Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 34

Sponsored links

“Hmmm I have a lot of questions, ya akayi ya daukeki ranar har daddy yace a bishi a kasheshi, I’m starting to suspect daddy akan gaskiya yake”…..

 

“Tsaya in sauka if you’re here to interrogate me!”…..

 

“Sorry wifey, I don’t mean it”……

 

Amma zuciyarsa taki aminta da babu wani abu tsakaninta da Deen, da zata amsa masa duka tambayoyinsa kila da komai yazo masa da sauki, ko ranar daya gansu a garden din ya akayi yasan suna chan? Ya akayi kuma ya dauketa a gidan daddy?, daya kawota gidansu kuma me yake nufi? Sai yaji gabadaya lissafinsa ya hargitse he needs more light on the issue…….

Wayar Umm dake hannunta ne ya fara vibrating alamun shigowar call, sosai hankalinta ya tashi har hakan yaso bayyana a fuskarta, tabe baki khaleel yayi yace;

“Would you stop this nonsense! Kasan fa wanda nake nufi”…..

Shiru khaleel yayi dan yasan wanda take nufi dagaske, kishi ne kawai ke damunsa shiyasa yake mata tambayoyi, yanaso ya cire Deen a zuciyarsa amma ya kasa, gani yake kamar there’s something between them….. Chan kuma sai yace

Kin tsaida motar yayi, cikin marairaice murya ya shiga bata hakuri…….

“I’m sorry wifey bazan kara ba wallahi, you know I love you so much ko? Sanki ne yajawo duk wannan abun da nake, but I promise to stop”…….

Bata kulashi ba ta kashe wayar Umm dake hannunta…..

So yake yace tabashi wayar ya boye ya cillar amma ganin ta hada rai ya sashi kasa cewa komai……

“Wifey we’re heading to the airport now”….

Kai kawai ta daga dan har lokacin bataji tayi wucewar da zata kulashi ba………

Haka sukaje sukayi boarding basu tafi da komai ba dama jirgin 6pm ne, yace in sunje sa siya……

Karfe shida Deen ya tashi, yana tashi ta fado masa arai, hankalinsa ne yayi gurinta sosai musamman yanda yasan bataci abincin kirki ba ranar, yasan kuma tsap zata iya kin fitowa daga dakin saidai kuma su mami na nan….

 

Ruwa ya fara wasawa yazo yayi sallolinshi sannan ya bar part din gudu gudu………

 

Sama ya fara haurawa gurinsu mami ganin yamma tayi sosai yasan kuma dole sun dubata by then…..

 

Tambayarsu ita yayi sukace ai sun dauka tana tare dashi, bece komai ba ya juya ya sauka kasa..

 

A bakin kofar dakin data kulle kanta ya tsaya, knocking ya shigayi a hankali amma shiru baa budeba……

 

Murmushi yayi gane fishi takeyi har lokacin sannan cikin kwantar da murya yace;

 

“Hey baby girl! Zo ki bude pls”….

 

Shiru har lokacin baa bude ba, Girgiza kai yayi aransa yana fadin yasan sai yayi dagaske kanta bude yarinya karama da ita sai zuciya, sake kwantar da muryarsa yayi yace;

“Kince baki gama dukana ba shine nazo ki karasa, so pls open the door”……

“Bazan kara miki ihu ba, kizo ki bude kofar pls, kinga bakici abinci ba tin safe”……..

“Oya let’s make a deal, open the door and punish me the way you want, I promise to be loyal”…….

“Has anybody ever told you how beautiful you are? Har kanki yayi kato ko? Toh you’re not even beautiful hhhh”……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button