Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 2

Sponsored links

“Jikin yaran ne yahau rawa kar kar kar kaman wanda aka sa masu shocking kamin salihu yace” A’a ke ba sa’an mu bace, Don Allah Sima kiyi haƙuri”. Kallon sama da ƙasa Sima kebin yaran dashi don so take ta fanshe hushin ta akan su ,yau ta wayi gari babu sisi , wannan yasa ta kai hannu tana damƙo Samuel da yake aikin raba ido yana neman hanyar fechewa ,don yasan irin laifin da yayi mawa Sumayya ta damƙe shi mai rabasu sai Allah”.

Oh Jesus! Samuel yayi maganan yana haɗe hannayen shi biyu alamun addu’a. Wani irin dariya Sima tasa tana murtike fuska tamkar ba itace tayi dariyar ba ,kamin tace ” Jesus ɗin uban ka,gama addu’a n naka tass ,yau sai ka san Allah ɗaya ne. Sima pls forgive me…Sima Sorry pls.

Wani irin gigitaccen tsawa ta daka masa wanda yasa shi yin shurin da bai shirya ba ,sai wani irin gumi da yake haɗawa kaman yayi wanka da ruwa ɗumi…Forgive ɗin ubanka ai Ni bansan meye kalmar ba tayi maganan tana ware manyan taffan hannayen ta tana zubasu a fuskar Samuel wanda jin sautin ƙarar marin tassssss kaman saukar tartatsin wuta yasa su salihu rugawa a wani irin matsiyacin gudu , suna barin Sumayya da Samuel da yake wani irin tsala ihuuuu …aaahhhhh kawai yake cewa yana kururuwa n neman agaji,kun san arna idan iftila’i ya same su basu san Allah ba sai ihu na banza…tsala ihu agaji yake yi amma kash kowa na leƙowa yana ganin Sumayya ce sai ya juya da sauri ,don tayi ƙaurin suna wurin iya masifa da tijara”.

Bakayi mata ba tayi bare kuma kayi mata? Wannan yasa duk dukan da take mawa Samuel babu wanda yaje ƙwatar sa ,sai magulmata da sukayi saurin sanar da maman biyode wanda ta kasance mahaifiyar Samuel a hasale ta ƙarako inda Sima ke zaune tana ba Samuel punishment a rana ita kuma tana gyefe a inuwa . Sam bata lura da Mmn biyode ba don idon ta a rufe yake cewa take” idan ka tsaya da up and down ɗin nan wallahi sai nayi ƙasa ƙasa dakai ƴan iskan yara marasa mutunci , nice Sima wando dai dai da kugun kowa….

Ɗan ta Mmn biyode ta nufa tana tada shi tsaye kamin ta nufo Sima da itama miƙewa tayi tsaye tana kallon ikon Allah ,ta kama kugu tana shirin tijara taji Muryar Mmn biyode na mgn cike da masifa….l I have never see stupid goat like you…mene yaro na yayi maki,always fighting ³ wid people! what’s wrong with you Sima? won’t be agree baxan yarda ba wurin Uwar ki zanje yanxu ,Allah yasa ba hauka ne akan ta ba itace asibitin mahaukata na duniya…zan kai ku court……wani irin rintse ido Sumayya tayi tana jikin ta na kyerma hawaye na bin kuncin ta , babu abun da ya ɓata ranta irin ambaton mahaifiyar ta da Maman biyoda tayi ta zaga…har da zagin lallarurar ta na hauka”. Yanda jikin ta ke tsuma kaman boss yasa Maman biyoda saurin kama hannun Ɗan ta tana shirin gudu wa…

Sumayya ne ta kai hannun ta tana miƙashi ga bishiyar darbejiyan dake kusa dasu wani tsalle tayi tana karyo reshen haɗi da daka tsalle tana biyo bayan Maman biyoda ,ihu ta hau yi tana faɗin Umma na zaki zaga ,kamin Maman biyoda ta juya taji saukar Sandar darbejiyan tauuuuu”. Wani irin gigicewa Maman biyoda tayi tana riƙe Sandar ,nan suka hau kokawa da Sumayya wanda dukan mmn biyoda take tana faɗin Umma ta zaki zaga yau sai nayi ƙasaƙasa da kowa naku…

Ihun maman biyoda da Sumayya yasa mutane fitowa daƙyar aka ƙwaci mmn biyoda a hannun Sumayya da ke ihu tana faɗin Umma na zaki zaga??????….

Murmushi Sumayya tayi a hankali tace ” Allah sarki Umma na , bazan bari bashin lapo su tajaramaki Ni ba , zan waxgi iya rabona mai Company kayi haƙuri nima ba’a son Raina zan saci kuɗin ku ba…astagafurullah mun astagafurullah mun tayi maganan tana hayewa wani dogon stairs , ba tare da tayi tunanin komai ba”.

Idon ta ne yy wal³ ganin hasken wurin yasha ban ban dana inda take , tabbas anan dukiya take! Tayi maganan a zuciyar ta tana takawa zuwa wurin wata matashiyar budurwa da ashekaru zata kai 32 ganin an rubuta sectary yasa Sumayya nufar inda take kai tsaye”.

Tsaye Sumayya tayi akan ta wanda mulki ya hanata ce mata komai wanda itama sectariya isa da mulki yasa bata kalli Sumayya ba…kujerar gyefen ta Sumayya tajah ta zauna ba uhm bare uhm’uhm. Wannan yasa Hauwa ɓaidu ɗago idon idanun ta cike da masifa tace ” Malama ba’a zama mana anan.

Shiru Sumayya tayi kamin ta ɗago da dara daran idanun ta tana watsa mawa sakatariyan wani irin kallo na baki isa ba kana ta motsa laɓban ta tana cewa ” Ba’a zama kuma aka aje a gurun?.

Ta ƙare maganan suna kallon kallo, fahimtar Sumayya ƴar bala’i ne kuma gashi a ƙaidar Company n kukayi faɗa korane ko cacan baki yasa Mrs Hauwa ɓaidu cije lips ɗin ta tana kwantar da murya wakike nema ko nace me kike so?”. Ina son magana da mai wannan wurin ne?. Saurin kallon ta Mrs Hauwa tayi kamin ta fara tunanin Anya Sumayya nada hankali kuwa? Sir Khamal da idan aka ganshi gudu akeyi ita tazo tana wani ce mata tana son magana dashi? Mutumin da idan yayi magana da kai sau uku to na huɗun korane??….

_Littafin na kuɗi ne normal group ₦300 vip group ₦500 spc ₦1000 zaki iya turo da katin MTN ta wannan number 08081202932 ko ki tura ta wannan account details…6037312299 Mohammed A’isha keystone bank Idan Vtu trnsfer ne kiyi ta wannan number 09061466409 zaku na iya fara payment ɗin cox free page ba da yawa xanyi ba_

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button