Daudar Gora Book 2 Page 90
A’a Ibnati daure kinji, idan kika sha madaran nan kikaci wannan naman sai na ƙarasa miki ɗayan alluran ki kwanta barci har sai sanda kukaso tashi kinji. Bakiji jikinki yayi zafi ba sosai. Haba ɗiyar albarka haihuwar alkairi”.
Da wannan lallaɓawar Iffah ta fara shan madarar a hankali, Daneen Ammarah na bata farfesun da kanta cike da kulawa. A haka Tajwar Eshaan ya shigo ɗakin da sallama ya samesu. A cikin kwalliya ya ke tsaf ta alfarma ga uban ƙamshinsa da ya cika ko’ina na ɗakin, a taƙaice dai a Shahan-shan ɗin sa yake. Cikin dakewar nan tasa mai ɓoye duk wani sirrin zuciyarsa da ainahinsa yake. Idanunsa sakaye da eyeglasses. Ya wani ƙara ƙyau da cikar kamala ga wani kwarjini mai ƙara yalwata haibarsa ga mai kallo. Daka gansa kasan shi ɗinne dai ɗaya tilo Shahan-shan ɗin ƙasar ruman mai rumawa da ƙasar ruman. Sai wani shining yake da ke tabbatar da yau ɗin ranarsa ce ta musamman mai ɗunbin daraja da tarihin da bazai taɓa goguwa a garesa ba.
Tun a kallo ɗaya da Iffah tai masa lokacin da yake sallamar shigowa ƙasa-ƙasa bata sake gigin hakan ba. Daneen Ammarah ma dai da ga kallo ɗaya bata sake wani ba, dan gaba ɗaya kwarjininsa ya cika ɗakin, ga wani kunyarsa da ke ɗawainiya da ita kamar itace ta aikata tsiyar ba shi ba. Koda yake shima ɗin dai ji yake Mamyn nasa a yau ta musamman ce a garesa, dan kasancewar ta a sashen nema ya sashi jin gara ya fita zuwa fada, sai kuma ga kira ya samu da ga Malikat Haseenat bayan fitowarsa Gym an wayi gari Ammien sa babu lafiya, yana shirin fitowar nan ma Jasrah tai kiran shi itama tana kuka dan tun ɗazun take kiransa ba’a ɗaga ba.
Cike da dakewa ya sake gaida Daneen Ammarah idanunsa kan Iffah da ke kai kofin madara bakinta tana sha kaɗan-kaɗan. Miƙewa Daneen Ammarah tai cikin hikima ta ce ta cigaba da shan madarar da nama bara ta amso saƙon sauran magungunan ta data bada a siyo….
Shiru ɗakin ya ɗauka sai sassanyan ƙamshin da ya gaurayesa ke tashi. Taƙi yarda ta kallesa koda da kuskure duk da yanda take jin ɗakin yay mata tsukuku saboda kasancewar sa. Idanu ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kanta sannan ya ɗan taka gaban gadon gab, zaune ya kai inda Daneen Ammarah ta tashi a gefen gadon kusa da ita sosai. Sai kuma ya kai hannu ya zare eyeglasses ɗin da ya sakaya launin idanunsa.
“Good morning Mrs Eshaan Qutb”.
Ya faɗa da wata irin shaƙaƙƙiyar murya mai sanyi matuƙa yana kai yatsunsa biyu kan haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau. Har tsakkiyar kai muryar da yay amfani da itan ta ratsa Iffah, ga wata matsananciyar kunya da shakkarsa da ke ratsata. Idanun ta da hawaye ke cikosu ta lumshe da sauri.
“Please open your eyes my life”. Ya faɗa fuskarsa gab-gab da ita batare data san lokacin da ya matsota haka ba