Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 14

Sponsored links

Koda ya dawo be nunawa momma komai ba dan tanata nan nan da yarinyar kamar yanda yasan tanayi da, sai ya fara dan bincike har Allah yasa ya kamata red handed, lokacin sun dawo daga masallaci shida abdul a ka’ida baya shiga part dinsu a irin wannan lokacin, ranar sai yabi abdul suka shiga, abun al’ajabi suka samu momma nata jibgar fatima zainab dake bacci a kitchen, dukan duniya kuma taki tashi saboda yanda tasha tayi makil bayan sallar asuba, tana dukanta tana zaginta harda fadin batace mata tadinga barin kitchen da sassafe ba, sai tayita bacci saboda alhaji yazo yaganta ya gane a kitchen take kwana……

 

Karap wannan magana a kunnen daddy da ya zama very shocked tinda suka fara jiyo maganganun momma……

 

Abdul ne ya ankarar da momma da tsayuwar daddy, ta jiyo sukayi ido hudu da daddy daya dafe kansa yana jinsa highly betrayed!….

 

Zatayi magana kenan ya daga mata hannu sannan yace ta tafi gida sai ya nemeta dan yasan inta cigaba da zama a gidan yana ganinta komai ze iya faruwa…

 

Har kasa ta tsuguna tana basa hakuri daya bata second chance zata rike yarinyar da gaskiya dan denying be taso ba tinda ya riga ya kamata red handed……

Dago fatima zainab yayi data riga ta farka ya rike hannunta yayi hanyar fita da ita……

“Kullum saina tambayeki a waya babu abinda ake miki sai kice min babu, meyasa baki taba fadamin abinda take miki ba daughter? Meyasa?”…..

“Karki damu babu abinda ze sameki da yardar Allah, daga yanzu duk wanda ya miki wani abu a gidannan ki fadamin kinji daughter?”…..

 

“Toh daddy”…..

 

Part dinsa ya tafi da ita yana kiran mama a waya…. Shigowa mama tayi da sallama hankalinta na kan fatima zainab, guri daddy ya nuna mata ta zauna, yayi gyaran murya ya fara magana;

 

“Hakika hafsah kinmin abinda ban taba tinanin zuciyarki zata bari kiyi ba, kin ankarar dani muguntar da akeyiwa marainiyar Allah da bataji ba bata gani ba, a yanzu bazan iya bari ta kara zama a gurinta ba, bansani ba ko ke zaki iya rikemin ita amana?”…..

 

“Nasan kanamin kallon wacce bata da kirki saboda yanda nake nuna kishina akan ka a fili, inaso ka sani son da nake maka ne yasa nake behaving haka, amma wallahi Alhaji bazan iya cutar da kowa akan hakan ba, ka jarrabani zan rike maka ita fiyeda yanda kake tinani”…….

“Kinyi alkawarin zaki riketa tsakani da Allah? In kinsan bazaki iyaba kema gwara ki sanar dani in nemi inda zan kaita”…

Daddy ya sake tambaya dukda ya gamsu da maganganunta, ya kuma yarda tana son shi sosai kamar yanda ta fada, kuma ko ba komai gwara ita tinda tana nuna abinta a fili akan momma me munafurci……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button