Idon Naira 16
Babban masifar data sake rikita Zainab shine rashin farfadowar maryamah Dan haka suka kwasheta hankali tashe sai asibiti.
A asibitinma saida suka dauki lokaci kafin ta farfado cikin tsananin kuka da tashiin hankali Mai ban tausayi,
Zainab sai alokacin tasan waye ya rasu take itama jikinta ya sake daukan rawa da firgici sbd Bata kawo mutuwar a kansaba….
Shine abinda tahau maimaitawa tanajin tashin hankalinta na qaruwa da tausayin Aqeel daya zama maraya kamar ita duk da shi yanada sauran gatansa sosai.
Washe gari har aka gama haɗa gawar MUHAMMAD ASADULLAH bisa jagorancin ƴan uwansa da suka samu isowa tare da abokan arziƙinsa Maryamah na can gadon asibiti ita da umma data taso tun jiya ta iso gabanin asubar yau
Zainab Kuma Dole Takoma gida sbd gidan a hannunta yake matuqar masu gidan basa Nan gakuma Aqeel da zazzabinsa ya dawo Wanda kowa ya tabbatarda na rashin mahaifinsa ne da yayi.
An Gama komai maryamah da ake jira suka dawo daga asibiti ko tafiya da kanta Bata iyayi riqe ake da ita sbd mummanan jiri dake dibarta ga wata irin firgicewa datai a kwana dayan Dan kuwa bakinta Kansa ya bushe ko yawu daqyar take iya nemowa a bakinta ta hadiye
Dawowarta kuka ya dawo sabo acikin gidan dake cike sosai da mutane Yan uwan Asadullah din na nesa da kusa duk sun halarto cikin baqin ciki da alhinin wannan mummanan rashin daya samesu.
An yi masa sallah an kuma kaisa gidansa na gaskiya ya samu ɗinbin mutane da kyakkyawar sheda daga gurin mutane musamman malaman addini sunata yabonsa sbd mutum ne Mai tsananin son Addininsa.
Maryamah kuwa dai tana cikin matsanancin hali na ɗimuwa da firgicin babban rashin nagartaccen miji kuma uban ɗanta ƙwaya ɗaya jal
Addu’a kawai ake mata tana sha ana tofa mata sbd lamarin ya tabata sosai Dan kuwa daga baya har asibiti ake tunanin fara kaita idan ba harda kanta rasuwar ta taba ba.
Zainab kuwa wani babban al’amarine ya risketa na zaman karban gaisuwar Dan kuwa kusan a tsaitsaye tagama figewa tas Takoma kamar Yar qaramar fatalwa sbd wahala da nata tashin hankalin na rasuwar Wanda shine takewa kallon gatanta a gaba Amma shima ta rasashi Dan haka kukanma kasawa tayi sbd nauyi da dacin da zuciyarta take dabaibaye dashi koina,
Abincin datake dafawa na zaman yafi qarfin duk wani kokari da iya wahalarta Dan kuwa duk masu taimakawa gurin aikin ba wani aikin arziki sukeyiba kusan duk itace qarfin aikin aikuwa take cikin kwanaki qalilan ta fice hayyacinta
Ga kula da Aqeel Wanda shima jikin yakeji Kuma yaqi aminta da kowa ya kula dashi sai ita Dan haka duk tabi ta qarasa haukacewa gwanin tausayi.
Haka aka gama kwanakin zaman karban gaisuwar har rasuwar tayi sati biyar kusan koyaushe basa rasa Yan zuwa gaisuwar.
Kwanakin da suka biyo bayan rasuwar Alh Asad sun kasance kwanaki mafiya ƙunci da soya zuciya a wajen Maryamah da ma duk wani me ƙaunarta don ta yi kwanakin ne cikin tsananin ruɗani da ficewar hayyaci sabida bada wasa ba soyayyar mijinta ta gama rarike zuciyarta baki ɗaya gashi Aqeel danta datake kallon Asad acikin Sam yakasa rabarta kokuma kaunarta yanda yake kaunar wadda renonsa kawai takeyi duk sai tasake susucewa Takoma kamar wata bebiya ko yawan magana bataso kullum shiru take batason hayaniya.
A hankali kwanaki sukai ta shurawa suna bada watanni cikin aminci da yardar Ubangiji Maryamah ta gama takaba
A hankali aka fara tattara duk wasu kadarori da marigayin ya mallaka kama daga kan kamfanoni da gidaje zuwa zunzurutun kuɗaɗe da ya tara aka raba gadonsa Wanda kusan ‘dansa Aqeel shine da mafi yawan gadonsa sai mahaifiyar Alh Asad din da matarsa maryamah sai ya kasance kusan komai na tarin dukiyarsa Mai yawa a hannun maryamah yaje Dan kuwa itama sai dataji tsoron dukiyar da ‘dan ya gada harma da nata Jason
Hakan ya sanya wasu daga cikin ƴan uwansa suka fara jin haushin Maryamah din musammam dasuka nuna zasu karba Aqeel din su rikesa Tunda ita Cameroon zata koma gurin mahaifiyarta…
Babban rikici tayi da Yan uwan nasa akan ‘danta Aqeel Wanda qarshe ta yanke shawarar Babu inda zata tafi zata zauna ta tarbiyantar da ‘dan takuma kula da dukiyarsa.
Da wannan aka kashe zancen Wanda kusan har kotu ake Dan kawai suna son karbe yaron.
Sun saka Mata ido sosai tareda sharadin idan ta almubanzarar da dukiyarsa da tarbiyarsa zasu karbesa har abada bazasu Bata Shiba.