Hausa Novels and Stories

X World 4

Sponsored links

*The Novel is only for matured , idan kin san You’re under 🔞 don Allah kar ki karanta .*

 

**

 

Wani irin farin ciki ne mara Misaltuwa ya mamaye Zuciyar Asmeey Saurin juyawa tayi tana neman Su Zee don ta basu kyaƙyƙyawar Labari don ita a jikin ta take ji Shureim ne wanda suke jin labarin su ɗaya daga cikin Star Gang na matasan Sojojin nan masu fama da Rashin ji da girgiwa . A hankali ta Dafa zee dake ta rawa kaman mazari babu Alamun Gajiya don a haka suke for more than 1hr . Bakin ta takai kusa da ita tana raɗa mata magana kaman Haka ” Zeee Dakata kiji nayi fa nitso yanzu haka na kamo Babban Kifi. Saurin kallon ta Zeee tayi tana maida Hankalin ta sosai kan Abin da take cewa”. Ke Asmeey ban gane ba. Wa kika samo mana .? One of the Star gang . Asmee tayi maganan tana Sakin murmushi . Eh Asmee A ina kenan .? Wa’annan da basu Ƙasar London basu Thailand basu America ta ina kika same su.? Ai wannan Wurin yayi masu Kaɗan koda Ma A shaharar ne . Star Gang fa Basu kusan Biyar bane. Eh nafi jin sunan mutane biyu dama daga Ciki Na Ɗaya Shine Muhammad Wanda ake kirar sa da Adnaan na biyu sai Shureim kaman haka ne . Zeee ne ta saki Ajiyar zuciya kamin tace ‘ kwarai fa su Nima nake jin sunan su sosai ,Adnaan Da Shureim . Wani irin Dariya Zeee ta saki Kamin tace ” Kice Zamu Fantama iya yanda muke so kudi ai kam yanzu sai dai mu koma Rabon shi . Chilling sai inda ya tsaya ,zamu koma fita kasashen Turai da Sauran su .

Kallon Anya kin san me kike yi Asmee ta Watsa ma Zainab kamin tace ” ke raba Ni , Ai nayi nadamar ma yanda ya Ganni Anan . Cike da Rashin Fahimta Zee tace me yasa .? Gyara Hannun Half vest din jikin ta tayi tare da cewa ” Ai yanzu ne nake jin na samu mijin Aure . Kin kuma san Gang din su ba sa’an mu bane . Amma sai na ga na mallake shi ko ta halin kaka nafa samu miji . Ai irin wa’annan baka bari suna kubce maka . Zee ce ta bude baki zatayi magana dai dai Seeyah na isowa . Me kuke tattaunawa Haka .?

Humm kedai Seeyah bari Abin nema ne ya samu . Cewan Zee tana Zaiyana mata labarin duk yanda suka yi da Asmeee . Kai Haba.! Wai da Gaske .? Allah kuwa nima kaina na ruɗe kaina ya dau chaji cewan Zeee tana saka hannun ta tare da kama Kan ta . Wani irin Dariya suka kece mata dashi kamin Seeyah ta kalle su duka tana cewa ” Back to Our business ya muke ciki .? Ta yaya zamu kama fatsan .? Zeee ne ta furta ” Ai mun kama ma ,mu abun da ya rage namu sanin yanda zamu gudanar da tafiyar har mu gan mu a inda muke So . Don kinganni nan inada Labarin rayuwar ɗaya bayan Ɗayan su. Mahaifiyar Adnaan kuwa Ita idan kika ganta baiwar Allah ce sosai . Ita bata Cikakken Wata shida a Nigeria tana Sa’udiyya don haka Hijab Zan koma sakawa Don na mallake shi , na kama Wannan . Kallon ta Su kayi suna saka Dariya tare da Cewa ” Shi da akayi masa Aure ,ko bakiji labari bane .? Wanda ya Aura Cikakkiyar Mayawaciya ce Ta gama shagalanta Sannan aka liƙa masa don Dole .

Shiru Zeee tayi kamin ta saki Murmushi mai manifofi tana cewa ” Dole a yanzu Gidan sa babu zaman lafiya . Don ko Dan iska yana son Auren kintsatstsiya . Don haka zan Amfani da Wannan daman don Ganin na shiga daga ciki Nima . In yaso sai a Cigaba da bandarwan Dani ba komai duk masifa indai zanci me kyau nasha me kyau . A tare suka sheƙe da Dariya kamin Aseeyah tace ” ya kamata mu fita daga Waje ne sai mu tattauna da kyau yanda abun zai tafi mana .

Suna Wannan maganan ne Asmee taji Hannun Wani yana lalubar ta sam bata san lokacin da tace ” Kai bawan Allah rabu Dani ,barni naje na nema ma kaina mafita ,na samu Wanda na dade ina Marari wanda banyi zaton zasu neme Ni Ko a karuwanci ba . Don haka rabu Dani zuwa nan ya kuma kare daga yau .! Ta ƙare maganan tana angaje yaron , Dariya suka fashe dashi su Zeee Suna juyawa tare da fara sauka Stairs din suna fadin Kin mana dai dai .

Cikin Wani irin yanayi Na rashin Jin Dadin dawowa Kasar Nigeriya Take kallon mijin nata Adnaan kamin Neesa ta Furta ” Yana ga Muna daukar Hanyar da ba gidan mu ba .? Nan fa Gidan Ammie zamu je kenan da Wannan tsalelen Daren .? Yanzu ba zamu sauka a gidan ka ba sai Gidan Ammie to me zamu yi a can Adnaan .? Duk magaanan da take masa banza yayi mata don dama tasan hali ba lallai ya tanka ta ba . Takaici Ni ya ishe ta Wannan yasa ta yin shiru zuciyar ta na mata ba Daɗi . Don ita ba haka taso ba sam .

Tafiya suke yi sosai ba ta ƙara masa magana ba haka shima bai da alamun tanka ta ko ya bata Amsa akan tambayoyin da take masa. Ear phone din sa ya gyara yana receiving call . No Shureim ka koma mun kusa Isa Gidan Ammie da Safe ma haɗu A Barack . Ba tare da ta ji mene Shureim din yace ba ta taji ya basa Amsa da Okay yana mai Cigaba da Driving ɗin sa a Hankali . Wani irin mahaukacin katafaren Gida ne suka isa . Inda Ko ina tun daga Farkon gidan har bayan shi Sojoji ne Masu Bama Gidan tsaro da kariya . Ko ba’a faɗa maka ba Gidan babban Soja ne wanda ya amsa Sunan shi . Cikin Arrogant Muryar sa irin na Sojojin nan marasa Kirki ba tare da ya Juyo ya kalle ta ba ya Kira sunan ta Da ” Neesa “.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button