Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 77

Sponsored links

Yanda ya barsu haka ya tarar dasu suna dan hirarsu sama sama idon Umm kur akan fatima zainab…..

“Ba nisa nayi ba, wani ne yayi mistaking gidannan da wani gida shine naje na nuna masa gidan dayake nema”….

Deen ya fada ganin mami na bashi wani questioning look….

“Kaga na tambayeka ne? You can get your mouth shut!”……

Shiru yayi be kara cewa komai ba sai ma juyawa dayayi yana taya Umm kallon fatima zainab dake bacci hankalin kwance…. Ya dade bega wanda yakejin lamarinsa sosai kamarta ba, ya rasa what’s so special about her that he’s feeling that way?, yanzu babban damuwarsa yanda ze taimaka mata as a Doctor ta samu lafiya sannan ya maida ita gurin iyayenta……

Suna cikin wannan hali sukaji ta kwalla wani irin ihu sannan ta tashi a birgice…….

Rige rigen zuwan gurinta sukayi ko tsoron karta musu wani abu basaji….

Umm datafi kusa da itane ta rungumeta tanajin kamar ta mata kuka, it’s so sad ace as young as she is tana battling da mental illness dan harga Allah sun yarda tanada problem a kwakwalwarta kamar yanda Deen ya fada…..

Kamar magic ta nutsu tana jinta a jikin Umm sai kuma ta fashe da wani mugun kuka me taba zuciya, shafa bayanta Umm ta hauyi tana fadin;

“Shhhhhh! Relax baby girl, stop crying okay?”…

Ta kuwa nitsu sosai dan har cikin zuciyarta takejin wani sanyi tinda matar ta rungumeta dukda batasan wacece ba, amma hakan besa tadaina kukan ba……

Mami na tsaye tana binta da kallon tausayi dan itama imagining kawai take as young as she’s tana fama da matsalar brain?….

Hankalin Umm ne ya kara tashi ganin sai rarrashinta take taki dena kukan, dagota tayi tana kallon cute face dinta ta shiga goge mata hawayen tana fadin;

“Waya fadamiki pretty ladies na kuka? Yanzu fadamin waya saki kuka in rama miki, kodai Saif ne?”……

Tsaida kukan tayi ta kalli gefe daidai inda Deen yake, batasan sunansa ba amma haka kawai taji alamun shi ake nufi”…..

Suna hada ido tayi yunkurin mikewa tana fadin;

“Yes shine, wallahi saina kasheka”……

Ta fada cikin muryarta me mugun sanyi da dadi….

Mami data fara suspecting ko dai akwai abina Deen ya mata ta riketa tana fadin;

“Meya miki dear fadamin, I promise you zan tayaki hukuntashi!”…

“Kasheshi zanyi yanzu, I will kill you”….

Fatima zainab ta fada tana kokarin kwace kanta….

Shiko Deen tuni ya dade da tafiya wata duniyar akan muryarta, shi baya ma jin maganar zata kashesa da takeyi, all he hear is her melodious voice that is ringing in his brain, kana kallonshi kaga wanda is so lost in thought, sam besan wainar da ake toyawa ba…

Nufota ya shigayi cikin rashin sanin abinda yake fada yace;

“Dan Allah recite Quran again for me kamar wanchan ranar, you have no idea how it has been giving me sleepless night, it’s worth listening”….

Mami ce ta daka masa tsawa me rai da lafiya ganin kamar shima ya fara samun mental problem din yazo yana musu sambatun da basu gane ba bayan suna fama da yarinya tana dagewa akan saita kasheshi shikuma dake wawa ne yana nufota, tace;

“Get out!!!”….

“She’s not okay, I need to treat her”…..

Ya kuma fada absentmindedly….

“My friend get out of this room now!!!”…..

Fita yayi da sauri jin tsawar har kansa, sai kuma ya jingina a jikin kofar yana sauraran maganganunsu….

“Ya isa dearie, kinga yariga ya fita, I promise you bazai dawo ba badai shine bakisan gani ba?”….

Cewar mami tana zaunar da fatima zainab kusada Umm, sai suka sata a tsakiya….

Daga kai tayi tace;

“Idan na kuma ganinshi saina kasheshi, why will he kidnap me, yasan wacece ni kuwa, wallahi I’ll deal with him!”….

Kallon juna Umm da mami sukayi suna jinjina alamarin, mami ta daure tace;

“Be kyauta ba gaskiya, amma ba gashi munzo ba, ki kwantar da hankalinki”….

Shiru tayi batace komai ba amma haka kawai takejin zuciyarta ta aminta dasu….

“What’s your name?”…..

Cewar Umm tana shafa bayanta…..

“Fatima zainab! You?”…

Haka kawai ta samu kanta da jin dadin conversation dasu itada maganar arziki bata hadata da mutane….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button