Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 98-99

Sponsored links

Yamma nayi Mami tazo Muna tsaka da labari sai ga Baffa Kamar an jefo shi,Muna amsa sallamarsa ya wuce gaban Mami suna wani kallon juna Kamar zasu lashe juna,tashi Muka yi ni da Nawwar Muka haura sama Baffa zube gwiwoyinsa yayi a kasa Yana dan Allah Salamatu ki yafe min dan Allah ki dubi girman Allah ki yafe min sai hawaye sharrrrrrr Kamar yaro,Mami ma tana kallonsa ta fashe da kuka tana ta shesheka sun dade a haka kowanne Yana kuka a cikinsu,nayi kuskuren da bazan yafewa kaina baaaaaa ya sake sakin kuka irin na manya Yana durkushe a gabanta ya rike kafafunta ki yafe min dan Allah,Mami tana goge hawaye tace ba komai na yafe maka ya wuce na yafe,Baffa ya manta Idonsa ya rufe ya rungume ta,Mami tace zaka shiga fushin ubangiji ni ba muharramarka bace yanzu,Baffa ya saketa yace yace na cuci kaina na yiwa kaina na biyewa son zuciya,yanzu da me Ummin Haidar ta fiki ni me ya rufe min ido ne,Mami tace Kai ka sani kuma,akan na zauna da Ummun Haidar gwara na dawwama a gwauro duk azumi azo a kada min ganga harda karasawa da tausayi,duk zuga ce tayi tasiri a kaina ,Iyamami,Yusuf,Ummin Haidar sune ke zugani gashi yanzu sun jawo min sun barni a ruwa,Mami tace oho maka kuma, Yana ta kame kame dai Mami sabo da takaici ta mike tayi tafiyarta ta bar gidan,tana komawa gida sai kuka take Kamar ba gobe,washe gari Nawwar ya kaita Airport ta shiga jirgi tana ta uban kuka tana tuna tsohon mijinta.

Baffa kuwa Yana komawa gida cikin fushi ya saki Ummin Haidar saki daya yace gwara na zauna a tuzuruna munafuka algunguma kina kallo na dauki hanyar jahannama ashe Kara danna ni ciki kike bakar algunguma kwashe kayanki ki tafi Kuma ki barmin yarana,Ummin Haidar za a bar gidan daula sai kuka taje wajen Iyamami ta fada mata,Iyamami tasa aka Nemo Baffa tayi tayi ya maida Ummin Haidar yace wlh Kuna takura min Zan karasa sauran igiyoyin gaba daya itama gwara ku kyale ni,Iyamami tace au au to Kinga jeki gida idan ya huce zai dawo dake da Kansa,Baffa ya kalli Ummin Haidar yace ke Kar a doraki a keken bera ki sani bazan dawo dake ba tunda ke ba matar arziki bace Kawai ke kanki Kika sani,kina kallo Ina kwana a dakinki na Hana Mami kwananta Kika kasa tunatar dani akwai Allah,kina kallo Ina cin mutuncin wata Kika kasa fada min gaskiya sai dai ki zugani to baza ki jani jahannama ba wallahi sai dai ki tafi ke kadai bar min gida ya daka Mata tsawa,Yaje ya kwashe yaransa biyu ya kaiwa Nasira da Sultana yace gashi nan ku kular min dasu.

Daga ranar Suka dawo Jin dadin babansu kullum sai yazo cikinsu ko ya kirasu part dinsa suyi ta hira tare,akwai maza masu daukan zugar matansu ko iyayensu ko da kuwa ba akan gaskiya ake Dora su ba,irinsu idan mace ta gari Suka samu to za a ji dadinsu zasu amfani alumma sabo da matar zata basu shawara su dauka,Mata a guji dora mazaje akan hanyar da ba dai dai ba,wani zaiwa Yan Uwansa kyauta kibi ki kankane sai naki Yan uwan,zaiyi wani aikin Allah na lada ki hana,Kuma da yawa maza suna daukan Maganar matansu.

Yau Sunday a jirki Muka tafi Jagawa state ni,Nawwar,wise,Star,Yar Zabil,Mandula harda Santana zamu je gidan su Wise ayi sulhu ita ce ta Mana Iso har gidansu Muna zuwa Muka hango wani Dattijo me Kama da Wise a kofar gidansa a zaune kujera da farin glass dinsa da wani katon littafi na tattalin arzikin duniya da gani kaga tsohon dan boko wasu suna tabarma da sauran dattijai irinsa ana hira,Wise a mota har zufa take sabo da tsoro tasan babansu,Muna Fitowa a motocin guda biyu taxi Wise ce ta Fara fitowa harda sa hijab mu Kuwa duk mun Sha gayu,farin glass dinsa ya cire a hankali yace Hauwa’u kece abin mamaki sai ya tashi ya rungumeta irin dan boko nan wayayye, Yana murna yace ki yafe min Hauwa nayi kuskure dana takura Miki sai kinyi karatu bayan ke aure kike bukata karshe na kore ki banyi tunanin Ina Zaki je ba,ki yafe min Hauwa daga kanki ban sake takurawa kowa sai yayi karatu ba a gidana,Wise tana kuka tace ya wuce Daddy nima ka yafe min nayi kuskure,Dattijan suna ta taya shi murna Muka shiga ciki gaba dayan mu,kannena Suka fito da uban gudu suna murna,Maman mu duk ta rame sabo da bakin cikin Ina na shiga mijinta ya korar Mata ‘yarta, itama muka fashe da kuka ta rungumeni Muna ta murna,gaba daya muka zauna har su Nawwar, bayan an kawo Mana kayan motsa baki sannan Mama ta Dora Mana girki gidanmu me kyau Kato da gani kasan akwai rufin asiri,labarin komai na zauna na bawa Daddy da Mama suka dinga ta kuka suna Kuma godewa Allah da yasa na shiryu,Daddy yace ai bayan tafiyarki kadan nayi ritaya Hauwa duk wannan kudin Nawa yanzu babu sai rufin asiri gidan ne kawai,da Nawwar Suka dinga hira Yana magana Daddy Yana jefo turanci shi ga dan boko daga nan ya Fara bawa Nawwar labarin yanda tattalin arzikin Russia ya karu,yace kasan Bellarus da Azarbajan tare da Ukraine Russia ai ita ke juya wasu manyan state nasu masu karfin tattalin arzikin,wannan yakin da akeyi ai ita Ukraine itace bata da Gaskiya,baka karanta Littafin yarjejiniya tsakanin Russia da Ukraine ba kafin ta amince Mata ta shiga yankin Europe,kasan ai da duk a Soviet Union suke under Russia,Nawwar dai yana haka ne,uhmm,ae haka ne kam ,nace Wise ma ta samu miji ma zasu kawo kudi kwana nan,Daddy yace mashaallah,sai Yamma su Nawwar Suka ce zasu tafi,Wise tace nima binku zanyi ni bazan iya rayuwar nan ba yanzu kwata kwata idan an tashi biki zamu taho nan,Mama tace ai Kuwa baki Isa ba ki zauna Mana muma muji duminki,da kyar Wise ta yarda tana Fushi Muka taho Muka barta a can harda kuka,nace ke da an kusa biki zaki dawo Mana mayi waya tace to video call zamu na yi Muna dariya Muka tafi.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button