Hausa Novels and Stories

Idon Naira 39

Sponsored links

Gashi sunga an kushe gyaransu ansaka tayi sun dauka shiga tafisu samu agun hajiyar gidan basusan wulaqanta tafisuba.

Duk uban aikin dasuketa fama dashi kwana biyu babu Wanda Haj Maryamah ke yabawa sbd tsaurin raayinta da yai yawa,

Duk aikin dasuke Mata Dama acan Bata Jin dadinsa Kuma tana nunawa Koda yaushe Amma sbd su kadaine sai basa damuwa sunyi sabo da halinta shiyasa suka Dena damuwa,

Amma anan duk aikin dasukai bayayi saita saka zainab tayi Mata wani sai hakan yasa sukejin daci da zafin zainab din a ransu,

Musamman babah ladi data fito fili ta bayyanarda rashin kaunar zainab din dake ranta,

Ita shafa’atu tana Dan taqaitawa sbd MARYAMAH data shiga ranta Dan tana tsananin kaunar yara.

Girkin abincin gidan a hannun babah ladi yake Dan haka idan tagama kullum Dan kadan take bawa zainab

haka zataci ko Bata koshiba zata Sha ruwa ta Kama kanta gashi tana shayarwa tana buqatan abinci sosoi gashi mukullin store a hannun babah din yake koyaushe da gayya take yawo dashi a jikinta duk inda zata.

Idan har tasamu taci abinci isashe yanda ya Kamata to itace tayiwa Haj Maryamah girki aranar dan bako yaushe haj maryamah din ke Jin Dadin abincin babah ba.

Shi gyaran bangarenta Kuma tuni yadawo kan zainab din da batason na shafa’atu Kuma tanada qarancin yarda shiyasa zainab kawai ke Mata gyaran daki taji hankalinta akwance da dukiyarta.

Bayan gyaran sashen Haj Maryamah harda abincinta yadawo kanta sai gashi kusan duka aikin gidan kadan ne basa kanta ga MARYAMAH da rigima sosai harma da qyuya Dan haka duk aikin dazatayi tana bayanta ko hannunta.

Ahakan suka fara Jan lokaci sosai suna wani irin mugun zama a gidan tsakaninta dasu babah..

‘yarta MARYAMAH tayi wayo sosai harta iya zama da rarrafe Amma batasan kowaba bayan mahaifiyarta,

Bata sabu dasu babah ba Dan basa janta ajiki bare hajiyar gidan da iyakacinta da ita idone.

Aqeel kuwa yayi rokon,

Yayi neman ummansa ta hadasa da mamin tasa Amma kullum uzuri take basa

Har waya yace asiya abata Amma duk dai hakan bai samuba Amma tunda dai ta sanar dashi suna lafiya hakanma yasa hankalinsa ya kwanta.

Babbar matsalar da aka fara samu a gidan shine tsanar da ake nunawa ‘yarta wadda ko sunanta basa Kira sbd sunan hajiyar gidan ne da hakan qarfi da yaji suke Kiran yarta da KE, kokuma ‘YAR ZAINAB..wannan kalmar itace abinda yake sosa ran Zainba aduk lokacinda suka Kira MARYAMAH dinta da hakan,

Tana danne wannan lamarin ne matsala ta bullo tsakaninta da Haj Maryamah akan MARYAMAH din datake zuwa da ita gyaran bangarenta Dan yarinyar nata barna sosai.

Tun lamarin na dannuwa a ranta har abin yafara yimata yawa Dan kuwa kusan kowa a gidan kyarar Mata ‘ya sukeyi.

Daga ita har yarta kamar wasu almajirai suke a gidan Dan kuwa kayansu na sakawa tuni suka mutu wasuma duk basa shigar MARYAMAH din Amma ahakn take saka Mata su tunda basuda wasu.

MARYAMAH sai datai kusan shekara biyu Ta yayeta sbd yarinyar itama yanayin rayuwar dasuke ciki yafara tabata,

Sam yanzu batada walwala ko sakewa yarinyar,

Duk da qarancinta tasan batada sakewa komai tayi na barna dukanta su babah da shafa’atu sukeyi tun zainab na kauda Kai har tayi magana sai abin ya zama fitina

Dama babah mutuniyar banza ce gidan abinci a Tasha takeda Jin gida masu kudine zaa Kai yar aikin abinci ta rufe shagonta tazo ta karbi aikin shiyasa take tsula tsiyarta son ranta tunda Haj Maryamah din Bata wani zama ba ruwanta da Yan aiki gashi yanzu itace shugaban masu aikin gidan Dan haka take zuba tsiyarta son ranta.

Zainab rayuwa a gidan tafara yimata tsanani,

Komai ya juye a rayuwar gidan ba kamar da ba,

Idan zata sashen Haj Maryamah ta dena zuwa da MARYAMAH ‘dinta sbd gudun fitinar dazata biyo baya idan tayi Mata wata barnar datafi fasa Mata laptop datayi ta aikinta.

Acan dinma idan tabarta kafin Takoma sai ta tadda bacin ran wani abun

Duk tabi ta fige da masifar gidan da yanzu komai ya lalace mata,

MARYAMAH sbd tsangwama da kyarar datakesha yasa gabaki daya ta rasa walwala da kuzari tareda sakewa irinta yara,

Idan har ba ajikin uwarta takeba Bata wani dogon motsi a gidan.

Wannan yasa itama zainab din ta tasa kuzarinta gabaki daya suka koma kamar Yan gudun hijirar gidan kullum suna daki kamar masu abin kunya.

Ana haka kwatsam Allah yayiwa mijin Haj Maryamah yace ta tattara tadawo Abuja gabaki daya.

Da farko shafa’atu aka fara sallama sbd idan Takoma Abuja Bata buqatar ya aiki da yawa sbd hutawa takeson Yi batason hayaniyarsu Dan can gidan baiyi girman wannan ba da bazakaji motsin masu aikinbama.

Ganin an sallami shafa’atu yasa hankalin babah tashi Dan ta fahimci zaiyi wuya a kori zainab duk da gata da ‘ya da Bata barin tayi aiki dakyau.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button