Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 102

Sponsored links

Cikin ƙanƙanin lokaci ta kimtsa, ta saka kamshin data maida nata ta ƙarfi da yaji. Tana fitowa daga sashen ta samu hadimanta na jiranta. Gaisuwarsu ta amsa a yau kam da kulawa, kafin ta shiga motar da zasuje sashen Malikat Bushirat ɗin a ciki duk da bawani uban nisa bane, amma akwai tazara gaskiya. Sojan daya buɗe mata yay salute ɗinta kafin ya maida ƙofar ya rufe, da sauri suma hadiman suka shiga ɗayar motar bayanta.

 

A tafiyar da bata gaza mintuna biyar zuwa bakwai ba suka iso, anan ɗin ma dai buɗe mata akai, yayinda hadimai ke faman zubewa ƙasa bisa gwiyawunsu. Hannu kawai Iffah ke ɗaga musu da sakewa. Tausayinsu da sake jin zafin wannan mulkin iko na kasarsu a ranta. Tun a falo na farko tabar hadimanta, inda amintacciyar hadimar Malikat Bushirat ta karasa mata iso har inda take.

 

“Barka da yamma Mah-mah”.

 

Iffah ta faɗa cikin girmamawa ga Malikat Bushirat dake hakimce fuska babu walwala. Hannu kawai ta ɗaga mata, daga haka falon yayi shiru. Sai da ta gama shan kamshinta kafin ta tashi zaune da ƙyau idonta akan Iffah da ta rissinar da kai .

 

“Ibnati kin san miyasa na kiraki?”.

 

“A’a Mah-mah”.

 

Iffah ta amsata da sauri. Cikin ɗacin murya Malikat Bushirat ta cigaba da faɗin, “Akan mijinki ne, nasan duk abinda ke faruwa a Masarautar nan kin sani kema”.

 

“Hakane Mah-mah, amma sai nake ganin kamar ba haka bane, kawai dai wasu ne ke son ɓata masa suna”.

Har cikin rai kamalan Iffah sun saka Malikat Bushirat jin sanyi a rai, sai zuciyarta na rawa dan zuwa yanzu al’amarin ɗan nata da gaske tsoro yake bata. Yayinda ita ko Iffah ta faɗi hakanne da manufar wayon da ALLAH ya bata domin son fahimtar abinda take son sani.

Malikat Bushirat ta katse mata tunani da faɗin, “Hakan zai iya zama gaskiya, sai dai bazamu saki jiki ba dan da gaske al’amarin mijinki na bani tsoro. A yanzu haka na bukaci ganinsa amma shi yace bai buƙatar ganin kowa”.

Da mamaki Iffah ta ɗan ɗago ta dubeta, a ranta kam jinjina rashin mutuncin sa take, a tunaninta ai ko kowa bai tsiraba mahaifiyarsa ta tsira. “Mah-mah kuma shi ɗinne ya faɗa?”.

A karan farko Malikat Bushirat tai murmushin takaici. “Kar kiji ko tantama akan hakan Ibnati. Dan duk yanda kike tunaninsa ya wuce nan ɗin. A yanzu dai tunda ya nuna bai buƙatar ganin kowan bazai gani ɗin ba. Shiyyasa na kiraki nan dan kimin wani taimako na haɗani da shi ta waya”.

 

Yawu Iffah ta haɗiye muƙut, dan itama dai a karan kanta kwanaki huɗu kenan bata sanyashi a ido ba. Tayaya kuma zata haɗasu a waya. To wanda ma ya nuna kai tsaye bazai haɗu da ita matsayin mahaifiyarsa ba ita kuma ƴar karere taya zatai hakan?. Amma bara ta amsa mata kawai, dan koba komai itama tana buƙatar jin gaskiyar lamarin ai….

Har lokacin kwanciya barci Iffah bata samu wata makamar riƙewa na tunkarar Tajwar Eshaan ba. Hasalima bata da tabbacin a inda zata samesa. Tambayar hadimai kuma tamkar gazawace a gareta matsayinta na Zawjata-almilk. Kusan ƙarfe ɗayan dare tana tsaka da kai kawonta da faman jan tsaki saƙo ya shigo wayarta. Kamar zata share sai kuma ta ɗauka dan koba komai kullum a cikin tsumayen ji daga su Babiy take. Mamaki ya sata buɗe saƙon da hanzari ganin Malikat Bushirat.

_Ina alfahari da kasancewar ki tare da gudan jinina Ibnati. ALLAH yay miki albarka, yanda kika zama sanadin yaye damuwata kema ALLAH ya yaye miki taki yanzu na gama waya da shi_.

“What!!”.

Iffah ta faɗa cikin ɗan zabura tana sakin wayar akan carpet. To mi hakan ke nufi? Ita da batama gansa ba taya har yay kiran mahaifiyar tasa da har ta gamsu itace sanadi. “Anya mutumin nan kuwa ba ifiritin aljani bane?”. Ta faɗa a zahiri tana waige-waige a ɗakin da tunanin ko dai akwai camara, to inma camara ɗin ce itada sukai magana a sashen Malikat Bushirat ma ta ina camara ɗin zatai tasiri kenan…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button