Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 8

Sponsored links

Hankalinsu duka baa kwance ba suka isa gida saidai cikin saa har lokacin Ababa bai dawo gida ba Hande ce kawai taketa fadan

sun samu sake sunyi dare babu wanda yayi magana acikinsu saida tagama yi musu tatas kafin suka hanzarta yin sallah suka fito suka karbarwa Annensu aikin da bata gamaba har lokacin.

Wani sabon wankin ne suka fara cikin dare basu gamaba sai guraren karfe tara na dare

Daqyar sukai sallah sukaci dan abincin da aka basu suka kwanta kowannensu gababin jikinsa na ciwo.

Washe gari haka guraren 9 na safe suka isa makaranta.

Sumayyah kai tsaye libry ta isa sbd acan zasuyi karatu da wadda sukai jiya,

Tana isa zata shiga ta nema id card dinta ta rasa,

Gefe ta koma ta zazzage jakarta tafara dubawa hankalinta na fara tashi sbd batasan ya zatayi ta samu wani ba komai Benazir ce take yi mata bata iya zuwa da kanta.

Dubawa takeyi da gaske tana bin pages damuwarta na bayyanuwa duk da tanada tabbacin yana jakar bata fiddasa ba.

Duk abinda yake jakar tayi masa daddaya amma bata gansa ba,

Tattara kayanta tayi ta maida jakar ta nufi gurin Benazir cikin dan sauri da damuwa,tsoronta da tashin hankalinta shine ace sai ka biya kudi zaa maka wani,

Ina zata samu kudin?Ababa idan suka fada masa saiya kusan rabata da duniya kafin ya bada kudin,ya Allah yasa ta gansa kokuma baa biyan kudi ake bada wani.

A yau dinma tashin hankalinta bai bari tana tantance inda take saka kafafunta ba kanta a qasa har ta isa department dinsu Benazir din.

Kiris ya rage tayi karo da wanda yake tahowa yana amsa waya cikin nutsuwa da sanyin hali

Da sauri ya dago hannuwansa yayi saurin tareta sbd kada jikinsu ya hadu.

A firgice ta dago tana ja da baya cikin qarfin gaske sai gata a qasa

Bata damuba ta miqe da sauri kanta na yin qasa a sanyaye ta basa hakuri tana sake sauke kai kaman wadda take gaban Ababa.

Cikin dan mamaki ya kalleta yana tabbatarda itace mai student id card din hannunsa,

Juyawa tayi zata wuce batareda ta dago ta kallesa ba zuwa lokacin jikinta rawa yakeyi sosai dan gabaki daya Azabar Ababa kawai take jin har tafara sauka jikinta.

“Hey Miss” yafada da muryarsa mai kamala yana taba Aljihun tsadaddun qananun kayan givenchy dake jikinsa baiji card din ba ya dan rintse ido a hankali yana tino yana cikin motar daya shigo makarantar jiya da ita.

Ba damuwan komai a ransa ya ambaci sunanta kai tsaye daya tina shine a jikin katin ganin tana sake sauri kaman mai tsoron mutane a bayyane sai kawai ya qyaleta ya wuce yana duba time din agogonsa sbd ba lokaci zai bata ba a school din zaiyi magana ne kawai da prof ya wuce gurin aikinsa.

Yana wucewa Sumayyah data labe daga gefen wasu students ta futo tana kallon inda yabi da ido tsoronta na qaruwa sbd ta tina fuskarsa shine ta gani jiyan ya tsaidata.

Meyake so a gurinta?

Baiyi kama da student ba sbd shekarunsa da jikinsa tareda maturity dinsa sun bayyanarda hakan,

Kyawunsa da kwarjininsa tsoro ya bata matuqa tareda firgitata,babban tashin hankalinta kada ya sake tsayar da ita wani yagani tsautsayi yasa Ababa ya sani Alkiyamarta ta tsaya.

Benazir data qaraso gurinta tana dafata daga baya saida sumayyar takusa shaqewa sbd tsoro da tashin firgita,tana waiwayowa taga Benazir ce wasu hawayen mutuwat jiki suka ciko idanuwanta ta sauke tana kokarin hanasu saukowa.

Kasa magana sumayyah tayi ta silale ta zube zaune kan gurin zama tana kokarin daidaita numfashinta dayake futa da sauri na tashin hankali biyu datake ciki na batan student id card dinta dakuma mutumin daya tsayar da ita wadda sunfi kaunar hadarin mashin da wani namiji ya tsaidasu.

 

Shafa bayanta Benazir ta ringa yi ahankali ta cikin hijab dinta tana cewa

“Ki kwantar da hankalinki kada ki bari yanayinki ya sauya asan halinda muke ciki kaman yanda Ababa yafada mana.”

A hankali ta ringa sauke numfashi tana kokarin daidaito nutsuwarta har tsowon mintina kafin ta dan dawo daidai ta dago idanuwanta da har sunyi jajir ta kalli Benazir dake jiran bayaninta cikin fargaban idan ba wani abin ne ya sameta ba.

Bude baki tayi ahankali ta yiwa Benazir din bayanin batan student id card dinta tareda kasa fada mata mutumin da yayi mata magana sbd tinowa da hakan kawai girgiza kayan cikinta da zuciyarta yake bare iya bude baki ta fadawa ko Benazir cewan wani namiji ya tsaidata.

Shiru Benazir tayi sbd itama batasan ta ina zara fara ba tunda ba muaamala sikeyi ba da mutane bare su tambaya qarin bayani.

Shiru sukayi sun jima a hakan batareda sanin abin yi ba,ganin hakan Sumayyah taji gabaki daya hankalinta ya qara tashi suka fito daga department din suka nufi gurin da babu mutane sosai suka zauna take Sumayyah ta fashe da kuka mara sauti tana jin yanda zasu sanar da Ababa hakan.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button