Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 11-12

Sponsored links

Mikewa yayi tsaye da sauri Kamar Cele zata Masa fyade Yana furta Haram…Haram Hajja,da Hausa tace Kai ka kasan wani haram can da yawarka,tsaye ta mike ya fisge zai fece ta shatilo kafafunsa ya fadi a kasa,Ahsan shi da kanshi sai da yayi dariya yana Namiji mace ta kayar da shi har kasa, Cele Yar ta kife komawa tayi ta cakume shi har gashinsa take shinshinawa sai kace mayya sabo da shinshinar kamshi Kawai ta takurawa bawan Allah,karfi ne bai sa ba Yana lallaba cikinta shi bai iya fada bama,cele harda uban nishi na gajiya tana Maganar Yan daba tane cewa yawa kake fa Baabaa kana yawa dalla ka tsaya Kamar wani dan iska ni ba fyade Zan maka ba kamshi kawai tana tura hancinta wuyansa,kyaleta yayi sabo da cikin da yake jikinta,ji tayi ana motsi a cikinta ta mike tsaye zumbur ta dage iya karfinta ta durmawa cikinta duka tace micijin ciki ne ta rasa me zata kira sunan miciji da Larabci Kamar zata yi kuka tace shi yasa nake da ci yanzu ashe micijin ciki ne da ni wayyo ya sake yin zullo ta dage rigarta sama,da hannu Ahsan ya tambayeta mene ne? ta rasa me zata ce cikinta ta nuna tace Sirasil wai kyankyaso ne a cikinta tunda bata san sunan miciji ba da ya yarensu, Laptop dinsa ya jawo ya koma kujera ya zauna tare da dora system din a cinyarsa ya kirata tare da nuna Mata gefensa ta zauna,da zancen kurame yace ta kalla ya kamo pics din mace me ciki a fili ga jajiririn nan ana gani a waje irin na littafin likitoci ya nuna hoton ya nuna cikin Cele da yatsa yace irin wannan ne fa a cikinta,Cele da sauri ta Bude baki tace Iskanci nayi da ubanwa nayi Iskanci da Zan samu cikin ni ko kirji na ba a taba tabawa ba Ina Zan samu ciki kaji balarabe yo a Oat na Sha? Ko a cikin shayi nasha,Yana kallonta tana ta surutu,laptop din ta karba dai dai wajen Google ta rubuta miciji da hausa sai ga pics din miciji ta kalli katuwar messa anaconda tace itace a cikinta,Ahsan ya dinga dariya ya zaci ta sani tsokanarsa ta ke Yi,Kansa ya nuna da yatsa ya furta sunan Maheerah matarsa sannan ya kamo Mata pics din jariri ya nuna Mata cikinta Wai shine a cikin cikinta,Cele tace wannan baya ganewa, sake karbar System din tayi ta rubuta wakar Kawu Dan Sarki ingallo sai ga waka,Cele tana ji har da kada kai ita bata rawa, Ahsan ya tsura Mata Ido tana ta bin wakar gata video shima Yana kallo sai dariya yake yana kallon wakar, Da zancen kurame yace tayi irinta ya gani,Cele tace sai da ya tashi su gwada tare, da sauri yace lah,wata wakar ta canja harda zabura tayi wani uban tafi tana rawa a zaune harda dafa kai tare da tamke baki irin shegiyar nan.

Juyowa tayi suka hada Ido gabanta ya fadi gaskiya Ahsan karshe ne a kyau ta ko Ina ya hadu ba karya a hankali tace kasan ka hadu,kyakyawa ne Kai,Zan iya lasheka na cinyeka danye, da zan sameka wannan da nayi yanga a Nigeria da Zan sameka to ai da nayi fanka,fari tayi masa da Ido da sauri ya dauke Kansa Kar ya kalli Haram wai, Ahsan ta furta ya juyo a nutse Kamar abin kirki wani fari ta sake Masa harda kashe Masa Ido daya,mikewa yayi Yana cewa Subhannallah Subhannallah,dariya tayi ganin yanda yake gaggawar barin gidan gaba daya kamar Yana Jin me nake furtawa da yarena.

 

 

Maheerah yaje ya dakko a hospital parking yayi a hospital din Yana tafiya a hankali likitoci suna ta zirga zirga,asibiti ne hadadden gaske,lift ya shiga zuwa Office dinta Yana kaishi Hawa na shida ya fito tare da takawa har Office dinta ya manta bai Mata knocking ba Kawai ya murda handle a hankali ya shiga gaba daya,daskarewa yayi a tsaye ganin Maheerah da katon balarabe tsohon zaurayinta Hussain shima likita ne suna kissing juna yana murza Mata Boobs da harshen larabci yaji tana cewa ya akayi har yanzu ban samu ciki bane mijina ya kasa bani ciki kaima Naga matarka tana haihuwa ai amma ya akayi ka kasa,Likitan Hussain yace ai ke matsalar a kene baza ki haihu ba mahaifarki baza ta iya daukan ciki ba kin sani kema, Maheerah rungume shi ta sake yi tace zamu ci gaba da Jin dadin mu ko Zan samu na dace mahaifata ta dauka,Ina son mijina sosai amma mijina ya min kadan,Ahsan a hankali ya juya da baya ba tare da sun kula ba,Fitowa yayi tare da fadawa motarsa ya zauna a ciki ya dafe Kansa bai San Sanda ya Fara hawaye ba sabo da bakin ciki da bacin rai dama su kishi Kamar hauka,sai da ya gaji sannan yayi Addua a motar ya goge hawayensa ya Dan huta Kamar ma baiyi kuka ba,waya ya dauka ya kira Maheerah sai da ya kirata sau uku sannan ta daga tare da harshen larabci ta furta masoyina kazo gani nan Wayar ta kashe ta sake yiwa Hussain kiss sannan da kyar Suka rabu ta fito,Ahsan Idonsa ya runtse nan take idonsa yayi ja Kansa ya fara masa ciwo sabo da tsananin bacin rai,abinda yake tunawa yasan Maheerah ce da matsala mahaifarta baza ta iya rike da ba amma ya hakura ya biye Mata Suka Yi dashen ciki gashi taci amanarsa ashe ta ma dade tana cin Amanarsa.

Motar ta shigo a hankali ta kalle shi cike da nishadi da kulawa ta shafa gemunsa tare da tambaya noorul qalb me ya faru lafiya? tana tambaya da larabci,Kai kawai ya girgiza Mata yace Kansa ke ciwo Kuma ya Sha magani tace Sannu Allah ya baka lafiya tana gyara nikaf Kamar mutuniyar kirki.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button