Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 49

Sponsored links

Sai yamma aka sallamesu daga asibitin, sallama sukayi da Abby suka tafi da niyar gobe Abby ze jagorancesu a daura auren tinda ta samu lafiya sosai, sai a lokacin kuma ta kashe wayar…….

 

An fito daga sallar isha’i Deen ya karaso ‘American Hospital Dubai’, sake duba tracker dinsa yayi yaga an kashe wayar dazu, hakan ya basa tabbacin dole suna asibitin inma basa nan toh suna kusa, reception din asibitin ya nufa da niyar ya nemi appointment da me asibitin a matsayinsa na likita yanda zeyi saurin gano patients din dake asibitin…….

Kamar a mafarki yaji an dafa kafadarsa, juyowa yayi da sauri duk a tinaninsa wata yar rainin hankalin ce yaci ubanta itama, sai kawai yaga mutumin da be taba tinani ze kara gani ga a rayuwarsa…….

Abby ya fada yanajin kamar yayi tsuntsuwa yagansa a Nigeria gobe……

Abby na komawa ciki su khaleel suka fadomasa, rudani ya shiga akan yanda zeyi da lamarinsu, tabbas yanaso yaga sunyi aure kamar yanda suke so amma ba irin wannan auren ba, ya fiso suyi aure na gaske da amincewar iyayensu….. Wani dabara ne yazo masa yayi dialing number khaleel……

Suna zaune yana matsa mata kafafunta yana mata tausa sunayi suna zubawa juna kalaman soyayya yaga kiran ‘waliyyi’ kamar yanda yayi wa Abby saving, ba bata lokaci ya dauka ya fara gaisheshi cike da ladabi…….

Saida suka gama gaisawa sannan Abby ya masa bayanin yar tafiyar data taso masa urgently zeje Nigeria, sosai hankalin khaleel ya tashi da jin wannan maganar saidai be gama jimami ba Abby ya fara masa wani bayanin daya faranta masa at the same time yasa masa shakku, cewa yayi indai ya daukesa a mahaifi kamar yanda ya fada yanaso su bishi Nigeria ya daura musu aure a goben kamar yanda yayi musu alkawari, shiru khaleel yayi dan ya rasa me zece, haka abby ya cigaba da basa baki da kara kwantar masa da hankali akan in suka bishi ba abinda ze hana a daura musu aure, in fact in zaman dubai din sukeso zesa a dawo dasu ana daura auren, nan ko so yake ya tafi dasu Nigeria yaje ya bawa mahaifin khaleel hakuri akan ya aura masa ita, yasan kuma Insha Allahu in yaje da kansa zasu amince, irin gamsassun bayanin dayayi ne yasa khaleel kallon fatima zainab dake sauraren komai itama kasancewar wayar a speaker take ya mata signal da ido akan me tagani, daga masa kai tayi dukda ba wani san Abby take ba amma maganganunsa sun gamsar da ita……..

Sai kawai khaleel ya fadamasa sun amince, sosai Abby ya nuna musu jindadinsa yayita shi musu albarka sannan yace ze aiko a daukesu gobe da safe kawai su zama cikin shiri……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button