Hausa Novels and Stories

Sanadin Zane 1-2

Sponsored links

Monday aka ce tushen aiki

 

 

 

12:40pm

 

 

 

Fitowa yayi Yana tafiyar kasaita Wanda ke nuni da jinin dake gudana a jiyoyinsa na cikakkiyar sarki ne watoh shi jinin sarauta ne ta ko wace fuska …. agogo ya duba kafin ya shiga motarsa domin aid dinsa sun shirya jiran fitowarsa kawai ake daga meeting zashi lunch….kafin ma ya karaso an bude me motar tsakiya ya shiga sai aka kulle

 

 

 

A mugun gajiye yake hakan yasa ya jingina da kujera ya lumshe Ido Yana Jin kewar gida na lullub’eshi yau dai zaiyi kokarin ganin ya Gama abinda ya kawo su ya koma gida ya gaji da kasar Nan

 

 

 

*Bilkebab minna niger state*

 

 

 

Babban eatry ne da tayi suna a garin minna, wuri ne na manya mutane irin yan siyasa da kuma manyan gomnati sai kuma masoya da suka amsa sunansu masoya watoh ba ko wani saurayi zai iya Kai budurwarsa Nan

 

 

 

 

 

Convoy ne na motorci wanda kallo daya zaka musu kasan babba ne ke ciki domin harda na security

Tsaye take ta bawa gate din baya sai bincika jakarta take da alamun dai da abinda take nima tayi zurfi hankalinta yayi nisa

 

 

 

Horn ake kamar za a tada gari amma bata motsa ba bare su sa ran zata matsa tun suna yi a hankali har suka fara matseshi continuesly sai piiiiiiiiii piiiiiiii kake ji ba gaugautawa

 

 

 

 

 

Motarsa ne a tsakiya daman ya kishigid’a ne ya lumshe ido saboda gajiyar dake jikinsa sai ga wanan azabben horn din a firgice ya bude idanunsa yana mamaki dan duk wani wanda ke karkashinsa Kuma ko yasansa toh an San da da rashin son hayaniya baya ko kad’an baya san hayaniyar

Driver dake motar gaba kallon wanda ke gefensa yayi yace”wanan ai rainin hankaline Ya za ayi ta tsaya a hanya ana horn taki matsawa

 

 

 

Bude motar driver yayi da niyyar zai je ya turata dan a zuciye yake wallahi yasan tana jinsa ta sharesa

 

 

 

Daidai lokacin data sauke ajiyar zuciya ta d’au jakar materials dinta tayi cikin gidan abincin ko juyawa batayi ba dan bata ma san sunai ba wallahi

 

 

 

Har dan dagawa yayi daga zaune da yake yana kallon bayanta yana mamakin nata kalan iskanci dan wanan horn din ko kurma ce ita zata ji,a ranshi yace”Nigerians”

Gyara parking sukayi security suka fito suna kalle kalle supervising the environment kafin suka bada umurnin ya fito

 

Wow nace domin ya kai duk inda ake bukatar namiji ya kai ga jiki ga height wanda kallo daya zaka masa ka gano sarautar dake gudana a cikin jininsa dukda ba wata shiri yayi da zai nuna hakan ba but izza da dattakonsa ya nuna waye shi,

 

 

 

Ciki sukayi Yana tafiya kamar dai baya son Yi Kamar wani Mara lafiya

 

 

 

Ciki ya shiga aid dinsa na kokarin sa a Kori mutane Dake ciki ya d’aga musu hanun tunda yasan shi ba Dan kasa bane kuskurene a nimi nunawa mutane ikonsa ba tare da sun San shi din ko waye bane hakan sai jawo Masa rainin Amma dukda Haka Saida suka Samar me kebetancen wuri ya zauna shi kadai sanan ya d’au menu Yana dubawa

A inda ta zauna da friend dinta tana facing dinsa ne tunda ya shigo ta zuba me Ido tana kallonsa har Saida kawarta ta tab’ata tana tambayarta da hannu

 

 

 

Girgiza Mata Kai tayi alamun ba komai tana kallonsa isah daya kawo su na kallonta dan da k’yar ta yarda ta Zo Saida kawarta Amina ta roketa a waya kafin ta zo Allah ya gani yana son fannah har cikin ransa ko ya take Yana sonta da kaunarta but sai wulakanci take Masa

 

 

 

Idanunsu na had’uwa ta sakar me murmushi daya kusan narka me zuciya dan Saida ya dafe Yana lumshe idanunsa

 

 

 

D’auko jakar material dinta tayi ta fito da wani board Yana da dan girma but ba sosai ba

 

Ta fito da paint dinta

Mikewa tayi cike da haushi ta kwashi pain work din da tayi ta rubuta fannah art work in Italian hand writing sai phone number ta

 

 

 

Tana zuwa security Dake tsaye Dan nisa dashi suka hanata karasawa

 

 

 

Murmushi tayi sai ta ajiyewa security din board din ta juya tana komawa table dinsu Jakarta ta kwashe ta bar wurin

 

 

 

 

 

Har ta Kai exit sai Kuma ta koma gun security din ta

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button