Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 71

Sponsored links

Jin yayi shiru ta sake nisawa da ajiye kofin. “Bayan nan mi kake son sani?”. Kansa ya jinjina mata alamar babu. Ta ƙara faɗin, “Ni zan iya tambaya?”. Nan ma kan ya jinjina mata alamar eh.

“Kace baka san duk matan da aka aura maka ba sai ni, a ɗan gajeren labarin da naji kuma ance sai an kawosu sashen nan suke rasa ransu ai, bayan mutuwarsu ka taɓa ganin gawarsu?”.

“Miyasa kike son sanin wannan?”.

“Saboda kace zamuyi aiki tare”.

“Wannan baya cikin aikinmu”.

“Shine mafi muhimmanci ma acikin aikin da zamuyi tare, dan nafi alaƙa da shi fiye da wanda kake son alakantani da shi. Inaji a jikina mutuwar matanka bata da alaƙa da yunƙurin waɗan nan Uncle’s ɗin naka. Su nasu yaƙin da banne da wannan”.

 

Kallonta yake kamar idanunsa zasu zubo. Itako ta kauda kan gefe kamar ba daga bakinta lafuzzan suka fito ba.

“Mi kike son faɗa?”.

“Abinda ya dace ka faɗa kafin faɗata. Ni nasan kasan su wanene Uncle’s ɗin ka da burinsu a kanka. Masu kashe matanka kawai kake buƙatar sani in har da haske bakai bane ba”.

 

Tsabar yanda maganarta ta masa dirar mikiya a zuciya da brain bai ma san sanda ya juyo da ƙyau yana fuskantarta ba. Eh tabbas ya jima da sanin su wanene Miran Arshaan da Miran Jasim har da ma burinsu a kansa, tun kuma randa ta bashi guba yaji a ransa su ɗinne, hakama kisan matansa da su yake dangantawa, su kuma yake bibiya da son tabbatarwa. Amma magana mafi ɗaukar hankalinsa da ga gareta furucinta na ƙarshe. “Basu bane ba fa?”. Zancen zuciya ya fito fili batare da ya sani ba.

 

 

Jajayen idanunta ta zuba masa kai tsaye, sai kuma ta saki murmushi mai ciwo. “Sultan ban shigo masarautar RUMAN domin kallon gine-ginen ƙawa da adon zinari ba. Idanuna a buɗe suke fiye da yanda na mage basa barci a cikin dare. A tunaninka na baka gubar da suka bani ne dan ka mutu?”. Ta juya idanunta da suka fara bashi tsoro ma shikam tana sakin ƙayataccen murmushi. “Lala-lala, madarar dana baka sam bata da alaƙa da wadda suka kawo na baka, wadda kuma na baka ɗin tun usil dama bata kisa bace” tai wata ƴar dariya mai ƙayatarwa. “Kayi haƙuri, su fa wawayen karatunsu karanta musu yake amfani suke da ni, basu san Fhareedah bint Zayyan bace ke amfani da su. Bari dai na taƙaice maka karna jaka da nisa. Ni da kaina na kawo kaina nan domin tabbatar da waye masheƙin ƴan uwana. Bani aka kawo domin bama kariya ba….”

 

Gaba ɗaya Tajwar Eshaan yama kasa gane suma yayi ne? Ko kuwa ya zama butun butumi ne oho shi bai sani ba. Abinda kawai ya sani idanunsa nakan aljana zai kirata ko mima bai tantance ba.

 

Iffah da ke wata ƴar dariya ƙasa-ƙasa ta yunƙura zata sauka a gadon ganin kamar ya zama gunki ne ma oho. Cak ta dakata jin an riƙota, maidota yay ta koma inda ta tashin yana binta da wani irin shegen kallo data kasa bama fassara.

“Wacece ke!?”.

Kalmar data iya fitowa a bakinsa kenan a cikin dubunan da ke masa kaikawo. Da gaske idanunsa razanata suke, dan haka ta kaudar da natan tana cigaba da murmushinta. “Nikam maimaita wacece ni ko bitar karatu ne ya kamata an haddace. Amma kayi haƙuri, Fhareedah bint Zayyan ce, mai jiƙaƙƙen shirin tarwatsa masarautar ruman kamar yanda suka tarwatsa min ahalina. Wlhy da gaske nake bana yafiya, in har nace sai nayi to sai nayi ɗin koda zan ƙarasa da bugun numfashina na ƙarshe.”

“Kin san zan iya kasheki a cikin ɗakin nan na binne gawarki kamar ba’ayiki ba”.

“Shiiii!!”.

Ta faɗa a hankali da ɗaura yatsanta saman tausasan lips ɗinsa, cikin raɗa-raɗa da ƙyaƙykyafta idanunta cikin nasa dake neman tsaida numfashinsa ta furta, “Da hakan kake da tuni kayi, amma nasan kai ba mai kisa bane bin Haysam Abdul-majeed Qutb….” sai kuma ta saki murmushi tana lumshe idanunta da har yanzu basu washe da ga shaƙar da Malikat Bushirat ta mata ba, tare da yo ƙasa da yatsanta da ke kan lips ɗinsa a hankali tabi takan kakkauran wuyansa tayo ƙasa kan ƙirjinsa da tai matuƙar dannewa kafin ta taɓa ɗin, a saitin zuciyarsa ta tsaida ɗan yatsan da buɗe idanunta dake lumshe. “Wannan zuciyar zinariya ce mai hasken diamond dake bugawa da harbawar numfashin duk wani talakan ƙasata, ba ita kawai ba, kai a karan kanka ZINARE ne ESHAAN”. Ta ƙare faɗa tana mai daddaga yatsan nata akan saitin zuciyar tasa idanunta na cika da hawaye….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button