Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 33

Sponsored links

Zuwa yanzu numfashin Iffah ma yana fitane da taimakon na’urori, yayinda jinin dake fita a jikinta har yanzu yake fita ta kunenta. Na ido da hanci da baki ne kawai likitoci suka samu nasarar tsaidawa. Baba yaro shine shugaba na masu maganin, dan haka ake basa damar shiga kai maganin da duk aka bayar dan ai mata amma da taimakon Jasrah kai tsaye. Yanzu ɗinma dai hakance ta kasance. Bayan neman iso aka bashi iznin shiga inda Iffah take, sai dai babu mai iya ganinta kasancewar zagaye take da glass…..

Bani kaɗai ba, nasan duk masu karatu tambayarsu zata rinjayane akan wai shin duk abin nan dake faruwa ina _Shahan-shan_ yake ne a matsayinsa na shugaba ga ƙasar ruman baki ɗaya bama daular ruman ba?. To amsar itace yana nan a cikin masarautar, sai dai kuma tun a yammacin jiya bayan dawowa daga sallar juma’a babu wanda ya sakejin motsinsa. Duk da dama fitarsa a zahiri ta zuwa massallaci ce kawai. Yana kuma da ƙofar dake kaisa har massallaci daga sashensa batare daya fito wani ya gansa kai tsaye a masarautar ba. Shiyyasa har zuwa yanzu wanda suka san fuskarsa ko’a cikin masarautar ma ƙalilanne musamman a cikin hadimai. Duk abinda ke faruwa a masarautar kuma kowa nada yaƙinin ya sani, sai dai ba’an miyasa ya zaɓi yin shiru ba.

Kamar jiya yau ma labari yajema Malikat Bushirat akan Shahan-shan bai fito sallaba har ta asubahi. A yanzu kam hankalinta ya tashi ba kamar a jiya ba data ɗauka dan yana fushi da auren da yaso bijiremawa ne. A take ta bada umarnin shirya mata zama da shi. Dan ita a karan kanta na uwa garesa bata da hurumin ganinsa a duk sanda taso ko kai tsaye bisa doka da al’adar masarauta da ƙarfin iko na Shahan-shan. Sai zuwa ɗaya tak na kowanne wata da yakanyi kawai na zahiri. Amma duk da haka Tajwar Eshaan kan saci jiki wani lokacin ya kawo mata ziyarar tsakkiyar dare cikin ɓadda kama batare da wani ya taɓa fahimtaba har yanzu a cikin masarautar.

Shiri ta farayi duk da batada tabbacin samun damar ganin nasa a yanzu, sai dai sanin duk ƴan majalissar fada na’a masarautar yau yasa bata fidda tsammani ba. Cikin sa’a kuwa cikin abinda baifi mintuna ashirin ba Ghazi ya zo ya isar mata da sakon ƙarɓuwar buƙatarta. Dan dama suma ƴan majalisar fadan nada buƙatar samun wanda zai duba shi, hakan kuma bamai yuwuwa bane dan ita dake amsa suna mahaifiyarsa da Malikat Haseena (Kakarsa) da matansa ne kawai ke da wannan hurumin saboda an tabbatar tun jiya baiko zo falo na uku ba. Sannan duk abincin da mai dafa masa ya shirya tun daga kan na daren jiya har safiyar yau da rana haka yake zuwa ya kwashesa ba’a taɓa ba.

Cikin shiri na alfarma da rakkiyar tawagar hadimai maza da mata Malikat Bushirat ta doshi sashen Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed……

Tuni labari ya kai kunnuwan sauran matan gidan musamman Malikat Ashwaq da Ameera Danish-Ara da Ameera Haifah cewar Malikat Bushirat ta ziyarci Shahan-shan saboda rashin jin motsinsa. Hakama wasu a cikin matan manyan masu faɗa aji a gidan harma da mazan, wasu iyaye, wasu ƴaƴa, wasu jikoki. Hakan yasa aka kafa gungu-gungu na cigaba da tattaunawa tare da sukar cewar yasan tsiyar daya aikata ai shiyyasa ya ɓoye kansa. Kokuma dodon tsafin nasa ne ya bashi wannan umarnin naƙin fitowa har sai yarinyar mutane ta mutu…

 

Wasu kuwa murmushine kawai nasu dan su kaɗai suka san kansu. Yayinda wasu ke tausayama Tajwar Eshaan ɗin da ganin abubuwa ne suka masa zafi da yawa dan suna kallon komai a matsayin makirci da mafi yawa akafi dangantashi da matan ubansa, da kuma ƴan uwan mahaifin nasa na jini masu zawarcin son hawa wannan kujera… (To koma dai miye ALLAHU shine mafi sani).

 

 

Duk inda ta gitta hadimai zubewa suke akan gwuyawunsu suna miƙa gaisuwa. Ko sau ɗaya bata ɗaga ido ta kalla kowa ba, sai hadimanta ne ke amsawa duk wanda yay gaisuwar. Tun’a harabar shiga sashen dukkanin hadimanta suka dakata. Sashen Shahan-shan shine mafi ƙyawu da ƙawatuwa na ƙyale-ƙyale a daular ruman. Gini ne da kusan zamuce an yisa da zallar gilashi. Yanada hawa huɗu dan haka sai da lifter. Zaman lissafin dukiya da daular da aka zuba a cikinsa da kuma ainahin fadar da Shahan-shan ke zaman fadanci ma ɓata lokacine. A lokuta da dama duk abinda ke faruwa a cikin masarauta Tajwar na kallo daga cikin sashensa musamman idan a hawa na ƙarshe yake, hatta da wajen masarauta yana iya hangowa. Hadiman dake tsaron sashen matsayin sojoji suka maye gurbinsu wajen take mata baya har falon farko. Anan ɗin ma hadiman zubewa suka dingayi ƙasa kawunansu a risine domin girmamawa a gareta har zuwa falon farko. Wanda suka rakota ciki suka dakata, na falon farkon dake a hawa na ɗaya suka take mata baya har zuwa falo na biyu a hawa na biyu, suma iyakarsu nan, wanda suke a falo na biyu sukai mata rakkiya har zuwa falo na uku dake a hawa na uku. Anan soja ɗaya ne, shine amintacce da yake iya haurawa har zuwa falo na huɗu hawa na huɗu a falon dake can. Anan ma akwai hadimi ƙwara ɗaya sai masu dafa masa abinci su biyu suma. Sune amintattun na ƙarshe dake iya zuwa hawa na can ƙarshe na huɗu kenan, suke iya ganin Tajwar kai tsaye kuma, suke iya sanin a wane ɗaki ya kwana, suke iya shiga ɗakin barcinsa suyi gyara ko kai abinda yake buƙata, ko isar da wani saƙo. Bayan gaisuwa a gareta Ghazi ya nema afuwa da bashi damar zuwa nema mata iso ga Tajwar. Hannu kawai ta iya ɗaga masa.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button