Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 123

Sponsored links

lya karfi da budewar murya Jasrah ta daddage ta kwalla wata irin kara na firgita, dan ganin jini ya wanke fuskar Ameera Haifah ga Mijinta shake da wuyarta sai ta dauka ta mutu.Wani irin wancakalar da Haifah Miran Arshaan yayi yana duban Jasrah data yanke jiki ta fadi. Har rige-rigen shigowa hadiman masu tsaron sashin keyi, ganinfa abinda ke faruwa tuni wani ya firgita ya kyalla a guje ya sanarma jami’ an tsaron gidan dan wannan faninsu ne…

Tofa dan-dan-dan, da alama dama irin wannan damar Iffah ke jiran samu, dan cikin

kankanin lokaci duk da darene masarautar ta dauki dumi, yayinda aka kwashi Ameera Haifah da Jasrah zuwa asibiti, Miran Arshaan kuwa da jikinsa ke tsumar toro gaba daya ya gama

gigicewa, dan sai zuwa yanzu ya dawo a hayyacinsa. Tuni kuwa ya tsure da ganin abinda ya aikata, sai kawai ya bige da borin kunya.

Sudai jami’an babu wanda yace da shi komai,sun tattara komai akan sai zuwa da safe za’a kai

maganar ga Shahan-shan. Abu dai mafi daure kai shine miye tsakaninsa da Ameera Haifah din

har haka a irin wannan tsohon daren, dan a kala fa karfe biyu na dare kenan.

A lokacin da duk ake waccan dambarwar anan ta-kurya ce ke ganawa da manomin ganyayyakin shayin Shahan-shan. A cikin badda kamarta take, dan haka shi bai san wacece ba.Hasalima magana da Jazaa sukeyinta ita dai tana hakimce komai batace ba. Da farko yaso ya, amma ganin wata lukutiyar jakkal da zinare ga barazanar halaka zuri’arsa kunne tuni ya mika wuya akan an gama. Malikat Bushirat tai murmushin basawa ta dauke kanta.Kwalayen ganyen shayin da uwa ta kawo kan ya fara kaiwa sashen Shahan-shan din kafin wanda zasu noma ya tsiro nan ma Jazaa duk ta ajiye masa su har uku..

Zaune take bayan idar da sallar asuba, yanda ta kurama waje daya ido zai baka tabbacin tunani take. Sai lokaci zuwa lokaci da takan saki murmushi, harda cusa kanta cikin kafafunta kamar mai jin kunyar wani da ke gabanta. Ta dan jima a hakan kafin ta mike kamar wadda aka tsikara idonta kan agogon dakin. Tasan yanzu kam yana Gym ne tunda har ya kai yanzu bai shigo ba. Itama tsaf ta shirya cikin kayan motsa jiki ta, sun mata matukar kyau da fidda ainahin surarta komai dam. Dan wani bana ta saka a kanta siriri kalar kayan sannan ta daura talda daura after dress saman sport wears din. Shiru tai tana bin Gym din data shigo da kallo, babu kowa komai ma a kashe yake, da alama banan yazo ba. Fuska ta dan bata da tura baki gaba, har zata koma sai kuma ta tuno randa ta samesa a can sama yana wasan takobi shi da Miran Arshaan. “Yes!” ta fada tana wani kashe ido daya da yin juyi sannan ta nufi can cikin takunta na nutsuwa,

Shelanta sunanta da na’urar kofar tayi kamar yanda ta saba duk wanda zai gitta ta cikinta ya sashi dakatawa da jujjuya takobin ya juyo a hankali. Tuni hadiman wajen sun jujjuya bayansu sukam. Yanda take takowa garesa kamar wata tarwada yasa shi gagara cigaba da abinda yake yi.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button