Hausa Novels and Stories

Furar Danko Page 9 Hausa Novel

Sponsored links

Duk da haka yakan ɗan gwada yin ƙwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ƙasa ma, ya fara neman aiki amma yaƙi samuwa duk da takardunsa sunyi ƙyau matuƙa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ɗaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaƙanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ɗaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ƙwallon ƙafa ya ajiye gefe ya shiga ƙoƙarin sana’a, sai dai anan ɗin ma dai komai yaƙi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ƙanƙanin lokaci al’amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ƙoƙarin kamo can idan nan taƙi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu ƴan uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika’il Idris Mawashi huɗu ne cif, hakama ƴaƴa su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da ƴammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu………

Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko’ina mulmule yake da suminti. BQ ɗin yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki

 

iyayensu mata, baya can ƙarshe sashen mahaifinsu Malam Mika’il Idris Mawashi. Sam baya buƙatar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki ɗakinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran ƙanensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a ɗakinsa. Dan a yanzu haka akwaima ƙanan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya kula ƴar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faɗan har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har ƙwallar ɓacin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ƙwaƙwƙwarar sana’a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, ba ɗaukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taɗe rayuwarsa haka. Duk inda ɗa nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini. Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko’a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button