Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 19

Sponsored links

“Kai, Allah dai ya shirya, nidai yaya sai inga kamar gwara a barshi ya kawo wacce yakeso da kansa, kina gani wacce ya damu da lamarinta ma ba kyaleta yayi ba inaga wacce kwata kwata baya bi takanta, tsoro nake kar ayi aure ya dinga cutar musu da yarinya da wannan zafin zuciyar tasa”…..

“Kinfi kowa sanin halinsa Umm, I’m sure ko zaa bashi nan da ten years baze kawo wacce yakeso ba, toh haka zamuyi ta zuba masa ido ba aure?”……..

“Hakane kuma, Allah ya tabbatar da alkhairi…

Fatima zainab na jinsu tayi kamar bataji, dan tsaki tayi aranta tace ashe aure ma zaa masa shiyasa itama yakeso ya mata auren dole kenan, aiko gwara tin wuri tasan inda dare ya mata dan zama a gidan ba nata bane……..

Haka suka cigaba da mata tambayoyi kala saidai kememe ta kasa basu kwakkwarar amsa kuma har cikin zuciyarta bata saniba, kamar dai wacce tayi losing memory dinta haka take basu amsa……….

Deen befi 30 mins da fita ba sai gashi ya dawo dauke da wata bakar leda sai envelope guda biyu a hannunsa…….

 

Umm ya mikawa envelope daya, ta karba batace komai ba ta hau karanta content din……..

Tashi fatima zainab da bata gane kan zancensu ba tayi ta bar parlourn, dakin da aka fara kaita randa ta fara zuwa gidan ta tafi ta kwanta tana tinanin yanda zata bar gidan ta kuma bacewa rayuwarsu gabadaya yanda duk neman da zasuyi bazasu ganta ba, sai kuma tinanin halin da khaleel yake yanzu ya fara damunta, tasan duk inda yake hankalinsa baa kwance yake ba..…….

 

Bin biyanta da kallo Deen yayi kamar ze lasheta har saida ta bace masa daga gani sannan ya dawo da kallonsa kan su mami, sai a lokacin yaga yanda suka tsaresa da ido, cikin borin kunya yace;#

“Sai kusan yanda zaku mata fada ta dena shayeshaye, dan in bata dena she’s at more risk”…….

Be jira cewarsu ba ya ajye ledar dake hannunsa shima ya fita……

Saida daddy ya saukewa khaleel lafiyayyun maruka guda biyu sannan ya nunasa da yatsa cikin bacin rai yace;

“Ni zaka tozarta khaleel? Ni ni! Ni mahaifinka dana nuna maka gata fiyeda kowa a cikin ya’yana shine zaka rufe ido saboda mace kana nema ka tona min asiri? Why are you so stupid for love? Akanka aka fara soyayya ne khaleel daka bari hankalinka ya gushe akan wacce ko damuwa batayi dakai ba, ko kunya bakaji ajika da mahaifinka akan mace? Mata gasunan dayawa kamar pure water sai wacce ka zaba ma, kai da a tinaninka zan barka ka auri fatima zainab ne? Ina take da tarbiyyan da zaa zauna da ita a matsayin mata?, kai bama wannan ba bazan taba yarda ka auri yarinyar da bata da asali ba, a titi fa na tsintota khaleel, a titi fa! Tana rike da sigari a hannu, wannan kakeso in bari ka aura? Allah ya kiyaye wallahi, gwara tin wuri kasan inda dare ya maka ka nemo yar mutunci ko yar gidan uban waye namaka alkawarin zan aura maka ita, damuwata kawai ka rabu da yarinyar nan!!!”……..

Khaleel zeyi magana kenan daddy ya dagatar da shi da fadin;

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button