Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 41-42

Sponsored links

Nawwar ma Yana komawa ya sanarwa da Baffa,Mami da Papa sai Iyamami tana ji tace karya ne Kawai dan ace Ina da iyaye ne ba shegiya bace, yaushe za a jefar da yaro tun Yana jariri kuma ace an ga iyayensa ai karyane.

Umma dai ana ta tayata murna ranar da nayi kwana na hudu sai ga Santana,Star, Wise,Seraline,Mandula,Yar Zabil ma da mijinta Suka Zo min a ranar suka samu su Bilkisu duk sun zo Muna hira sai gasu.

Star ce ta shigo ta Sha shadda nace Yan banzan sun dira,Wise ta shigo itama taci wani material me tsada,Sera ansha leshi,Mandula Kuwa Arabian gown ta Sha,Yar Zabil ta Sha material,Suna shugowa Nazira me kaunar su Star tace Ina tauraruwa take,Na nuna mata Star ta ruko hannunta ke shu’uma ta wajena shugo,dariya ta Kama mu,Umma tace ita Nazira ai bata San tayi abu kadan ta hakura ba,Star ta kalleni tana dariya tace Aunty ce wannan? Nace ae ta tsaya a gaban Nazira ta Mata yanda sojoji keyi tace I salute you ta Sara mata harda kamewa a gabanta,Wise tace Ina Auta na? nace yanzu ya fita ta kirashi a waya tace Auta na zo fa,yace to zanzo ai na ganki Ina kofar gida kuka wuce.

Santana da mijin Yar Zabil suka ce da Auta tsohuwar budurwar ce ne? Yace itace ta nace min, ni Allah da yayoni bana son harka da matar aure ba kyau,shi a dole saurayi..

Bilkisu tace wace Seraline ta Amana? Sera tace yes ma gani harda daga hanu,gida duk ya rude taron Mata,Umma suka tsuguna Suka gaisar tana ta musu godiya Jin Muna ta hira tace bari taje ta yo barka makwafta ta dawo ta fice ta bamu waje,Uwa Kawai shewa take ji,Nazira ce ta fito da maganin Mata Wai ashe tana siyarwa, tace Mata masu aji ga kayan aiki fa harka sai da gyara,a gyara ko Ina a kwalkwale a kwatalle hanyar Oga,Madula tace ban mu kashe ta wajena za aje dake irinku nake nema, Yar zabil tace ni har na hango ma Kalar nawa,Wise tace to mu masu juna biyu sai mun haihu ai ko? Nazira tace ae gaskiya kina haihuwa kiyi magana yarinya na hadaki sai ya manta Hanya kofar gida,Aunty Bilki tace Allah ya shirye ku girma ya Fadi ke Kam kullum bakya girma,Duk suna da aure harkar nan duk mun santa kema fa kina sadadowa a baki kyauta jarin Nawa duk ba ke kike karya min jari ba ke da Nazifa,to tona Mana asiri ki huta,su Omaira suna tsakar gida su yara ne muka kore su, Star tace dan Allah ku bani Wanda Malam zaita kiri’a iri iri,muka yi dariya, Nazira ta zaci mu irinsu ne masu kunya sai taji ta tono abinda yafi karfinta Iskanci Kawai su Wise suke tsulawa,Bilkisu tace karfa Umma ta dawo bamu sani ba,Seraline tace Kakar su Miracle tana jinku,Ba itace ta jefar da Miracle ba? Star ta tambaya,akace itace tace to ku rabu da ita tayi ta ji irin Iyamami ce,Wise tace wlh basa saduda sai sunji wuya.

Uwa tana jinsu ta leko tace Wanda ya zageni Allah ya Isa,Nazifa tace ta ciki kema, shegu Yan Iska watsatu cewar Uwa,Star da shigigi harda yiwa Uwa kukan Saniya mooo mooow Wai itace Saniya,Bilkisu ta bude baki Yara da shishigi sai kace gidansu,Uwa tace kinwa uwarki itace Saniya,Bilkisu tace ku kyaleta yanzu sai ta hadamu da Abba yazo ya kore mu,Muka rabu da ita tana ta masifa Muna surutunmu Muna labarin duniya kowa yaki saurarta tace kun share uwarku shegu haihuwar tsiya,ba Wanda ya kulata har ta gama ta koma daki ta fashe da kuka Jin muryar Abba ya shigo,ya karasa ciki Yana tambayarta lafiya? Su Bilkisu ne Suka zazzagi iyayena Suka ce min jaka,Abba ya fito a fusace yace duk ku fito ku bar min gida,Nace a bangaren Umma muke ai mu ba a naka ba,Uwarku ce ta gina min gidan shima ya dinga sababi ba inda Muka je sai kyale mu yayi har Umma ta dawo,Da kanmu mukayi girki,Auta Yana tare da Mijin Yar Zabil da Santana sai Yamma likis su Star suka ce zasu tafi dukkansu kowacce dubu ashirin ta bawa Umma kyauta Suka tafi.

Washe gari Nawwar,Baffa,Mami,Papa,Iyamami sabo da shishigi tace sai tazo taga karya,aka zo da ita Kuwa tana cin magani tana gadara tana cika tana batsewa,Mami Suka shugo aka gaisa,Mami tace ba shakka tabbas Rabiah jininku ce ba tantama ga Kama nan,ana ta hira ta barke Iyamami Harare Harare Kawai takeyi ta ta tashi ta fito sai ga Uwa ma ta fito daga dakinta, Suka hadu Dattijan banza,Iyamami tace an likawa jikana gayyar tsiya karuwa ga talauci,Ashe Iyayen nata ma matsiyata ne tazo gida ta kankane shegen gidan nasu Kamar na tsohon tuzuru Wanda ya Dade ba mata,Sai Uwa taji haushi kuma shi yasa akace duk tsiya naka naka ne,tace mene da zuriar tamu bamu fiku asali ba ma,sabo da Kuna da kudi karki manta akwai me kudi akwai me arziki fa,Yara ma kyawawa Kamar yayan larabawa ke in Banda kaddara ma waye zaice wannan Auta da Nawwar jikokinki ne kalleki fa baki Kamar zunubi,Iyamami tace ke Iya gyara zancenki ruwan zafin wankan jego ne ya dishe Mana hasken ki taka a Sannu Zan sa a batar min da ke talakawan banza matsiyata.

Uwa takaicin haihuwar Mata ya sake kamata a ranta tace kalli ta haifi maza duk gasu nan sun Zama attajirai mu Kuwa shegiya Uwar Yaya Mata ta cika Mana gida da Mata gasu nan ba me tashin wani,a fili uwa tace Banga laifinki ba Dan kin Mana gori mu matar da Dana ya aura itace ta haifo Mana Yara duk Mata shi yasa Babu me tashin wani dukkansu talakawa suke aure da ta haifo mana maza ai da ba haka ba,Iyamami tace ji Jahila dan Allah ji Hahila to Yaya matan mene da su,Kece babbar Jahila da zaman aure kin Hana yaranki da jikokinki kin takura sai wacce kike so za a aura ai munji labarin komai ke sai dai ayi auren zumunci da ba a auratayya a bare da duniya za a samu dangi daban daban ne sai kace Zamanin Annabi Adamu kice ke dole sai a danginki za ayi aure dole,uwar banza me hada yaranta fada da Raba Kan Yaya,Iyamami a ranta tace wato Rabi zuwa tayi tayi gulmata wallahi sai taci ubanta zata dawo ne,a fili Kuma tace ai gwara ni ba jayayya nake da halittar Allah ba ke dai kice Allah ya baku na gari ke ba macen bace ke yanzu in kina da hankali ma kyace Kar a haifi mace kina macen tsohuwar alagwan Gwan.

 

 

 

Santana da mijin Yar Zabil suka ce da Auta tsohuwar budurwar ce ne? Yace itace ta nace min, ni Allah da yayoni bana son harka da matar aure ba kyau,shi a dole saurayi..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button