Latest Updates

Furar Danko Page 11 Hausa Novel

Sponsored links

“Ammah barka da yamma”.

Ya faɗa cikin muryarsa mai sauƙin amo da rashin son hayaniya. Maimakon amsa masa gaisuwar tambaya ta jeho masa cikin nutsuwarta da cikar kamala. Dan da yawan halayensa ya samosu da ga gareta ne, duk da ya ɗakko wasu da yawa ga mahaifinsu ma.

“Baka da lafiya ne?”.

Gajeren murmushi yayi da ɗan girgiza kansa. “Lafiya lau nake Ammah, na ɗan yi barci ne”.

“Shima wannan aikin an samu matsala kenan? Ya rabba..”

Ta ƙarashe faɗa a hankali cikin damuwa. Gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, murya a sarƙe ya ce, “Amma ba matsala aka samu ba karki saka damuwa a ranki. Na dawo da wuri ne dai”.

Shiru tai tana kallonsa, sai dai har cikin ranta bata gamsu da maganar tasa ba. Ta sanshi fiye da yunwar cikinta akan zurfin ciki, sannan kuma bai iya ƙarya ba, ko yaya ya kuskure takan saurin harbosa. Tunda ya fara aikin ko ƙarfe biyar na yamma baya dawowa balle yanzu da azhar, alamuma sun nuna tun ɗazun yake a gidan tunda gashi yace har barci ma yayi. Fitowar ƙannensa biyu ƴammata Maryam da Asma’u masu kama da shi sosai kamar mahaifiyarsu ya katse shirun falon. Ƴammata ne ƙyawawa masu tarin nutsuwa da rashin son hayaniya suma. Suma dai ɗan turus sukai na ganin nasa. Sai kuma cikin damuwa duk suka kalli mahaifiyar tasu. Ɗauke kanta tai, dan gaba ɗaya rauninsu da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu.

“Yayamu ina yini”

Suka haɗa baki wajen faɗa a sanyaye. Kansa ya jinjina da amsawa cike da kulawa, duk ba wani yana wasa dasu bane ko sakewa yana ƙaunar ƙanensa, sannan suna bashi tausayi da ya gagara tsayawa akan al’amuran su na yau da kullum a matsayinsa na babba namiji a ɗakinsu tunda mahaifinsu abubuwa sun masa yawa yanzu, ga shekaru ga rashin tausayinsa da ga ƴaƴan gidan da kowa ya samu ya tsallake da ga shi sai iyalansa sai uwarsa ne..

“Babu wata damuwa ko?”.

Kai suka jinjina masa alamar babu duk da sunada buƙatu, sai dai sun san koma sun faɗa tayar masa da hankali kawai zasuyi tunda bashi da shi. Abincin da akai gidan kason ɗakinsu da aka kawo suka zuba masa, tuwon shinkafa ne da miyar ganye dai-dai ƙarfin talaka mai rufin asiri. Ya jima yana kallon tuwon bayan fitar su Asma’u har sai da Ammah tai masa magana sannan ya fara ci dan yunwa yake ji sosai, yau baya jin ko karin kummalo ma yayi, sai ruwan shayi da ya zame masa jiki ko yaushe bai rabo da shi a flaks da ya sha……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button