Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 20

Sponsored links

Wata mota ce me tsada ta tsaya Suka tafi da gudu tare da yanyameta sai Kuwa Suka ga mace Yar gayu babbar mace ta fito ta duba cikin Yan daudun ta zabi Wanda ake Kira da Santana ya balle Mata botin rigarsa Yana karairaya taga ya Mata ta jashi Suka Shige mota,ihu na saki Ina Dariya nace wayyo ana tallan duwawu,ba shegen da zai bi ta local government dina my GRA wlh lala babu me shiga GRA na,juyawa nayi Ina tafiya dagwas dagwas na koma gida abina Ina Allah wadai da wannan sana’a Wanda Hausawa musulmai Suka Fara tsunduma kansu cikin irinta su hada jaka su tafi street Ashawo.

Washe gari ma haka na cakare cikin kayan Seraline Muka je Nasha kallo tun abin baya birgeni har naga suna ta tara kudi ni ana ta barni a baya sai tura kudi sukeyi gida ana siya musu gida da filaye da kudin ashawo duk sun tara kudi a tunanina fa,ni kuwa kowa sai kallon banza suke min,sannan ba mutunci kwandala babu me baka kyauta,bayan satikai haka kawai Katsam ba abinda nake so nima sai Karuwanci yau dai na sa a raina zan fara Karuwancin nan nima na samu kudi amma me tsada zan yi sai idan namijin yayi min sannan sai idan da kudi da yawa,Shigowa nayi dakinmu da dare na samu Seraline tana shirin fita nace Kawata na sa Raina yanzu Kam Zan Fara Ashawo work dinan ki ci gaba da bani aron kayanki kafin na samu customers na siyi nawa,Saratu taji dadi tace ko kefa maza shirya baki da matsalar kayan sawa Kinga yanzu 10pm Kar mu makara,da sauri na Fara shiri na dau wanka cikin dogon wando tight da Yar riga karama nayi kyau matuka Muka tafi,gefen titin Muka tsaya tunda naje motoci ke tsayawa daukana amma kowa yazo sai nace Million daya daga nan me motar zai dauki wata ya barni nan tunda wasu gasu nan 2k 5k ma daukansu akeyi idan customers basu zo da yawa ba,Haka yau ma na koma gida ba kowa,washe gari aka sake fitowa dani nan ma nace sai Million daya kowa sai ya min kallon banda hankali, wani bahaushe ne yazo a Yar karamar motarsa ya tsaya tare da Fitowa Yana Kare mana kallo ya kalli mandula yace juya na gani ta juya sosai ya barta nan ya karaso wajena baki na tabe,yace juya na gani na juya a gabansa ya jinjina Kai yace kinyi muje ko nace kaje da wa? You dey craze? Kasan kudina Kuwa? Nawa to ya furta Yana kallona nace million daya zuwa sama,Ido ya zaro yace ke Kuwa sai kace matan gidan Aljanna zunubi ne fa ga tarin zunubi sannan ga tsada haka,kaga ja kayi gaba ko yanzu na tarwatsa maka kwakwalwa wlh bani da mutunci da kake gani na ja tsaki, wuyana ya shafo kafin ya zare hannunsa na kwashe shi da Marin da yasa ya gigice sauran karuwan Suka goya min baya gamu da hadin Kai kafin kace me mun kashe titi da fada da kyar ya kwaci Kansa ya bar wajen a guje cikin motarsa muna binsa da zagi nace shege ko maza sun Kare me zanyi da Kai na ja tsaki Ina gyara gashina sannan Ina tauna chewgum kas kas kas…

 

Nawwar magungunan Iyamami ya raina su ganin yayi masu tsadar gaske ma amma me sai yaji idan yaci ya koshi ba abinda yake bukata sai mace,sai da Sabreen tayi 3days sannan aka dawo da ita gidansa bata canja zani ba sai ma rashin mutunci data karo,Yan aikin ta fara ci musu mutunci dama hakuri suke yi da ita idan Coccaine dinta ta motsa haka take daddana musu ashar bata da respect,Daya Yar aikin ta hada kayanta ta gudu Sabo da zagi da cin mutunci sannan bata basu abincin kirki a dafa ayi komai amma ta hana su,Ladidi me girki ce ta rage sai maza masu aiki su dama yawanci kudi yake basu suci abinda suke su sunfi son ma a Basu kudin har canji suke samu kullum,Ladadi ce ta fito Kawar Sabreen tazo Jamcy ta kawo Mata lemo,Sabreen tace ke tsohuwa wannan Kawai zaki kawo shine kadai a gidan? Ladidi tace Zan kawo ai Hajiya ban gama abinci bane,Wai ke wacce irin dabba ce ne,Ladidi da mamaki ta kalli Sabreen domin tayi kusan jika da ita ma,tace dani kike Hajiya? No da uwarki nake dalla wuce ki kawo Mana snacks,Ladidi tace ko ba komai Sabreen ai naci darajar furfurata sannan ni nasan nayi jika dake amma ki iya kallona ki zageni, Sabreen daga Jin haka sai haukar kwaya ta motsa ta zabgawa Ladidi Mari,kumatu Ladidi ta dafe hawaye ya shiga sintiri a kumatunta juyawa Kawai tayi ta shiga bangarensu ta hado kayanta tana hawaye ta fito zata tafi,Jamcy tace wannan shine dai dai banzayen Yan aikin nan sai su dinga hada kansu da me gida, Sabreen ko a jikinta tace kina jina dan iskan mijin nan nawa Watarana Yana birgeni da baya shiga safgata inyi shaye shaye na lafiya lau dariya Suka Yi tare da tafawa dukkan sirrin Sabreen ba abinda Jamcy bata sani ba ko hannu Nawwar ya rike Mata to sai Jamcy taji labarin ita kuma Jamcy wayo gareta bata fadawa Sabreen sirrinta sai dai dai, Motar Nawwar ce ta kunno Kai cikin gidan cikin jerin motocinsa yayi parking sannan ya fito ya samu Ladidi da kayanta tana kuka zata tafi,da sauri ya fito ya tareta Yana Tambayarta lafiya tace matarkar ce ta zazzageni sannan ta mareni,Nawwar zuciyarsa ta harzuko tsohuwa haka, muje Baba Ladidi tabi bayansa tana cewa ni gida zan koma na zauna gaban yarana har abada na daina aiki a gidan masu kudi Ina da gata na,suna shiga palon a tsawace yace ke har kina da damar Marin Baba Ladidi ubanki ta miki ya karasa Gaban Sabreen tace dan Iskanci na….Saukar Mari taji ba daya ba ta ko Ina,Ladidi tace na gode Alhaji ka rama min, Wayar tv ya fisgo ya tsulawa Jamcy itama ya haukace musu,Jamcy ta mike ta fice da gudu ta bar gidan Sabreen ma taga zai Mata illa ta buya a kitchen ta saka key, Kudade masu yawa ya bawa Ladidi tana ta godiya ranta fes an rama Mata ta tafi gida.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button