Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 16 Hausa Novel

Sponsored links

Aminu ya kalli Khalil yace “Ni wallahi ca nake saurayin nata ne ya dawo da daddaren nan kuma, kasan fa sai ya iya xuwa ya dauketa su tafi babu wanda xai sani banda ni da nake bakin gate din nan” Khalil yace “Saurayin wa?” Aminu bai kai ga basa amsa ba aka bude Driver seat, Hamid ne ya sauko tare da abokinsa Mujahid, a tare suka nufo gate din, tuni Aminu ya dinga jera ma Hamid gaisuwa uwa maroki, Hamid ya amsa yana kallon Khalil, sai kuma ya mika masa hannu, Khalil ya kai nasa hannun suka gaisa, Mujahid dai sai kallon Khalil yake, kauda kai khalil yayi ya fara tafiya xuwa gun mai gadin daya gidan dake kusa da su, Bayan sun shiga gate Mujahid na kallon Hamid yace “Waye wannan gayen?” Hamid yace “I don’t know, ni ma yau na fara ganinsa, probably gidansu na nan layin” Mujahid yace “No, he looks a bit familiar, amma gaba daya na mance inda na san shi…” Hamid yace “Wait” Juyawa yayi ya koma bakin gate, Mujahid ya bi bayansa, Hamid na kallon Aminu yace “Aminu” Da sauri Aminu ya nufi gate din yace “Na’am ranka shi dade” Hamid yace “Wanene mutumin nan da ku ke tsaye da shi?” Aminu yace “Au.. ai sabon dreba ne, kasan Habibu ya bar gidan nan, Alhaji ya bude masa tafkeken shago ya koma can, shine ya kawo wannan, ai ya kwana biyu da fara aikin ma” Hamid dai sai kallon Aminu yake, Mujahid yace “Driver????” Aminu yace “Ehh dreban gidan ne” Mujahid ya kalli Hamid, Hamid ya juya ya koma cikin gidan, Mujahid ya bi bayansa yace “Seriously kamar na san shi a UK” Hamid yayi dariya yace “Kai dai kasan me kama da shi a UK” Mujahid yace “Toh amma kaman is very obvious, kawai dai i can’t recall…” Parlon gidan suka shiga, Nihad na kwance parlor tana danna wayarta, tana ganinsu ta mike tayi wucewarta sama, Hamid ya bi ta da wani irin kallo, Mujahid ya saki baki shi ma yana kallonta, can yace “Yarinyar nan fa na feeling kanta da yawa” Hamid yace “A very spoilt Brat, right from when she is little bata da manners dama, unlike her half-sister Nihal…” Hamid ya xauna ya dau wayarsa ya hau kiran Farooq don dama wajensa suka zo. Washegari Monday Nihad ta gama shiryawa misalin karfe tara da rabi ta fito parlor, gaida Farooq da ya bi ta da kallo tayi, yace “Amma ba da wannan ɗan iskan mayafin xa ki fita ba Nihad?

Ta juyo tana kallonsa ta marairaice tace “Yanxu yaya me ya samu wannan mayafin? Dubi fa ya sauka har bayana fa” Yace “Wuce ki canxa” Muryar Umma suka ji tace “Ta canxa a saboda kai ke siya mata mayafan? Ko kuma sabida a jikinka ta yafa?” Ya juya ya kalli Umma, Umma tace “Sharesa kije kiyi breakfast din ki, ki kama gabanki” Dinning area ta nufa, Umma ta shigo parlon ta zauna, Farooq bai sake cewa komai ba, Nihad ta gama shan shayin da ta hada sannan ta mike, ta gefen ido farooq ke hararanta taki yarda ta kallesa ta nufi bangaren Mumy, a handle din kofar parlonta ta rataye mayafin sannan ta shiga parlon, zaunawa tayi saman kujera tana kallon Mumy tace “Ina kwana Mumy” Mumy tace “Wato sai kin gama duk abinda kike sannan xaki shigo ki gaisheni ko Nihad

 

Nihal bata ta6a kai wa karfe bakwai bata shigo nan ta gaisheni ba, amma ke sai sanda kika ga dama” Nihad tace “Toh Mumy ai saboda Nihal a nan bangaren take kwana shi yasa, ni kuma ai ba nan nake ba” Mumy tace “Toh yayi kyau ki ci gaba, nan gaba ma ki daina shigowa gaisheni kawai xai fi maki alkhairi” Nihad tayi shiru sai kuma tace “Kiyi hakuri” Mumy na kallon kayan jikinta tace “Wannan ɗan iskan dinkin kika yi da tsadadden atamfar nan kenan?” Nihad tace “Mumy gown ne fa” Sai kuma ta mike tace “Mumy na makara, yau muna da test” Mumy tace “Ki tabbatar Hijab xa ki sa Nihad” Tace “Toh, sai na dawo” Daga haka ta fita daga parlon, zare mayafinta tayi ta bar wajen da sauri sai da ta tafi dakinta ta dau jakarta sannan ta dawo parlor, lekan parlon ta dinga yi ta ga har lokacin Farooq na xaune, Umma ma na parlon, tana kallon Umma tace “Umma sai na dawo” Umma na Murmushi tace “Toh Allah ya tsare daughter” Ta saci kallon farooq tace “Yaya sai na dawo” Banza yayi da ita, bata ko kallesa ba ta fita, tana isa gate ko kallon Mai gadi da Khalil dake wajen bata yi ba tayi ficewarta daga gate din tana tafiya cike da isa, ta riga ta dau vow daga yanxu, da dai Khalil ya sake jan ta a mota gwara taje ta hau adaidaita, tayi canceling ta hau mota yayi driving dinta.

Mai gadi na mata Allah ya tsare ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa masa, kamar yanda bata kalli Khalil ba shi ma haka ba kalli inda ta bi ba, Mai gadi yace “Ikon Allah, yau kuma da kafa xa a makarantar” Khalil yayi murmushi kawai bai ce komai ba. Nihad na isa makaranta har wajen karfe sha daya basu da niyyar shiga lectures da su Husnah suna xauna Cafeteria suna ta hira abunsu, kaf Clique din sun canxa xuwa latest iphone da ya fito ko wata daya ba ayi ba amma banda Nihad, kuma kaf dinsu babu warce iyayenta suka siya ma, sun dai yi kame kamensu sun samu waya, Naf tace “Amma nayi mamaki kice ke baki da just 250k da xaki cika ki canxa waya, to shi wannan saurayin naki Aliyu meye amfaninsa?” Nihad tace “Aa ni dai baxan tambayesa ba, kuma dama ni bana tambayarsa komai” Sai kuma ta dau wayarta tayi dialing number Abba ta saka handsfree tayi masu alama su yi shiru, yana fara ring Abba ya daga yace “Hello dear” Shessheka ta fara yi tace “Abbaa”

 

Daga daya bangaren Abba yace “What happened?? Me ya sameki?” A hankali tace “Abba ina shigowa makaranta xan sauka daga mota wayata ta fadi screen din ya fashe gaba daya” Abba yace “Subhanallah” Nihad tace “Yanxu ga shi wayar ya dauke” Abba yace “Hasbunallah, baya yi yanxu wayar kenan?” Tace “Ehh baya yi” Abba yace “Toh abinda xai faru idan kin koma gida ki ba wannan driver din ya je inda ake gyaran waya a gyara ko nawa ne ma sai ya kirani ya sanar min” A hankali Nihad tace “Toh” Abba yace “Shikenan, Allah ya tsare gaba” Nihad tace “Ameen, Nagode Abba, sai anjima” Daga haka ta katse wayar tana kallonsu Naf dake sauraron Abba gaba dayansu, suka kyalkyale da dariya suka ce “Gaskiya ne er daddy” Nihad tace “Toh amma me yasa xai hadani da wannan fitsararren yaron, this plan isn’t going to work idan da shi fa” Husnah ta cije yatsa tace “Kashh, yau ga ranan Habibu, to wai shi wannan din dama har yanxu ba a koresa bane?” Nihad ta tabe baki tace “Toh mayen xai tafi ne? Wallahi duk abubuwan da nake masa ya ki tafiya sai ma gyara xama da yake yi a gidan yanda ku ka san gidan ubansa, yau ma fa wani gaye ne ya kawo ni schl don nace baxan sake shiga mota daya da drivern nan ba, ina tsaye busstop din anguwanmu sai ga benz din gayen, shine ya rage min hanya har cikin makarantar nan, amma da da adaidaita Sahu xa ku gan ni ae” Zully tace “Aa to baki yi masa yanda xai bar gidan bane, da nice tuni xan masa check out wllh, wannan ai karamin kwari ne” Nihad tace “Kai Zully wasu fa mayu ne, shi wannan a maitan ma yayi nisa, gaba daya na lura bai son barin gidan ne, tunda yana cin me kyau ya sha me kyau” Husnah tace “Kawai shiryawa xa mu yi mu je har gidan mu ci maki ubansa mu masa tijara”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button