Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 15

Sponsored links

Ni Kuwa cike da murna na kwana da sassafe Ina idar da Sallar Asuba wanka nayi da ragowar sabulun wankina na wanke fuskata tas duk da na dan canja sabo da yawon bara a rana,kayana dana jiya na wanke su tas jakata na dauka Yar wayata na Kira Saratu kawata tana shiga Kiran duniya ba a daga ba,nace ya zanyi haka Zan tafi Kawai,sai dana jira 8am tayi na samu na karya sannan na tambayi wani me Napep inda ake shiga motar su Anambra ya kaini Kuwa har can irin inda ake shiga mota haka Ina zuwa aka saka ni a motar Onitcha direct duk haka Ina ta Kiran Wayar Saratu amma taki dagawa Kuma tasan number ta haka mota ta ja Muka tafi,mun biya kudin mota tuni harda Yar ragowar kudina na adana abina cikin aljihun doguwar rigata domin sanye nake cikin doguwar rigar wani material orange rigar harda aljihu shine a kayana me Dan dama dama Yana min kyau,na yafa dan karamin mayafina,tunda muke kwarara tafiya nake uban bacci na farka na koma cike nake da nishadi Kamar ba gobe, sai tsakar dare Muka Isa Wanda mafi yawa a tasha muka kwana,in Banda turanci da Kuma pidgen English sai yaren Igbo shi Kawai ke tashi, gaba daya a tsorace nake,na matsu na ga Saratu nace yanzu Saratu dan masifa ta iya Zama a garin nan ko tsoro bata ji Kar fadan arna da musulmi ya barke a halakasu, gashi bana Jin turanci,Fitowa nayi daga tashar ba Wanda ya saurareni kowa Harkar gabansa yake yi, Napep na gani na tare iya sunan street din na iya fada masa yace you be Hausa? Yana cewa Hausa na washe baki na daga Kai sama kamar naga Dan uwana bahaushe,shiga nayi ya Fara tafiya Naga haduwar birni gidaje na gani na fada Muna tafiya Ina ta farin ciki,a fili nace yanzu nasan nazo birni, Birni na shigo,Yan Kudu gani sunana Rabi ae Rabi me zamani dariya na saki hahahaha kamar sabon kamu,nace wuhuhu kuturun dosan uwa ana bala’i a kudu, na nuna wasu Yan Mata da yatsa nace kalli cinyoyi Kai cinya a waje haka da Dan wando gajere wasu da mini sun Sha takalma masu tsini,na saki ihu nace yehoho ana tsiya nayi tafi da hannayena nace naga waje.

Munzo wucewa ta wata GRA nace wuhuhu Kai Saratu lallai kinci gaba haka Zan zauna a katon gidanki,bani ba Arewa dole sai nayi kudi inzo inyi ta aikina in tara kudi ba inda zanje naga waje,Kai Rabi kin dace Ina magana da karfi Ina dariya Ina zazzare Ido Ina nunawa da yatsa Ina ta kallo,Me Napep bai San me nake cewa ba, tafiya mukeyi kamar zamu bar gari tafiya taki karewa tun Ina nishadi har na gaji nace Allah dai yasa yasan unguwar da nace,tafiya akeyi na gaji ma tun Ina magana har na gaji nayi shuru ga yunwa na cina,cikin birnin naga mun bari munzo wasu unguwanni Ghetto area unguwar talakawa da Yan jagwal badan ginin bulo bane da yawa sai nace kauyenmu yafi nan komai da komai.

Sai da muka zo daidai wani lalataccen gida yayi parking Yana min alama da na fito,Ina mamaki na fito dauke da jakata a Hannu nace ya za ayi ka kawoni kauye ni da nace birni dan mugunta sai da ka wuce duk wurare masu kyau sanna ka kawo ni lalataccen wuri ni nasan wacce nazo wajenta baza ta zauna a nan ba Yar gayu ce me kudi tace Mansion ta gina a birni wata ce ta karaso wajen tana Jin hausa da alama ma bahaushiya ce itace ta tambaye shi da turanci meke faruwa? Yace shi bai San me nake cewa ba,tace ke meke faruwa? Ina masifa nace Odimgbe Street nace ya kawoni shine ya kawoni kauye Kuma wajen kawata nazo Saratu Amma kamar ana kiranta da Seraline,nan take matar ta sheke da dariya tace nan ne Abeg dauki jaka ki Shiga ciki kice a nuna Miki dakinta ki jirata, Ni dai nace Yar gayu ce fa me kudi ce kawata matar ta sake shekewa da dariya tace bawa me Napep kudi dalla malama kinzo mansion din Sera,Ina mamaki duk na hada zufa na biya me Napep kudi na Shiga ciki,matar ta rakani wani dan daudu ya shigo Yana karairaya yace wannan fa daga Ina haka? key zaka bata na dakin Sera zata jira ta bakuwarta ce,shewa Dan daudun yayi tare da furta ahayye daga Kauye amma wannan za’a kwashi gara,nidai mamaki nakeyi Dan yanda Naga Saratu ta hadu bazan taba yarda a irin wannan gidan take ba, gidane baida Fadi sai tsayi zururu daki daki sunfi ashirin ko wacce kofa na facing wata kofar dakin,tsakar gidan siminti duk gidan Kuma bandaki guda daya ne tal dakunan Kuma harda Yan daudu mutum uku a gidan,duka layin unguwar Haka gidajen suke unguwa ce ta karuwai arna da musulmai da duk wani yare a kwai a unguwar, kidane iri iri ke tashi Mata ta ko Ina gasu Nan da kyawawa da munana duk da shigar banza wasu sabo da kyau sai kace mene ma ya fito dasu amma haka aka bude min dakinta na shiga.

Dakin nake karewa kallo da tiles dinsa sai katuwar katifarta da fanka irin ta kasa sai akwatunan kayanta a gefe,can barin Kuma Gas ce karama da duk wani kayan girki na bukata akwai shi,Babu wutar nepa Sanda na shiga sai zafi kamar zai kashe ni na jike da zufa haka na zauna na buga tagumi Ina kallon hoton wani katon gida me kyau manne a bangon dakinta,Daya barin Kuma katuwar poster ce ta batsa Namiji ya rungume mace babu Kaya a jikinsu ni dai kunyar hoton ya kamani na daina kalla na sadda kaina kasa,gajiya nayi da Zama na fito waje na samu a tsakar gidan wasu suna shan giya,wasu sunyi group kayan maye suke sha,wasu suna ta busa wiwi,wasu Kuma suna ta buga chacha sai bina suke da kallo suna kus kus gasu duk matane sai Yan daudu a cikinsu da wasu tambadaddun mazan,Ina juyawa wani yace Kai ji Duwawu dan Allah bakuwar Sera ce,wata inyamura ta kalleni tace Ohh Jesus see her back nidai fita nayi daga gidan da ko kofa babu bare a rufe a jikin wata bishiya na tsaya Ina kallo yanda karuwai ke hada hada wasu suna rawa kamshin girki sai tashi yake,inda nake tsaye Me POS ne wani tattirin dan duniya hancinsa ya saka barima har waje uku,kitso ne a kansa kana ganinsa kasan ya gogu da bariki,yace ke ya sunanka? Yana Jin hausa amma ba sosai ba dake Wai ya zauna a Jos,

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button