Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 38-39

Sponsored links

Auta yace you see.. you see hakki ne yake binka itama ba itace ta bawa kanta ba Allah ne waye ya Isa ya ja da Allah,shi fa Allah ba mate din kowa bane da za a dinga yiwa mutum baiwa Yana rainawa wannan shishigi ne da Butulci ake wa Allah,Allah waye ya Isa yayi abu ya zauna yana cece kuce me yasa da ya baka ji da gani ya baka iska kyauta kana shaka baka ce laifi bane,sannan ya saukar da ruwan samu muyi shuka mu samu abincin ci shi wannan duk dai dai ne ya baka haihuwar Namiji shima dai dai ne amma mace ita ba Allah ne yayita ba,ka godewa Allah ma da ya baka yaran idan ka mutu ka samu me maka addua.

To Addua ma tana yankewa bawa idan ka mutu mutane da yawa zasu dinga tuna halinka na kirki suna maka Addua da Yan Uwa da yaranka,bayan nan kowa ya manta da kai a hankali sai yaranka ko Wanda kuke uwa daya uba daya a Zamanin nan ba kowa zaiyi Sallah ya tuna da Kai ya maka Addua ba sai yaranka daka bari Ashe baza ka godewa Allah ba?

Ni ka ganni magana ta Allah kullum tunanina yanzu ya za ayi nayi aure da matata da yarana, mu maza shine a ranmu Mata Kuwa kullum iyayensu da danginsu suna ransu,me yasa kake fito na fito da Allah ba a fito na fito da Allah wlh baza kayi karko ba tuni zaiyi fata fata daku gwara tun wuri ka tuba kayiwa yaranka Addua na gari ake nema ba wani sai mace sai namiji,in Banda karfin hali ma Abba karka kace na maka rashin kunya gaskiya ce Kai fa Kawai manniyi ka zuba Allah ne yayi sauran aikinsa har ya tantance Da a ciki ka samu mata ba abin a gode Masa bane wa zai iya wannan aikin sai Allah iyakaci fa kawai kaji Dadi ka fitar da kazanta Allah yayi halitta Kai in ba Allah ba sauro wannan wa ya Isa ya halitta bare Dan Adam me daraja Kuma mace haba Abba ai mace duniya ce, mace ta haifeka ta raineka ka girma,kazo ka auri mace kaji Dadi da ita ta baka farin ciki sannan aka zo aka sake baka Yara Mata ka musu tarbiyya ka aurar da su bi Allah a saka a Aljanna,ga Jin Kan iyaye su taimakeka su tallafa maka su share maka hawaye,gaskiya ka daina yiwa Allah tawaye ba a ja da Allah magana ta gaskiya fa.

Abba yace gaskiya ka fada yaro kana da hankali Kuma ban taba ganin yaro me tunani irinka ba amma ni zuciyata tafi son namiji,Auta yace shike nan Kai da Allah ba ruwana,Abba yace Kai yaro dalilin da yasa fa kaga na tsaya Ina saurarka sai dan Kai Namiji ne Ina son Yara maza shi yasa nake saurararka me ka sani ma a duniyar yaushe aka haifeka?

Abba yana ganin wasu yara maza Yan dagwai dagwai na makwafta ya kafe su da Ido Yana sha’awa Yana wani washe baki,yace Yara manyan gobe kaga mazaje yace kuzo,Suka karaso ya basu hamsim Hamsim kyauta sabo da Kawai maza ne,har awara da alawa zaka ga Yana siyawa Yara maza,Yan mata Kuwa idan ya gansu tsakaninsu harara ce da bakar magana.

magana nayi nace Auta jiranka fa nake Yi kazo mu tafi ko baza kaje gidan su Aunty din ba,yace gani nan ya taho Muka rankaya tare,Rahma da Raheema,Omaira tana gida tana aiki,Auta na mikawa jakata nace ungo kayi duty din yayanka,karba yayi yace ya zamuyi an mallake mu duk kin Mana barbade mun cinye a abinci,an rubuce mu tsaf an shanye,dariya nayi nace Auta wai a kannen nawa baka zabi wata bane ciki? yace ai kunyi sake an riga ku Sahar nake so ni,na rigada na fada Mata Kuma ni bana yaudara,idan Kuma ba a bani ita ba na sake ganin kanwar Sagir Zarah sai na dawo,shike nan Yaya Nawwar Yana aurenki nima sai na sake dawowa gidanku dama Cele tana nan ita Zan so,shi Auta baya kula Yara dai dai shi sai ya samu katuwa yace ita yake so,nace Cele din ai Kuwa da Watarana kaci duka,yace haba sai dai idan ba so amma ko kallon banza ta Isa ta min taji aiki, Wanda ta Raina zata yiwa,Kinga da munyi anko da Yaya Nawwar tunda baku da banbanci da ita irinku daya sak har ba a gane ku shike nan an daina min gani gani nima.

Auta ne ya kalli Raheemah yace ke Yar tsugula kiwa Allah ki daina sa fitted gown din nan wallahi bata yiwa sirara kyau Kara kankace mace takeyi mace ta fito kamar sanda Sam sirara basa kyau a ciki amma mutanenmu sunki ganewa da Kinga wata ta saka tayi kyau kema sai kice Zaki saka ayi ta yayin Abu mutum bazai duba abinda zai Masa kyau ba Kawai daga ganin wata tayi kyau sai kace kaima sai ka Zama irinta,Nace wlh kuwa Auta wata ma fara zata gani Allah yayita haka sai tace sai ta koma wannan farar dole,gasar masifa musamman kwaikwayon Yan fina finai, da jaruma tayi Abu sai a fara yi kowa ,fitted gown dinma yawanci duwawun ciko ake sawa ayi cikon karya wacce bata yi ba sai a ganta Kamar muciya da zani mu dinga yin abinda Muka San zai Mana kyau dai dai da jikinmu,Raheema tace to ni Ina so ba wanda zai hanani ai Umma tasan na sa katon mayafi,Auta yace mayafin da kina Fitowa Kika dangale abinki,dariya Raheema tayi ta gyara tana cewa amma ka cika Dan sa Ido yanzu kaga Sanda na dage ashe, Nawaf yace Ina kallonki Mana ke sai anga kin hadu dole,Gidan Aunty Bilkisu Muka fara zuwa,Mijinta Kamar zai goyani ka rantse nice kanwar tasa ko su Bilkisu basuyi murnar da yayi ba har mamaki ya bani ya siyo Mana lemo da ruwa

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button