Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 104
Yana cikin wannan hali Mom tashigo, kamar ko yaushe murmushi dauke akan fuskarta, karasowa tayi ta zauna a hannun kujerar da yake, cikin kwantar da murya tace;
“Alhajina ni kadai!”……
Shiru yayi kamar bejitaba dan so yake tabashi space yanda ze samu damar yanke abinda ya kamata yayi…
“Kasan yanda nakeji a raina idan na ganka a cikin damuwa kuwa? Dan Allah ka tausayamin ka fadamin damuwarka kona samu salama a zuciyata, da yarda Allah kuma in tayaka nemo mafita”……
Sosai ya danji kalamanta sun sanyaya masa zuciya, shiyasa take da wani guri me girma a zuciyarsa saboda gwana ce wajan kwantarwa da mutum hankali, ko yanaso ya boye mata damuwarsa saiya kasa shiyasa babu abinda bata sani ba akansa har wanda be kamata ya fadamata ba saiya samu kansa da fadamata………
“It’s about Deen!!”…….
Kara matsowa kusa dashi tayi cikin kwantar da murya kamar yanda ta saba tace;
“Allah ya huci xuciyarka yallabai, but what about my son?”…..
“Aure nakeso namasa very soon!”…..
“Nagane, toh amma meye abin damuwa tinda yasan da maganar dama?”……
“Mahaifiyarsa ce tashigo da wani abu!”……
Ya fada wani bari na zuciyarsa najin kamar be kamata yayi hirar da ita ba…….
Gabanta ne yayi wani mugun faduwa jin abinda yace wai mahaifiyarsa, yaushe suka hadu har sukayi magana har tashigo da wani abu? Ashe tana zaune gaho abubuwa nata faruwa bata sani ba?…. Cikin basarwa tace;
“In banda abinta ai gwara yayi auren zefi samun nitsuwa, ita da kanta hankalinta sai yafi kwanciya da yawace yawacen daya keyi, adai bi abun a sannu”…..
“Ba auren bane bataso, wai tana da wacce takeso ya aura”……
Nan ya kwashe duka yanda sukayi da Mami ya gayamata da yanda suka kare da shima Deen din har yace karya sake yazo masa gida gashin yanzu abun ya damesa…….
“Yallabai in banda abinka ai hannunka baya rubewa ka yar, be kamata kacewa son kar yazo ba kamata yayi ka bishi a hankali tinda yasan da maganar Hamida a kasa, kuma tinda tace saidai ya auri daya ai zabinka ya kamata ya aura tinda uba keda alhakin aurar da dansa, yanzu gashi ka kara bata damar da zata janyeshi sosai, tsap saita masa auren baka saniba ma!”……..
Dafe goshinsa yayi yana harhada maganganunta, tabbas abinda ta fada gsky ne, yin zuciyar da yayi kamar ya kara bata damane taci galaba akansa
“Just trust me alhajina, yanzu ka kirashi kace ya tawo”……..
Daukan wayarsa yayi ya shiga dialing number Deen, kira uku ya masa be dauka ba…..
Deen da suke cikin tashin hankalin neman fatima zainab wayarshi na jikinsa amma ko ringing bejiba……
Sosai ran dad ya baci yana ganin kamar Mami ce ta hanashi daukan wayarsa, wato tin baaje ko ina ba maganar sameera ta fito na janyeshi kenan?…. Dukda haka sai ya kasa hakura ya cigaba da kiransa,
Sai a kira na biyar sannan Deen yaji wayarsa na ringing, kamar ya share kawai ya fito da wayar, ganin Dad ne yasasa daukan wayar da sauri……
Tinda ya dauka yake zazzaga masa masifa akan rashin daukan wayarsa da wuri, yana sauraransa amma bece komai ba saboda abinda yake damunsa yafi karfin masifar da Dad yake, shiko jin abinda yake cewa bayayi dan hankalinsa baya wajan……