Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 18

Sponsored links

Humm Sumayya ta nisa tana kallon Haulatu kana tace ” Ke ana faɗa maki har yanxu bata sauko ba , tana can sama tana bacci ita da ɗan ta…yanxu abinci na kawo maku ku ci sannan ,Ni Bara na koma… Safna ce ta fito tana amsa kana tace ” Wallh ko kamannkn san yanxu Umma ta tashi daga bacci Bara a sa mata ruwa tayi wanka sai taci abincin. To nidai na koma”. A dawo lafiya sukayi máta tana fichewa cikin sauri.

Bayan koma wanta gidan Hjy Juwairiyya ne ta haɗu da Oruma wanda cikin sauri take cewa ” Kije kiyi serving nasu , suna dirning yanxu . Buɗe baki Sumayya tayi cike da mmki tana cewa “Au yanxu abincin ma Ni xan zuba masu suci?.

Ke Summy ki shiga da sauri , wannan ƴar bala’in Binafa tana nan tana cika wuya. Ganin yanda Oruma ta rude yasa Sumayya nufan falon ,wanda kai tsaye Dirning area ta nufa…wani irin ƙamshi ne ta shaƙa mai daɗin gaske , wanda yayi mata gauraya kaman da wanda tasan ƙamshin sa irin haka…………

Cikin sauri ta nufi Dirning ɗin tana zubewa har ƙasa tana gaishe da Alh Y Kumbo Wanda ya kasance mahaifin Khamal , fuskar sa sake cikin fara’a ba izza da mulki ta masu kuɗi babban mutum wanda ashekaru yakai 70 . Kallon Hjy Juwairiyya tayi da take cikin tsadaddan lace black Wanda itace take serving din su tana zuba masu abincin kowa a gaban shi , sun san Shi Daddy Kunu ake masa ta gyaɗa da safiya wannan yasa Hjy Juwairiyya tsiyaya masa a wani cup tana risinawa tare da ajewa a gaban shi….Binafa ce da take ta kallon Khamal wanda bai san tana yi ba , yana can yana latsa wayar hannu shi… ɗago da idon ta Binafa tayi tana dalla mawa Sumayya Harara kana tace ” Ke meye aikin ki a gidan nan da har sai Momy ta yi srvng ɗin mu ? Ke ba ƴar aiki bace?”. Tayi maganan a gadarance cikin faɗa? Jikin Sumayya ne ya hau Rawa ,cikin sauri ta amshi ladle ɗin hannun Mom Juwairiyya tana cewa ” Yi haƙuri hjy bari na yi. Humm zama mom Juwairiyya tayi , Daddy ne yace”Aa Binafa kiyi haƙri ƙila wani uzurin ne ya zo mata but yanxu ba gashi tazo ba?”.

Talia ce ta zuba masa a platin Gaban shi tana ɗaura masa miyar hanta akai tare da cewa ” Yallaɓai Bismillah”. Tsam Khamal yayi jin Muryar da baxai manta dashi ba , don duk maganan da suke yi bai tankasu ba ,bai ma sauraren su sai a yanxu . Wuce shi tayi tana nufar Binafa tana ɗaukar ruwan lipton tana shirin aje mata , ɗago da dara daran idanun shi yayi yana watsa su ga sabuwar ma’aikaciya r Momyn tasa….Wani irin shock yayi yana kallon ta gaba ɗaya ƙwaƙwalwa e sa ta tsaya cak….LADY BOSS? Tartstsatsannnnnn kaji Sumayya ta saki cup din tea din tana watsa ma Binafa da tayi zumbur ta miƙe don ruwan zafin ya taɓa ta sosai…..wani irin mari ta ɗauke Sumayya dashi ji kake tassssss ke makauniyace wacce jaka ce?”.

Binafa kina da hankali kuwa? Cewan Daddy cikin ɓacin rai….Daddy zuba mun ruwan zafi tayi fah, Binafa tayi maganan cike da shagwaɓa tana shirin sa kuka. Sumayya ko da nata hawayen ya riga sauka , cikin sauri da gudu ta bar wurin….tana nufan store. Duk da hakan baki ga yarinya ce ƙarama ba? Cewan Daddy cike da damuwa don bai ji daɗin marin da Binafa tayi mawa Sumayya ba .

Miƙewa Khamal yayi yana barin wurin tare da nufan falon Daddy. Zama yayi shiru yana tunanin abubuwa tabbas dubu ɗari hudun da ta ɗeba masa a wurin sa bai ganin sa a koman komai . Zai iya bata kyautar million bai dame shi ba ,bai kuma ji komai ba , amma maganan da ta yaɓa masa shine baxai iya yafe mata ba…wanin zagaye na ne , xan axabtar dake , zaki san koni waye? Zan saki kuka na dana sani….miƙewa yayi yana nufar store inda yaga ta nufa ..cikin takon sa na taƙama ya kutsa kai dai dai Mom Juwairiyya na miƙa mawa Sumayya takardar sallama daga aiki…..

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button