Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 13

Sponsored links

Hakuri Sir bilal ya sake bawa Dad kaante tareda tabbatar masa da zasu dawo qarshen watan da yardar Allah harma da DD din idan Allah ya dorasa akanshi.

Cikin ‘yar damuwa Dad kaante din yayi sallam da Bilal ya fito yana fidda wayarsa dan kiran Sulaiman da hankalinsa yake kansa.

Motarsa ya nufa batareda ya nufi babban part dinsa ba dayake gefen mansion din iyayensa ba duk acikin guri daya.

Yana shiga motar ya rufe ya saka kiran Sulaiman wanda shima yake zaune yana jiran kiran maigidan nasa dan sake kora masa bayani.

Kiran Sir bilal din na shigowa wayarsa ya dauka da sauri yana sake gaishesa kafin ya sake masa bayanin komai na abinda ya fahimta.

Shiru Sir bilal din yayi kafin ya kashe wayar yana tinanin menene zai saka sumayyah kuka da damuwa har a hanya?

 

 

 

Tada motarsa yayi yana kallon time sbd yanada meeting da baqin masu mahimmanci ga DD yana buqatan nutsuwa yayi magana dashi ta waya Dan haka ya daure ya wuce office idan Yaso washe gari da wuri zai sameta school yaganta.

Washe gari Koda ya isa suna cikin exams dan haka ya zauna cikin motarsa yana jiranta.

Tsawon mintina talatin da shida yayi yana jira sai gata ta fito ta nufa inda suke zama yau din ma bata cikin kuzari sbd zuwa lokacin tagama saddaqar da masifar da zata shiga ta Ababa.

Kokarin zama takeyi qamshin tirarensa ya shiga hancinta ta dago da sauri tana ganinsa tayi saurin maida kanta qasa tareda zamewa ta durqusa ta gaidasa cikin tsananin girmamawa.

Yanayinta yake sake karanta yanason magana da ita amma sanin hankalinta bazai taba kwanciya ba sai yace ta biyosa kawai.

Kaman baiwarsa haka tabi bayansa kanta a qasa cikin nutsuwa.

Motarsa ya bude mata tashiga shima ya zagaya ya shiga tareda rufe motar yaja suka bar makarantar saida sukai tafiya mai dan nisa zuciyarta na bugawa

Inda babu mutane sosai yayi parking ba tareda ya kashe motarba sbd Ac ya juyo ya kalleta cikin nutsuwa ya sauke numfashi mai dumi tareda ajiyar zuciya kai tsaye yace

 

 

 

“Meyasa kiketa kuka yau sulaiman yace akwai matsalan dayake damunki,

Ko zan iya sani idan ba damuwa

Idanuwansa ya zuba mata yana jiran amsarta,

Shiru tayi bugun zuciyarta da rawar jikinta na bayyanuwa ga hannuwanta dake rawa.

Hannuwanta ya kalla yaga yanda suke rawa a hankali kafin ya maida idanuwansa kan fuskarta yana sake tabbatarda akwai matsalar dake damunta.

Jin hakan yasa gabanta mummunan faduwa sbd duk yanda suka kai ga kamewa da kiyayewa tareda taka tsantsan koyaushe da zuwa gidansu yake musu barazana yana taimakonsu dan kuwa duk abubuwan dayake musu saiya basu tsoro ya firgitasu da cewan zashi gidansu gurin babansu suke yarda su karba taimkonsa.

Bude baki tayi cikin sanyin jiki da damuwa ta sanar dashi bata gane komai na karatun da sukeyi ne har jarabawar.

Shiru yayi yanason fahimtar zancen nata da kyau sbd jin zancen yayi kaman kai tsaye da yawa dan haka ya sake kallanta da kulawa yace

“Karantarwar ne malaman basu iya ba basayin yanda zaku gane kokuwa?

Shiru tayi sbd muzantar datayi saidai kuma daman su din ba masu wata darajar da zasuce basu saba da muzantar ba dan haka a sanyaye tace

“Aa nice bana ganewa,kaina baya gane komau” da wasu irin hawayen kunya da muzantar kai ta qarasa zancen.

Ya fahimci abinda take nufi dan haka jikinsa yayi sanyi da tausayinta dakuma nauyin zancen dan kuwa a familynsa marasa ilimi zaune a kansu basa karbuwa a Kaantes saukin abin suna dubawa hardana Addini ba iya bokon kawai suke so daga matayensu ba.

Ahankali ya sake kallanta yana sake jera mata tambayar yanayin yanda tayi last session dinta da yaya results din suke.

Batada zabi bayan fada masa gaskiar bataci komaiba a bayan duka wannan semister din ma courses din datake carry over dinsu yafi wainda zatayi a semister din yawa.

Wayarsa ya dauka ya saka kiran wata number ta wata lecturer mace wanda tana dauka kai tsaye ta hau gaishesa.

Cikin mutuntawa ya amsa yana tambayarta aiki da dama da student ta amsa da duk lafiya kalau,

Cikin natsatsen turancinsa daya kama bakinsa kusanma fiyeda hausarsa sbd zamansu a qasashen turawa fiyeda nan din idan ba yanzu daya dawoba sbd su biyu ne ‘yaya maza a familyn kuma idan ba shi din ba DD bazai taba dawowa dan karban ragamar kula da huldodin kaantes ba.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button