur self abt them, suna Lou and insha Allah in naje zan basu waya ku gaisa kiji muryarsa may be u will be calm,”

 

“Shikenan Omar kada ka manta sai na jika,”

 

Ya amsa mata da cewa “Insha Allah”

 

daga bisa ni su kayi sallama ya ajiye wayar yaci gaba da Cin breakfast ɗinsa,

 

Acan ciki kuwa tuni Sehrish ta shirya kayan mazan ne ajikinta tunda su ke gare ta, hijab kawai tasanya ajikinta brown colour, azmee kuwa dama atampa ce ajikinta, Mayafi kawai ta lullu6a a jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba, suna a babban falon sai ga junaid shima ya sauko, bin shi da kallo sehrish tayi jikinsa na sanye da suits baƙaƙe kamar ma’aikacin banki, yayi kyau sosai acikinsu abun sai wanda yagani, sai faman murmushi yake saki da white teeth ɗin nan nasa kamar gonar auduga,

 

“Gsky junaid bazan iya jerawa dakai ba, Irin wannan kyan haka,” sehrish ta faɗi tana nuna shi da hannu,

 

Ƴar dariya junaid yasaki kafin yace “duk kyan da zanyi bazan fi ki ba, ke fa maca ce, ni kishi ma nakeyi don nasan yanzu zaki fara ɗaukar wanka da zarar munyi Siyayyar nan,”

 

Murmushi sehrish tasaki ita kanta har ta hango ta cikin Gown ta gayu wow, azmee ma murmushin take saki, atare suka jera suka fuce, a cikin Motar Junaid haɗaɗɗiyar gaske, Shi ke driving yayin da sehrish ke a gefensa sai faman fira suke suna zuba, azmee na a back seat tana sauraron su wani lokacin ma tana sa musu baki suna firar atare, suna ta tiƙar dariya abinsu gwanin burgewa, har suka isa katafaren shopping mall ɗin mai matuƙar girman gaske, sehrish taga haɗuwa yau dae karo na farko data fito kuma karo na farkon data fara ziyartar wuri irin wannan, atare suka fito suka shiga wurin, Mutane gasu nan kowa ya ɗau wanka ana ta siyayya ba kowa ya tsone mata ido ba face ƴan mata da samarin dake a wurin, duk sai taji kunya ta kamata ganin yarda Matasan matan dake a wurin siyayyar suka ɗau wanka iya wanka, ita kuwa kallo ɗaya za’ae mata ansan bazata wuce ƴar aiki ba,

 

6oyewa ta rinƙa yi abayan junaid da Azmeee, dariya kawai junaid keyi don ya gano dalilin dayasa sehrish jin kunya tana la6ewa abayansu,

 

Sam ruwan ido ya hana sehrish Sa hannu ta ɗauki wani abu, junaid ne kawai da azmee ke faman ɗebar mata kayayyakin sawa iri iri masu kyan gaske na mata, yawanci arab gowns ne, turkish dress, night dress, Pakistan, english wears komai jidar sa kawai suke yi, laces ne atampa ce, materials, shadda, Everything,

 

Duk tana tsaye tana kallonsu kowanne ya cike shopping basket dake hannunsa, sai dai in sun matsa nan tabisu, in kuma anzo abunda zata gwada tasanya su bata taje dressing room ɗin dake a wurin ta sanya,

 

lokacin da suka zo wurin jerin panties da bra, hannu junaid yasa ya ɗauko brazier ya ɗago da ita yana cewa “Sehrish Ga wannan gwada mu gani,”

 

Sam bata lura ba tana ta faman kalle kalle, ganin hakan yasa shi ta6o hannunta yana nuna mata bra ɗin dake hannunsa yana cewa “Ina magana,” aikuwa cikin jin kunya ta zaro ido tare da sa hannu ta rufe fuska tana faɗin “junaid dan Allah kadaina menene haka agaban mutane,” fashewa da dariya yayi cikin mamaki yace “menene aciki? Kunya kuma ni bansan wannan zancen ba, ni dae ki amsa kawai kije ki gwada in tayi maki, in batayi ba acanza wata shine kawai,”

 

Hannunta na kerma ta karba tana ɗan kallon shi, har time ɗin dariyarsa yake Don shi mamaki ta bashi wai kunya,

 

Shiga dressing room ɗin tayi hada datso kopa, faskekan madubi ne aciki ya cike bangon, cikin hanzari ta tu6e hijab ɗinta da rigarta, ta shiga kiciniyar zira bra ɗin daker hada su sakin nishi,

 

Tsayawa tayi tana kallon kanta acikin mirrow ɗin wow, ta fito ɗas abunta dama tubarkallah masha Allah full ɗinsu suke, bra ɗin ta hau raɗau launin ta maroon colour ce, abunda sehrish take ma mamaki yarda akai junaid ya nemo bra dai-dai size ɗinta,duk jerin braziers ɗin dake a wurin,

 

Cikin hanzari ta cire ta, ta mayar da rigarta da Hijab ɗinta, sannan ta fito, karaf suka ci karo dashi abakin ƙopan ɗakin,

 

a ɗan razane tace”junaid yaushe kazo nan,” hannu yasa ya ɗan sosa sumar kansa yana cewa “Naji kin jima ne, shine nazo in ga ko kin gaza sawa ne, sai in taimaka miki…..,” ganin yarda ta waro ido waje yasa shi dakatawa, muryarta har wani shaƙewa take yi wurin cewa “Junaid kana nufi brazier ɗin zaka taimaka mun nasa !!” ta tambaya a rikice,

 

Kai tsaye yace “eh mana,” Jinjina kai sehrish tayi tare da wuce shi aranta tana mamakin hali irin na junaid shidae ba ruwansa komai normal ne a wurinsa,

 

tsayawa ta ɗanyi da tafiya ta ɗago ta kallesa Cike da tuhuma tace “Ya akai kasan size ɗina?

 

Da buɗar bakinsa sai cewa yayi “Ni dana ga Zahiri,”

 

Cikin sauri yasa hannu ya rufe bakinsa saboda su6ul da bakan da yayi, kamar zatayi kuka take kallonsa tana cewa “Junaid hakan na nufin ka ta6a gani na babu kaya ko”?

 

Girgiza kai yayi yana faɗin “No ba haka bane reeesh, baki fahimce ni bane, Ina nufin….,” sam ya gaza samun amsar da zai bata gashi ta tsare shi da ido tana jiran amsar shi,

 

Muryar azmee ce ta katse su da cewa “tsayuwar me kuke yi ne? Ku hanzarta mana muyi mu kammala, yaushe har muka wuce wurin Saloon ɗin,” cikin sauri junaid yace “Hakane aunty azmee muje kawai yanzu saura me ya rage,” Ya tambaya yana kallonta

 

yayi hakan ne don ya gusarma sehrish da tuhumarsa da take yi, cikin sauri suka wuce tabi bayansu itama,

 

A ranar yini su kayi siyayya Kamar zasu kwashe kayan Mall ɗin,komai sai da suka siyar mata shoes & bags ne Cosmetics komai wannan ba abunda suka bari,

 

Daga nan suka wuce wurin haɗaɗɗen Saloon ɗin duk acikin Mall ɗin yake, a lokacin junaid ya koma cikin mota yana jiran su,

 

Already sun kammala purchasing ɗinsu an jera Manyan akwatinan guda uku biyu sunfi girma a boot aka zuba su, Wasu kayan kuma na acikin Manyan Shopping bags an zuba su har a cikin back seat na motar,

 

Murmushi kawai junaid ke saki ya langwa6ar da kansa jikin seat ɗin motar, babban burinsa shine yaga yarda sehrish ɗinsa zata fito amatsayin mace a fili ya furta “Can’t wait to seee” tabbas yanzu ne yasan yasamu abokiyar rayuwa wadda zasu kasance atare na har iya tsawon rayuwarsu, shigowar sehrish rayuwarsa ta canza mishi wasu abubuwan da dama da yake kewarsu,daga ciki harda kewar Mommynsu da tatafi tabarsa tun yana jinjiri wannan abun ya ta6a mishi zuciya sosai raɗaɗin na’a ransa yana jin cewa duk cikinsu shike bata so, hakan yasa shima baya sonta duk in ta kira waya tana so abashi tayi magana dashi baya kar6a, har ila yau junaid bai ta6a ganin Mommynsu ba ido da ido sai dae a hoto, babu yarda batayi ba akan akawo mata shi Sydney amma abbansu yace muddin tana son ganin shi ta tako tazo da kanta in ba haka ba ita dashi har abada, saboda batayi mashi adalci ba,’ wannan kenan

 

Ya jima yana tunane tunane shi kaɗae abunsa yana ta faman sakin murmushi, adai dai time ɗin Sehrish ta fito tare da Aunty azmee,

 

Ƙaraso wa su kayi ta bude gaban motar ta shiga aunty azmee kuma ta shige baya sannan junaid ya tayar da motar yana faɗin “Har an kammala saloon ɗin”?

 

ya tambaya yana ɗan kallonta tace mashi “Eh,’.

 

“In munje gida za’a nuna min,” ya faɗi da ɗan murmushi a fuskar shi, kai tsaye yabar bakin Mall ɗin yaja Motar kai tsaye ya nufi hanyar gida dasu duk da yaso su biya wurin shan ice cream amma shi kanshi a gajiye yake yafi buƙatar gidan don ya huta, Dama jikinsa sam ba irin na ƴan wahala bane,

 

Motarsu na shiga babban entry ɗin gidan adai-dai time ɗin kuma Motarsu Marshal Omar ta fuce daga gidan, Tasu na shigowa tashi na Fice wa,

 

🙅

 

Bayan yayi parking ɗin motar, wani sergeant ya ƙaraso ya kwashe akwatinan da junaid ya fito a boot ɗin motarsa, , Hada jakunku nan siyayyar na cikin back seat ɗin duk ya fiddo su, yayin da sojan ke kwashe su izuwa cikin gidan,

 

Agajiye azmee da sehrish suka shiga cikin Babban falon bakowa alamar duk sun fita, azmee ta taimaka mata suka shigar da kayan ɗakin suka jibge su da nufin in sun huta an jera su a wardrobe ɗinta,

 

Cike da zumuɗi sehrish ta cire hijabinta don taga gyaran gyashin da akayi mata, Gaban mirror ta tsaya tana kallon gashinta, haɗaɗɗen gyaran gashi akayi mata mai haɗe da Twist,

 

Sai ta rinƙa jinta tamkar Queen saboda haɗuwa, ta jima tana kallon kanta a mirror kafin ta wuce toilet don yin wanka da alwala,

 

Shaf shaf ta fito jikinta ɗaure da toilet, wardrobe ta wuce ta samu riga da wandonta ta zura ajikinta sannan ta ɗauki hijab da dardumar salla ta shimfiɗa, ta kabbara sallah A natse ta Gabatar da sallar,

 

Bayan ta kammala Jiki na rawa ta cire hijab ɗinta ta ninke tare da abun sallar asaman gado ta ajiye su,

 

Zama tayi tana bubbude kayayyakin da aka siya mata na cikin jakun kunan, sam bakinta yaƙi rufuwa, wani haɗaɗɗen takalmi ta ɗauko high heels ta ciro shi daga kwalinsa tana gwadawa a ƙafarta ita kanta ta razana daganin yarda ƙafarta ta fito ɗass acikinsa gashi ash colour jikinsa duk kyalli yake ga wasu igiyoyi na ɗaure sa ya haɗu,

 

Shigowa azmee tayi tana faɗin “Kai!kai! Irin wannan zallar kyau haka gaskiya naji tsoran haɗuwar da zakiyi anan,” .

 

Dariya sehrish tayi tana cewa “dama yanzu nake so in jera kayan acikin wardrobe bansan ma ta inda zan fara ba,”

 

Azmee tace “kada ki damu ae shiyasa nazo saboda nata Ya ki jera su Muyi mu gama, akwai sauran aiki agabanmu ga gyaran cikin gida ga kuma aikin Kitchen,’

 

Miƙewa sehrish tayi ta janyo akwati nan biyu da hannunta izuwa wurin wardrobe ɗinta ta jingi ne su,itama azmee ta janyo ɗayan akwatin tana cewa “Ki barmun jeran kawai, kije ki gyara cikin gidan kafin na kammala Canza ma ɗakin nan naki kamanni,” .

 

Murmushi sehrish tasaki tare da cewa “Toh aunty azmee,” Sai da tafara ɗaukar mayafinta a cikin wardrobe ɗin sannan ta fuce tana murmushi,

 

Babban falon tafara gyarawa duk da babu wani datti a tsaftacensa yake, shaf shaf tagama, cikin hanzari ta wuce upstairs don gyara ɗakin babban yayansu, tana cikin taka steps ɗin taji motsin mutun a down, juyowa tayi don taga kowane ne, Karaf idonta suka sauka akan na HAR0ON, sam yagaza ɗauke idonsa akanta kallon kallo suka shiga yiwa juna, duk a tunaninsa sehrish zata mayar masa da martani amma abun mamaki sai yaga tasakar mashi wani irin ƙayataccen murmurshin kashe zuciya tamkar ta soke shi da kibiya a ƙahon zuciyarshi haka yaji, don har saida yasa hannu ya tarbe saitin zuciyarshi, wani irin sabon kyau yaga yarinyar tayi mishi (nace ba kabari sai ta fara ɗaukar wanka tukunna munyi wannan maganar,”

 

Juyawa sehrish tayi cikin hanzari ta wuce apartment ɗin SGR, tabbas taso ta mayarwa Haroon martani amma daga baya tagane cewa ba buƙatar yin hakan, yanzu fa ita tamkar Princess take ƴa ɗaya tak ga Shugaban sojoji kuma ƙanwar sojoji, dole ne taja class muƙami iya muƙami, wannan kaɗae ya isa ya kashe haroon saboda ƙululun baƙin ciki,

 

Zuru haroon yayi sam yagaza motsi daker ya iya ɗaga ƙafarsa ya soma tafiya jiki a mace, Har time ɗin tafin hannunsa na a dafe da saitin zuciyarshi

 

Bin shi da kallo junaid yayi wanda fitowar shi kenan daga sashen abbansu,

 

Ƙarasawa yayi cikin sauri ya nufi haroon yana faɗin “Yaya Haroon lafiya meke faruwa ne, naga ka dafe zuciyarka, ince dai ba wani abu ya same ka ba,’

 

ɗagowa da ido haroon yayi yana kallonsa yace “Jini Junaid,”

 

Jin wannan yasa junaid tallabo shoulders ɗinsa yana faɗin “Subhanallahi jini kuma a ina yaya haroon,”

 

da wannan muryar tasa ta ƴan giya yace “Yanzu duk jinin dake kwaranyowa daga zuciyata ba ka gani ba? Kibiyar da aka soka mun fa? Ko shima baka gani ba”? Ya faɗi a susuce yana kallon junaid,

 

Baki asake junaid ke kallon ikon Allah shidai baiga komai ba a ƙirjin haroon hannunsa ne kawai daya tallabe wurin,

 

Cikin ruɗi yace”yaya haroon babu komai fa a wurin hannunka ne kawai daka sa ka dafe,

 

Muryar tamkar zaiyi kuka yace”Manxon Allah yayi gaskiya Junaid, shikenan bakomai jeka kawai Allah yayi maka albarka, ya kare ka daga sharrin Maƙiya,

 

Ya faɗi tare da janye hannun junaid daga kafaɗarsa ya wuce sa yana cigaba da sambatu

 

Girgiza kai junaid yayi tare da cewa “Allah ya baka lafiya yaya haroon ya yaye maka wannan shaye-shayen da kake fama dashi,”

 

Yana gama faɗan hakan ya wuce direct ɗakin sehrish don yagaza runtsawa burinsa kawai yaganta ta zura kayan mata ajikinta, yana shiga ya samu azmee tana faman jejjera mata kayan a cikin wardrobe ɗinta, ko ina da abunda aka zuba aciki, gasu nan komai ajere, gwanin kyau,

 

Jin sallamar junaid yasa ta juya da fara’a tana amsa mashi,

 

Yace “Aunty azmee ina Sehrish ne i thought zanzo na same ta anan ne,”

 

Azmee tace “ae tuni ta fita don gyara cikin gidan kasan munbar aiki dayawa shiyasa bamu samu hutu ba,”

 

ɗan zumbura baki yayi tare da cewa “Aunty azmee wane aiki kuma? Mu dawo agajiyen sai kuma ta kama wani aikin, gaskiya bai yiyuwa zanje na dakatar da ita,’ ya faɗi tare da juya ya fuce

 

Murmushi azmee tasaki aranta tana fadin “Romea kenan, Allah dae yasa sehrish tazama mallakin ka, duk da nasan abune mai wuya ayi mashi aure at his age, bansani ba shi da ita waye zai raini wani shi shagwa6a ita kuma shiririta, amma kuma raina na bani cewa akwai wanda sehrish ke so ga dukkan alamu……………

 

ta ƙare maganar zucin nata ayayin da ta koma gaban dressing mirror ɗin sehrish dayake wayaam babu kayan kwalliya kona shafawa illa kwalba ɗaya tak na turaren junaid da tata6a satar mashi wanda har yau bata ta6a amfani dashi ba,

 

Janyo trolley ɗin dake ɗauke da cosmetic tayi ta shiga jera mata su, da turarurruka da mayukan jiki masu kyau da ƙamshi da sauransu, sai gashi mirror ɗin yafito sosai na ƴar budurwa,

 

Cikin ƙanƙani lokaci rishi ta kammala gyara masa part ɗinsa, da wata irin yunwa ta fito ga bacci tana ji tana saukowa down suka ci karo da junaid dake tunkaro stairs ɗin,

 

da murmushi a fuskarta tace “Junaid dama idonka biyu ae nayi tunanin kana can kana sharar bacci,’

 

yatsina fuska yayi tare da cewa “taya zan iya bacci bayan banga gyaran gashinki ba, zuwa nayi ki nuna min in gani,” ya faɗi hada ruƙe ƙugu,

 

Dama tana kallon fuskarshi tasan rigimar ta motsa ga Idonshi sai faman lumshewa suke yi alamar bacci yake ji over,

 

Saukowa ta yi tana cewa “Shikenan zan nuna maka ammma kabari nafara samun natsuwa tukunna, yanzu kitchen zanje na gyara kuma yunwa ma nake ji,”

 

Shiru yayi baice komai Ba dayaso hannu kawai zaisa ya tu6e mayafin data yafa, abunda ya hanasa yin hakan baiso wani yagani cikin Yayyensa balle ya ƙyasa, don kishinta yake ji ayanzu kamar kamar me,

 

Shiga gaba sehrish tayi ta nufi hanyar kitchen, cikin hanzari yabi ta yana faɗin “Nima yunwar nake ji, zan tayaki mu gyara kitchen in mun kammala cin abincin atare,

 

“Shikenan bita zaizai,” ta bashi amsa tana dariya, shima dariyar yayi jin sunan da tasa mashi,

 

“Idan baki so zan daina bin ki,’ ya faɗi ayayin da suke shiga kitchen ɗin,

 

Sehrish tace”Nafison hakan ae, saboda kana ɗebe min kewa sosai,”

 

Jin hakan yasa junaid sakin murmushin murna,

 

Wuce wa yayi yazauna saman ɗaya daga cikin dining chairs ɗin dake kewaye da dinner table yana cewa “Ki haɗa mana corn flakes kawai mu sha, in akwai snacks ki haɗo mana dashi,

 

Ta amsa mashi da “Toh,”

 

A cup biyu ta haɗa musu sannan ta haɗo masu da snacks suka zauna suna sha suna fira ❤

 

AUNTY BABBA

 

Suna cikin wannan fargabar wayar hafsat ta sake yin ringing, cikin hanzari tunkan tasa hannunta ta ɗauka aunty babba ta riga ta ɗaukar wayar asaman cinyarta, a tunaninta Omar ne amma tana dubawa taga Sunan My Dad ya bayyana, ɗagowa tayi ta kalli hafsat hankali atashe tace “Abbanki ne ke kira, Allah yasa dae ba dawowa zaiyi ba, ya salammm ni bansan meke faruwa dani yau Ba

 

Hannu hafsat tasa ta kar6i wayar, ta amsa kiran sannan takara a kunnanta tana zabga Sallama,

 

Janar ishaq ya amasa mata da cewa “Wa’alaikum salam my daughter, ina mommynki take ne, i ave been trying her phone number tana ringing ba’a ɗagawa why”? Ya tambaya yana jiran amsa,

 

Murya na rawa hafsat tace “am..dama…umm…tabar wayar a ɗaki ne ina ji, saboda ta shiga kitchen,

 

tayi maganar tana kallon mommyn nata data ke faman dafe zuciya,tana sauraron mai zai ce saboda wayar na a handsfree,.

 

Genar ishaq yace “shikenan ki sanar da ita cewa cikin week ɗin nan zan dawo insha Allah,”.

 

“Shikenan daddy Allah ya dawo daku lafiya,” sukayi sallama ta ajiye wayar tana faɗin “Tabɗijan Can akwai matsala fa,”

 

Aunty babba kuwa miƙewa tayi tana faɗin “Nashiga uku ishaq zai dawo ga zuwan Omar yau, bansan me zan fuskanta ba a wurin kowannan su… ‘.

 

Muryar hafsat ce ta katse ta da cewa “Amsar fa abayyane take mommy, ke ma kin sani Allah,saki ukun nan sun Wajaba Akan ki muddin Abba yaji abunda kika aikata, saboda wancan karan Ladi mai aikin mu da kika ma bugun mutuwa sai da ya aika ki maiduguri bayan marukan da kika sha awurinsa ina ga waɗan nan bayin Allahn da kika naƙasa har Su biyu, gasky mommy kin shiga Uku, ga kuma ƴa Omar zaizo ni addu’ata Allah yasa Abba kada ya sake ki yabarki kawai da hukuncin Omar na zuwa prison kowa ma ya huta…..

 

Hankali tashe aunty babba tace”Hafsat prison fa kika ce? So kike akaini can kin gaji dani kenan”?

 

Rai a6ace hafsat tace “dole nagaji dake mommy, duk ke kika ja mana wannan masifar da muke ciki muna zaman lafiyar mu,’ ta faɗi a ƙuke hada buga tsoki kamar bada uwarta take magana ba,

 

Jinjina kai aunty babba tayi batare da tace komai ba, adai dai time ɗin dr ya fito daga ɗakin da aka kwantar dasu hosana, jiki na rawa tabishi tana faɗin “dr ya jikin nata ta farfaɗo,”?

 

dr yace “Alhamdulillah tafarka yanzu haka bacci take yi itama saboda allurar da nayi mata,”

 

ɗaga hannu tayi tana cewa “Alhamdulillah har naji ɗan sauki, amma dr babu yarda za’ae ciwon fuskarsu ya warke nan take? kumburin ya sa6e, ni dr kodai surgery za’ae musu ne acanza fuskar,’ tayi maganar in serious matter tana kallon shi,

 

Wani irin kallo dr ɗin ke yi mata yama rasa amsar da zai bata,

 

wuce wa gaba yayi ya tunkari Office ɗinsa yana cewa “sam Bazaiyiyu ba gsky,ba muyin irin wannan aikin anan, kuma fuskarsu batayi komai ba da za’a canza musu Ba,da alama madam kema kina buƙatar Aduba ki,’ sarai taji abunda dr ɗin yace amma bata ji zafin maganarsa ba, saboda bata cikin natsuwarta a yanzu,

 

Yini su kayi cikin fargaba ba salla ba salati dama ba ita bace agabansu ba, an saba haɗa salloli ayisu a lokaci guda,Saboda duniya aka sa agaba Ba lahira ba,

 

gajiya su kayi gaba ɗayansu da zaman asibitin ga uwar yunwa kamar suyi hauka, ga zullimi da fargabar zuwan Omar, ganin har Magrib tayi babu kiran Omar yasa suka fidda tsammani da zuwan shi,

 

Ƙarshe basu jira dr yayi discharge ɗinsu ba, aunty babba ta ɗauko hosana dake kwance saman gado agalabaice ta sa6o ta a kafaɗarta ta fito da ita, sai cikin mota ta kwantar da ita, Jahad ma tashiga motar baiwar Allah ga zazza6i tana ji, gashi dr yace suna buƙatar jini su duka biyun amma babu yarda zasu yi, rayuwarsu a tagayyare sai yarda akayi dasu,

 

Shiga motar hafsat tayi mazaunin driver aunty babba na gefenta suka ja motar suka bar asibitin, a time ɗin har dr ya biyo su da sauri sauri don ya dakatar dasu amma ina tuni har sun bar arean asibitin………….

 

A tsiyace ta shiga da motar cikin gidan tayi parking ɗinta, tana fito wa ta wuce ciki saboda jirin da take ji na yunwa, fitowa itama aunty babba tayi sam bata tsaya taɗauki hosana ba ta shige ciki itama,

 

Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba ganin sun tafi sunbar hosana kwance sai faman nishi take saki numfashinta na fita daker-daker,

 

bata son yaya zatayi ba ta ɗauke ta saboda itama babu sauran ƙarfi ajikinta, fitowa tayi daga cikin motar tana faman zubda hawaye, Iya cuta dae an cuci rayuwarsu,

 

Ganin yarinya tsaye abakin mota yasa wani soja ƙaraso wa yana faɗin “Lafiya dai ƴan mata meke faruwa ne,”

 

Cikin shessheƙar kuka jahad tace “ƴar uwata ce ciki kwance bata lafiya bansan yarda zan shiga da ita ciki ba,”

 

Sojan yace “Can I help”? Jahad tace masa “eh” saboda bata da wata mafita da ta wuce hakan,

 

Buɗe motar yayi ya zura hannunsa ya sungumo hosana dake kwance magashiyyan ya ɗaurata a kafaɗarta ya shige da ita ciki jahad ta bi bayansa,

 

A saman 3 seater ya kwantar da hosana, jahad tayi masa godiya sannan tasamu wuri daga ƙasa ta zuƙunna fuskarta na dai-dai saitin ta hosana,

 

Hawayen fuskarta har ɗiɗɗiga suke yi a fuskar hosana, addu’o’i tashiga karantowa tana tofa mata,.

 

Duk hosana na jinta tana so ta buɗe idonta amma ta kasa saboda kumburar da su kayi, tana so ta buɗe bakinta tayi ma Jahad magana amma tagaza saboda haƙoranta kansu sun raunata sosai don ba’a rasa mai girgiɗi acikinsu, ga la66anta da sukayi suntum sam bata iya motsa su,

 

Cikin kuka jahad tace”Hosana na sani nasan akwai abunda kike son faɗa mun amma kin kasa, kada ki damu ina jin duk wani raɗaɗi da kike ji azuciyarki, inaji inama ace zan iya ɗauke maki zafin ciwon da kike ji da tuni nayi wlh…….taƙarasa mgnr tare da kifa kanta ajikin hosanna,sun jima a haka wulaƙance babu wanda ya leƙo su, sai daga bisa ni hafsat tafito har tayi wanka da alama ta canza kayan jikinta, doguwar riga ce tasanya har ƙasa, ta ɗaure gashin kanta,

 

Binsu da kallo tayi gwanin ban tausayi ita kanta duk rashin imaninta yau ta tausaya ma twins ɗin,girgiza kai tayi tare da wuce wa ta nufi kitchen,

 

Jim kaɗan sai gata ta fito hannunta ɗauke da tray mai girma, Tea set ne ɗauke asaman shi, sai French toast ɗin da ta hado masu dashi da sauran snacks, duk da tasan ma daker zasu iya ci

 

Bedroom ɗinta ta shigar masu da shi ta ajiye Tray ɗin asaman table ɗin dake a dab da gadonta, Sannan ta fito ta nufe su jin takun tafiyar hafsat yasa jahad ɗagowa daga kwancen da take tana kallonta da rinannun idanuwanta da suka jigata,

 

Hafsat batayi mata magana ba hannu kawai tasanya ta cicci6i hosana ta ɗaura a kafaɗarta sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinta tana cewa jahad “Ki biyo ni,”

 

Cikin sauri jahad ta tashi tabi su cikin ɗakin, kwantar da hosana tayi asaman shimfiɗeɗen gadonta, sannan ta juyo ta kalli jahad tace “Ga tea nan da snacks nasan kina jin yunwa ki ɗaure ki sha,’

 

Girgiza kai jahad tayi tana cewa “Bazan iya cin komai ba,

 

“Soboda me”? Hafsat ta tambaya tana kallonta,

 

Jahad tace “Sabodo ƴar uwata, bata ci komai ba,idan naci ita kuma fa”?

 

Shiru hafsat tayi jikinta yaɗanyi sanyi aranta har tana mamakin dama har yanzu akwai ƴan uwa masu ƙaunar junansu haka aduniya? Jinjina kai tayi kafin tace ” kada ki damu, zan ƙara dubata yanzu insha Allah,zata ji sauƙi,”

 

Shiru kawai jahad tayi,amma fa ba zancen Cin abinci agare ta muddin hosana bata ji sauƙi taci ba itama, sai dae yunwa takashe ta,

 

“Ave a seat,” hafsat ta faɗi tana nuna mata saman gadonta,

 

Jahad tace “Ina so nayi sallah tukunna,” ta6e baki hafsat tayi tana cewa “okey ga toilet nan ki shiga,”

 

wuce wa Jahad tayi ta shige toilet ɗin tana rufe ƙopa tafashe da kuka mai cin rai tunaninta yanzu shine yarda zasu gudu daga gidan gaba ɗaya, don yanzu ta kwammace Su ƙare rayuwarsu a titi akan su faɗa hannun wani, tunda abun nasu ba sa’a kowa baisan taimakonsu don Allah batare daya cutar dasu ba,mutun huɗu kawai tasan suna da kyakkyawan niyya akansu, tsohuwa wadda Allah yayiwa rasu sai Goggon katsina da aunty saude da Yaya Omar ɗinsu…..

 

hafsat na jiyo kukan jahad dake acikin toilet, jikinta duk ya ƙara mace wa, karo na farko da ta fara jin tausayin wani aduniyar nan,

 

gaban mirror ɗinta taje wata roba ta ɗauko ta magani na shafawa a ciwo mai kashe raɗadi,

 

Dawowa tayi ta zauna saman gadon ta buɗe murfin tasoma lakuto shi tana shafa ma hosana a fuskarta, cikin lokaci ƙankani wurin yayi mata wani irin sanyi tamkar an ɗebe ciwon,

 

“Sannu ya jikin naki,” hafsat ta tambaya tana kallon hosana wadda ke ɗan buɗe ido a hankali, sam ta kasa magana,

 

pillow hafsat ta janyo ta sanya mata kan gadon,sannan ta taimaka wurin tada hosana zaune ta jingine ta ajikinsa,

 

jikinta sai faman kerma yake yi, cup hafsat ta ɗauka ta shiga haɗa mata tea,bayan ta kammala ta sheƙa mata dashi da wani kofin donya rage zafi daga bisani taimaka wurin bata abakinta, la66anta har rawa suke yi wurin buɗesu saboda wata irin mahaukaciyar yunwa da take ji, sosai tasha tea ɗin kaf tashanye har dae hafsat ta ƙara haɗa mata wani ta bata,

 

Jahad ba ƙaramin sanyi taji aranta ba ganin yadda hafsat ke kula da hosana tayi mamakin yarda take bata tea abakinta, tsayawa tayi tana kallon su har sai da hafsat ta juyo ta kalle ta tace “ki buɗe closet ɗina akwai hijab ki ɗauko tare da Sallaya,”

 

Bude wa jahad tayi ta ɗauko hijab tasanya sannan ta shimfiɗa carpet ɗin tashiga yin sallah Hada isha’e tayi wadda ake cikin kira,

 

Daker hafsat tasamu hosana taci kaɗan daga cikin snacks ɗin data kawo mata saboda ciwon da bakinta ke yi mata, tea ɗin dae ne tasha sosai,

 

Gyara mata kwanciya tayi, sannan ta sanya bargo ta lullu6e ta,

 

tashi tayi ta koma saman doguwar sofa ɗin dake facing gadonta ta haye sama ta kwanta itama,.

 

Bayan jahad ta kammala sallar ta ninke mata abun sallar da hijab ɗin ta mayar dasu inda ta ɗauko su,

 

Sannan ta koma saman gadon ta haye, ta soma haɗa tea ɗinta tasha tana ci tare da french toast ɗin da hafsat ta haɗo masu, sosai taci don bata rage komai ba duka ta lamushe,

 

Bayan ta kammala ta shiga cikin bargon da hosana take ta kwanta itama, janyo ta tayi jikinta ta rungume ta tana kiran sunanta “hosanna ya jikin ki”? Har yanzu akwai raɗaɗi ko”?

 

daker tace “Eh,”

 

Jahad tace “kiyi haƙuri kinji, insha Allah bazamu ƙara shan wahala ba,inaji araina komai ya kusa zuwa ƙarshe bansani ba ko mutuwa zamuyi ba shine sauƙin mu Allah kaɗai yasani,

 

saurarawa tayi don jin mai hosana take cewa, saboda fuskarta na’a kwance achest ɗin jahad,sam sautin bai fita sosai

 

“Bana jinki hosana, kibar magana kawai kada ciwonki ya ƙara raunana,”

 

Shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, bakomai take son faɗama jahad ba face sunan YA OMAR da take kira……………………………….

Abban Sojoji Complete Census Education Free browsing Hausa Novel Hausa Novels Hot Romantic Hausa Novel Idan ba ke Kannywood Maganin sanyi Mtn Scholarship Sirrin rike miji Tusar gaba Wace ce ita warin gaba warin kashi Zafafa 2023

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button