Daudar Gora Book 2 Page 118
Haysam, tadai samu ciki sau daya ya lalace bama ya haura wattani uku ba, harma Waheeda itama acan bata haihu ba. Nata bai damu kowa ba, amma na Haysam an fara kanan magana akan sai ya kara aure kasancewar shine Miran mai jiran gado. Bai son kara aure, amma mahaifinsa ya takura masa, ya nema damar a basa lokaci zai nemo da kansa. Anan kam sai ya bashi dama. Ba’a rufa watanni uku ba kuwa ya kawo sunan Bushirat, ta kasance kanwa ga wani abokinsa da sukai karatu, amma suma yan nan kasar ruman din ne, sannan kuma manyan mutanene dan mahaifinta babban malami ne masani sosai. Kyakykyawar nasabarta yasa bamu wani tsananta bincike ba akai biki. Sai dai me itama shiru, dan garama Ashwaq ta taba bari sau daya.
Shekarar Bushirat biyu a masarautar nan itama babu labari sai ma Ashwag din ce dai ta kara bari, dan haka aka sashi ya kara auro Danish-Ara, cikin ikon ALLAH Danish-Ara bata rufa wata guda ba sai ga ciki da ga Bushirat. Kowa yayi farin ciki sosai musamman ma shi da ita da mu kammu, hakama Ammarah kai kacema ita keda cikin, dan gaba daya ta tattara ta koma sashen dan uwanta tana kula da Bushirat. Bamu hanata ba, duk da rashin aurenta na damunmu, sai dai mun fahimci akwai matsalar junnu tattare da ita, dan haka muka dage da addu’a gareta kawai”
.”An haifi ciki lafiya, kuma da namiji sanbalele da yaci suna *_Eshaan_*, Eshaan kyakykyawan yaro mai lafiya da ban sha’awa ga kowa, ga
shiga rai. Wata irin makauniyar soyayya Bushirat ke nuna masa har takai Ni kaina sai nayi da
gaske nake ganinsa, hakan da take yasa Waheeda yimata tas kafin ta dan canja aka
dinga kawomin shi nan. Ya taso yaro mai wayo, miskili da baka iya gane abinda yake so ko baya
so sam. Shi ko irin abokan wasan nan na kuruciya Eshaan bayayi, yafi so ya zauna shi kadai shiru ko yayta karance-karancen
abubuwa musamman a litattafan tarihin wannan daula da suka shude. Sai dai yana
matukar son wasan doki da basket ball, da wasan takobi, idan kuma yana tare da Kakansa
ko mahaifinsa zaki dingajin maganarsa ko babu yawa. Al’adar wannan masarauta da Miran mai jiran gado ya kai shekaru bakwai zuwa goma
ake kaishi can wani boyayyen waje ya rayu har sai girmansa, ko kuma sarki ya zabi murabus
kafin ya mutu shi ya daurasa, idan kuma bazaiyi murabus ba za’a dawo da shi cikin masarauta
da iyalansa dan su basa wuce shekaru ashirin basuyi aure ba gaskiya. Shiyyasa sai kiga yaro
ya taso mahaifinsa bai wani tsufa ba. Da farko Bushirat ta tsaya tsayin daka akan baza’a rabata
da danta ba, nima kuma na bata goyon baya dan banji dadi ba sanda aka rabani da Haysam,
sai dai was tsurface-tsurfacen tsafi da Uwa ta fara kawowa a kansa yasa nace a kaisan, ta
nuna bakin cikinta sosai akan hakan da nayi, har tai gargadi mai girma akaina da cewarta ni na
cika shiga mata hanci ni da zuri’ata. Sam wani kurarinta da tsubbace-tsubacenta basa bani
toro, dan da UBANGIJI NAna dogara akoda yaushe. Dan haka na cigaba da dagewa har sai
da Tajwar Abdul-majeed ya yarda aka kaisa kasar Cuba. Haukane kawai Uwa da Bushirat