Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 12

Sponsored links

Bata nuna mata komai ba tasata tayi wanka tayi sallah, ta kuma bata abinci sannan ta kaita wani spare room tace ta kwanta, part din Alhaji ta koma suka raya daren cikin aminci, alhaji sai nan nan yake da ita……..

Tinda momma ta tafi ta barta ta kasa bacci, babu abinda takeso illa taga tasha kwalbar codeine dan shi kadai ne ze iya sata bacci a halin da take, da abin duniya ya isheta sai ta tashi da niyar fita ko Allah zesa ta samu me bata codeine kamar yanda wanchan ya bata sigari dazu, saidai kash tana zuwa taga kofar parlourn a garkame, ashe momma ta kulleta ta waje kamar tasan zata fita……

Komawa dakin tayi tanajin yanayinta na dan chanjawa, chan kuma saita fara birkicewa saboda tanaso tayi baccin amma ta kasa, kuka ta hauyi me karfi amma ba wanda ya jiyota ballatana akawo mata dauki, haka ta cigaba da kukanta har akayi kiran sallar asuba lokacin idonta yayi ja kamar gaurashi, tayi kukan tayi kukan harta gaji, da kyar ta daure tayi sallar asuba dan lokacin zazzabi harya fara kamata……

Karfe bakwai momma tashigo part din, sosai hankalinta ya tashi a halin data ganta dan alhaji yace da wuri zasu fita, idan yaga yarinyar a haka ai sai ya dauka wani abun aka mata bayan jiya har kyauta ya mata……

Tambayarta ta hauyi meya sameta saidai kememe taki cewa komai har ran momma ya fara baci, daurewa tayi ta sata tayi wanka ta gyara mata fuska dukdan kar daddy ya gane komai sannan ta mata breakfast ta bata taci tanata lallabata, a haka alhaji yazo ya samesu ya kuma ji dadin yanda momma keta nan nan da ita, sai hankalinsa ya kwanta ya bawa momma yarda dari bisa dari……

Kamar yanda ya fada haka suka sata a school da islamiyya, suka kuma kaita shopping yace ta dauki duk abinda take so, kasa dauka tayi sai momma ce ta saki jiki ta dinga jidar mata abubuwa kamar gaske….

 

Hatta drivern da ze dinga kaita school saidai daddy ya daukar mata daban dan be hadata school daya da ya’yansa da suke boarding ba saboda yasan halin mama yanzu zata tada fitina akan hakan, sai ya bawa drivern kudi yace yana bata kullum idan ya kaita school, be bawa momma ba saboda hali irin na zuciya kartasa mata sake saken yana yiwa yarinyar hidima da yawa…..

 

A washe gari kuma urgent tafiya ta taso masa, dole yabar kasar ba shiri bayan ya tabbatar ya mata providing komai…….

 

A kuma lokacin fatima zainab tagane shayi ruwa ne a gurin momma, da farko kitchen ta maida mata gurin kwanciyarta, haka zatace taje ta kwanta ba shinfida ba komai tsabar mugunta, na biyu abinci sai taga dama take bata abinci a rana so daya, wataran in bataci saa bama bata bata, sannan zagi da cin mutunci ya biyo baya, bata sata koda dauke tsinke ne wai karta koya mata abubuwa ta moru a gidan mijin, gwara duk wanda ya kwasa ya sakota dan babu wanda ze yarda ya zauna da wacce ko shara bata iya ba……

 

A lokacin fatima zainab ta kara kulla aminta da codeine shiyasa duk abinda momma take baya damunta, kudin da daddy yasa ake bata kullum akan siyan codeine yake karewa kamar wacce aka yiwa baki, data siya abinci taci ta gwammace ta siya codeine tayita sha, tana sane da cewa smokers and drinkers are liable to die young amma she doesn’t care anymore dan tayi nisan da bata jin kira, abun nata har ya wuce addiction ya zama disorder…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button