Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 60

Sponsored links

Suna fitowa da ga lift ɗin ɓoyayyar hanyar da zata fiddasu batare da ko hadiman ƙasan sungansu ba ya nufa, amintaccensa biye da shi. A wani ƙaton fili suka fito, an gyara wajen da wani irin farin yashi mai matuƙar ɗaukar idon mai kallo da birgewa. Kasancewar ruwan saman da aka sha sai wajen ya sake bada wani yanayi mai matuƙar daɗi ga sassanyar iskar da bishiyoyin da aka ƙawata wajen na dabino na bayarwa. Da ga ɗan nesa da su Sarkin barga ke riƙe da ƙyaƙyƙyawan farin dokin da shi da kansa ya raɗa ma abinsa suna da ƙyautar ALLAH. Kamar yanda ɗabi’ar dokin take suna fitowa yay wata irin haniniya da girgiza kai kace ƙamshin Tajwar Eshaan ɗin yake ji ya shaida kasancewar sa a waje. Da wani irin gudun bajinta ya nufosu, yana isowa gabansa yay wata irin ƙwafutar ƙasa yay girgiza da haniniya, har gashin saman kansa zuwa wuya na wani tarwatsewa da haɗe kansa waje guda. A hankali Tajwar Eshaan ya lumshe idanunsa yana sakin sassanyan murmushi da mutane kan jima basu gani tare da shi ba sannan ya kai hannu ya shafi fuskar dokin yana masa magana ƙasa-ƙasa da ko Sarkin barga da amintaccen hadiminsa dake tsaye gefe kawuna a risine basa iya jinsa. Cikin wani irin salon da ke tabbatar da ƙwarewarsa a iya sarrafa dokin ya damƙi linzamin sa cikin action mai matuƙar ɗaukar hankali da bajinta ya ɗane saman sa. Cikin tabbatar da ƙwarewar da dokin ya samu a hanunsa yay wata irin haniniya da ƙwafutar ƙasa ya ɗiba hanya tamkar a filin polo. Rere suka fara ɗan gaske da sauran dokunan huɗu da aka sakakarma linzami batare da kowa a kansu ba. Duk wanda ya ga yanda yake sarrafa dokin basai an faɗaba ya san shi ɗin ƙwarren ɗan wasan polo ne kuma jarumin gaske. Dan cikin ƙanƙanin lokaci yay ma sauran dokunan da babu kowa ɗin fintinkau, har ya sake dawowa ya koma sannan su suka iso. Kaida gani kasan yana nishaɗi da wasan matuƙa. Sosai su sarkin barga ke murmushi da jinjina jarumta irin ta gwarzon Sarkin nasu. Ko’a cikin dubu shi ɗin na dabanne da kai tsaye za’a nuna a shaida. Dan suna da tabbacin da a lokacin yaƙi ne yazo babu abinda zai hana ya zama babban jarumin da tararsa a filin daga abin tsoro ne. Ya ɗauka tsahon lokaci yana wasan dokin har sai da yaji ya gamsu jininsa ya tashi fiye ma da yanda yake buƙata sannan yaja linzamin dokin ya dire bisa ƙasa cike da bajinta yana sauke numfashi ɗaya-ɗaya. Da sauri amintaccensa ya matsa garesa hannunsa ɗauke da ƙyaƙyƙyawan tray mai ɗauke da gorar ruwa da glass cup. Goran ruwan ya ɗauka batare da ya haɗa da cup ɗin ba, ya ɓalle murfin ya kai bakinsa. Yasha kusan fin rabi sannan ya juyo ya juye sauran akan fuskar dokin nasa yana ɗan murmushi. Haniniya dokin yayi mai nuni da isharar jin daɗin kasancewarsa da adalin ubangidan nasa. Shima sai ya kai hannu ya share masa ruwan yana murmushi. Ƙaramin towel Sarkin barga ya miƙo masa da sauri, bai musaba ya amsa ya goge hannunsa da wuyansa sannan ya kai shi ga fuskar dokin shima ya share masa ruwan da ƙyau. Yanda yake ma dokin da kansa dolene ka tabbatar akwai matuƙar shaƙuwa a tsakaninsu mai birgewa da ƙayatarwa. (Ko dabba ma ta san me bata kulawa da nuna ƙauna kenan☺️😘)

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button