Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 8-9

Sponsored links

,abinda ma basu sani ba Nawwar ya mallaki gidaje da abubuwa da dama a nan Nigeria Maminsa da Baffansa sun sani su, sai Murna su Papa sukeyi lokacin Sabreen taki dawowa rabonta da Nawwar tun suna Yara,bayan Nawwar ya cika wata Daya da dawowa ya Fara zuwa Office Yana ta kasuwanci gidansa da ake kera Masa Wanda zai zauna da matarsa idan yayi aure wannan na musamman ne,Papa hankalinsa ya tashi ganin Nawwar ya Zama me kudi shi Kuma Wanda ya handame sun kare ga Baffa dan Uwansa arziki sai abinda yayi gaba duk da kuwa irin zaluntarsa da yake yi yana siyar Masa da kadara ba tare da ya sani ba,sai ya dage da son lallai Sabreen ko tana so ko bata sai ta auri Nawwar ta nan zai samu ya mallake dukiyar Nawwar, Haka ya Kira Sabreen Yana masifa yace wlh idan baki dawo gida Nigeria ba ban yafe Miki ba, Mama zaune take kusa da Papa tace ka dinga binta a hankali ita kadai ce garemu,Papa Yana fada yace to kina ganin ni naki yin arziki gaba daya kamar bakin uwa duk gani a tsiyace kina gani dan uwana Sunusi uwar mu daya u abanmu daya yazo yayi kudi ni kuwa na roka na roka Shuru,akan haka fa ganin lokacin Sunusi har ya kusa fin Sulaiman kudi hakan yasa na tura aka kashe Sunusu ya bar duniya,da Sauri Mama ta rufe masa baki tana furta ka rufa mana asiri Kar wani yaji tunda ba Wanda ya sani to muyi shuru, yace to nayi shuru,Sabreen masifar papa yasa ba shiri ta tattara ta dawo,Papa da Kansa ya dakkota a airport,tana shigowa part din Mami a Palo ta iske Nawwar Yana dining Yana cin abinci Mami tana ta zuba Masa surutu,dake Allah yayi ba me son magana bane Kuma shi bai fiye fara’a ba ga kafirin Isa da mallaka da son girma sai ya Mata shuru sai jefi jefi yake furta uhm hakane, har Sabreen ta kwala sallama ta shigo ta Sha tsadaddijar gown golden ga takalmi da Haka tayi kyau matuka,Mami ko murna bata yi da dawowarta ba ,Nawwar ko kallonta baiyi ba yaci gaba da uzurinsa itama bata kulashi ba sai da Mami tace ga yayanki Nawwar ku gaisa,sai lokacin tace Ina yini ta Kara gaba bai ko amsawa.

 

 

 

Itama sai bayan ta cika sati biyu da dawowa sannan Papa ya kirata ya sanar Mata cewar ya hadata aure da Nawwar ita Kuma Saurayinta Dan Italy take so Lorenzo,Zata Yi Musu papa ya dakatar da ita yace wlh idan baki yarda da auren nan ba sai na tsine Miki muna so muci arziki kina hauka kudi ne fa da shi kina gani arzikina ya Kare shi yake mana komai yanzu ci Sha sutura idan Kika aure shi ai dukiyar ma zai mallaka Mana wata Kuma mun samu damar Shiga jikinsa tunda shi Sulaiman busy ya Masa yawa, Mama tace ana Neman arziki kina hauka idan kika aure shi ai kinyi dace, Sabreen ba yanda ta iya haka ta amince Kawai,sannan Baffa ya samu Nawwar har dakinsa ya zauna yace Nawwar magana nake so muyi Jin haka Nawwar ya gyara zama sabo da shi mutum ne me biyayya, sune Suka kula da shi Suka dauki nauyinsa har ya zama abinda ya zama yanzu,Baffa yace dan Allah na rokeka Nawwar ka auri ‘yata Sabreen sabo da Kaine kadai na yarda zaka riketa da Amana ko bayan ba raina dan Allah karka ce a’a ka amsa min,Murmushi Nawwar yayi yace ni ai bance bana son Sabreen ba na amince Baffa bani da abinda zan biya ku iyayena,sannan na gama gina gidana na gama komai sanda kuka shirya ayi bikin,Yusuf Papa yana gefe a zaune shima ya dinga murna yace an gama dan albarka Allah ya baku zaman lafiya Kamar gaske bayan a ransa yana ta saka tsiyar da zai hadawa Nawwar ya gaje wannan kudin nasa da ya tara.

Baffa tunda ya auri Amaryarsa Ummin Haidar gaba daya ya tsani uwar gidansa Mami haka su Iyamami ma Suka tsani Mami basa sonta kullum sai zagi da cin mutunci,duk abinda danta yayi to ita zasu Zo su zage tasss bata da iko tayi magana Baffa sai ya sake ta gaba daya igiyar auren Saura daya jal,bai bata kwananta sai dai ranar girkinta tayi girki ta Kai Masa part dinsa amma Kuma Ummin Haidar ce zata kwana da miji,tun Mami na zuwa Yana wulakantata ya koreta har yace ta daina zuwa Masa da dare,a gidan daga ita sai yaranta su Nawwar da su take rayuwa,Abu na gaba gaba ma abinci ya daina zuba Mata a part dinta ganin haka Nawwar ya koma siyen komai a gidan na abinci Watarana ma har bangaren Iyamami da Papa, basa kaunar Mami ko kadan a gidan,Ko bata je wajen Baffa ba idan yaga dama har bangarenta zai Zo ya zazzageta ya fita,tayi kuka har ta Saba ma da rayuwar.

Bikin su Nawwar wata daya kacal aka saka sabo da gaggawa nan da nan biki yazo ba wani shagali Kawai aure za a daura a Kai Amarya cewar Sabreen tunda ba auren soyayya bane ana gobe daurin aure Yan Uwa da abokan arzuka sun ciga gida, ga kawayen Amarya sai Nawwar Wanda bai kaunar auren Sabreen baya sonta Sam haka suka raba Iv,Hajiya Binta da Rukayya kannen su Papa sun iso da yaransu samari wasu Kamar Nawwar wasu Kuma kasa da haka,akwai ma Mus’ab babban dan Binta ya girmi Nawwar,Washe gari aka daura auren Sabreen Yusuf Raj da Nawwar Sulaiman Raj Kan sadaki dubu dari, kudi dama ya basu da kansu Suka je kazar waje suka hada lefe, bayan Sallar Isha Papa da Mama suka Kira Ango da Amarya,Baffa,Mami,Ummin Haidar suna gefe Papa ya fara Nasiha me shiga jiki kamar gaske har zuciya sannan Suka ce su tashi su tafi shine Suka tafi gidan aurensu yayin da Ango ya dandana Amarya yaji ba kanta.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button