Furar Danko Page 5 Hausa Novel
Da sauri MM Atik ya nufi tasa motar yana sanarma bodyguard ɗin sa su bisu. Wani saurayi dake jingine jikin motarsa da ke kusa da su MM Atik ɗin ya dubesa. Komai a
gabansa ya faru, dan haka yay murmushi da duban MM Atik ɗin. “Ranka ya daɗe Bama sai ka wahal da kanka ba indai sanin gidan su Lulu ƙamshi ce. Sai dai zan baka shawara karka wahal da kanka dan ba lallai ka samu yanda kake so ɗin ba. Kamarka ma ɗan manya daya fito a gidan mutunci ka wuce da ajin wadda ta gama zama gawurtacciyar karuwar turawa tun tana mitsitsiyarta”.
Ƙaramin murmushi MM Atik Kumo yayi, ya matso kusa da saurayin yana mai girgiza kansa. “Abokina karka damu da son nuna min abinda na gani da idona. Kai dai kawai faɗamin inda zan sametan tunda har ka mata irin wannan sanin haka”.
Cikin rashin damuwa saurayin ya faɗa masa cikakken adireshin gidan su Lulu ƙamshi. Sosai ya masa godiya ya shige motar da aka buɗe masa fuskarsa ƙawace da murmushi……
_Manseer M Atik Kumo_* kenan. Ɗa na farko a wajen Hon. Mustapha Atik Kumo. Babban ɗan siyasar nan kuma tsohon gwamnan Kano da ya sauka, a yanzu haka kuma yana ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na wannan zangon da ake kan fara campaign. Sannan shi a karan kansa ma matashin ɗan kasuwa ne da kuɗi ke kaɗa masa gangar lokaci. MM Atik Kumo shegen kansa ne shima a wajen rashin jin magana. Dan duk wani mahaɗar marasa ji na ƴaƴan manyar ƙasar sune ɓoyayyun limamai. Manemin mata ne ƙwararren gaske, dan duk yanda mace takai da iya kame kanta sun san yanda zasu kutsa kai cikin mutuncinta har saita koma jin maganarsu fiye data iyayenta. Mahaifinsa mutumin kirki ne dattijon arziƙi abin alfahari, dan haka yake taka tsantsan akan iya shegensa ba ko’ina yake yarda ya nuna halinsa mara ƙyau ba, idan ma akace maka yana aikata wani abu makamancin hakan zaka iya ƙaryatawa dan ya iya takunsa sosai sosai
Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi ɗin yay horn kamar yanda ta umarcesa. Leƙowa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi ɗin wulaƙanci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Ko gama parking mai taxi ɗin baiyi da ƙyau ba ta ɓalle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaɗa. Abinda zai baka mamaki ko rawa ƙafarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin ƙafarta mai shegen tsini. Duk wani ma’aikaci dake gidan da ga kallo ɗaya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buɗaɗɗen abune ga duk wani ma’aikaci na gidan. Duk tsufarka duk ƙanƙantarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a ƙanƙanin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi ƙoƙarin mata a yanda ta buƙata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daɗi kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen ƙanin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu’a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu’ar tasu bata amsu ba😂 dan gata ta dawo ɗin a bazata.