Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 79

Sponsored links

Zuwa yanzu tako ina maganar tsallakewar Iffah ce ke kaikawo a cikin masarautar. Kowa ya nutsu wajen tattauna abinda ke bakinsa da abokin maganarsa. Wasu jin daɗine game da hakan, wasu ko baƙin cikine a ransu, dan mutuwar Zawjata-almilk ɗin kamar wani makamine a hannayensu na dukan nasarar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ɗin. Tsallakewar Iffah kuma zai kasance kamar damar ƙalubalantarsa da suka riƙe ya kuɓuce musu kenan. Ita kuma yarinyar kimarta da nunawa duniya tafi ƙarfin masu ƙarfin zai yi tasiri a zukatan jama’a…..

★Komai dake faruwa yana isa da shiga a kunnen manyan masu faɗa aji ta bangaren iko da kusanci da Tajwar Eshaan ɗin. Wato Malikat Haseenat da Malikat Bushirat. Sai dai sunyi biris babu alamar zasu tofa nasu akan hakan bayan bayyanar farin cikinsu akan fuskokinsu daya gaza boyuwa ga kowa. Dan a dalilin wannan al’amari Malikat Bushirat har ƴafiya tayi ga wasu firsinoni dake a cikin kurkukun masarautar akan wasu laifuka nasu da basu kai sun kawo ba. A cikin sunne kuma aka sallami harda Diwa a dalilin bincike daya tabbatar da bata da hannu game da abinda ya faru ga Iffah a waccan ranar.

★A ɓangaren Malikat Haseenat kuwa maimakon bama abinda ke zuwama kunenta muhimmanci hankalinta ta maida wajen tantance hadiman da zasu koma aiki a karkashin Iffah ne bisa taimakon Daneen Ammarah da farin cikinta itama yake a bayyane. Dan itama dai har kyaututtuka na musamman yau ta bada ga hadimai tare da sakawa a tattaro mata dukkan malaman masarautar zuwa sashen Iffah da bukatar suyi saukar Alkur’ani mai girma. Ta kuma miƙe da karfin jikinta wajen shirya lunch na musamman ga Tajwar Eshaan da amarya Iffah Zawjata-almilk…

Abubuwan da suka faru sun sakashi dakatawa a zahirance bisa shawarar Kaka. Sai dai yana cigaba da gudanar da wani binciken sirri dan yayma kansa alƙawarin binciko duk mai hannu akan wannan al’amarin nasu Babiy da ma inda aka ɓoye su.

 

Kamar yau ma tun jijjifin safiya ya fito daga gida. Kai tsaye hanyar jihar Hubab ya nufa inda bincikensa ya tabbatar masa nanne ainahin jihar da matar Abu Moosa ta fito. Jihar Hubab makwafciyar Dahab city ce (Daular ruman kenan) dan haka a cikin ƙanƙanin lokaci ya isa. Bai tsaya sanyaba ya ɗauka hanyar ainahin kauyensu kuma. Kasancewar anan ma hanyace shimfidaɗɗiya a kanƙanin lokaci ya isa. Da farko ya sha wahalar binciken inda gidansu yake, sai da yay dabarar nuna hotonta sannan.

 

 

 

Kusan mintuna goma bayan isar da saƙon tanada baƙo gareta ta fito cikin irin shigarsu. Tayi ɗan tsamm alamar shan jinin jikinta kafin ta ƙaraso a yanayin son basarwa. Barrister shi ya fara gaidata, tare da sanar mata sunansa. Lokaci ɗaya ruɗani ya bayyana akan fuskarta ta shiga waige-waige irin na rashin gaskiya da ƙoƙarin ja baya daga garesa…

 

“Bawan ALLAH ina baka shawara ka taimaki kanka ka bar ƙauyen nan, babu wani abu da zaka iya ji a gareni dan ban san komai ba”.a

A fusace Barrister yay tsalle gabanta yana huci. “Baki san komai ba amma akaje da ke har gida aka kamasu. Karki sha mamakin bayan sanin inda kike har wasu abubuwa na sani a kanki Mss Farishta. Rashin bani haɗin kai kuma na nufin na tonasu kowa yasan ke ɗin wacece har ma da dalilin auren Dawood, sani kankine wannan babban koma baya ne a gareki kuma harma da zuri’arki”.

Yayu ta haɗiya masu kauri tana kallon Barrister, sai kuma ta sake wawwaigawa tabbacin dai akwai abinda take shakka. “Naji Barrister zan baka dukkan bayanan da kake buƙata, amma ina roƙonka kabar wajen nan, idan ma zai yuwu kauyen nan gaba ɗaya nake son ka bari. Wlhy na maka alkawarin zan zo na sameka na kuma faɗa maka komai da kake buƙata harma wanda baka sani ba”.

“Miyasa bazan sani ba a yanzu?”.

Tafiya yake zuciyarsa na faman masa kaikawo akan haɗuwar tasa da Farishta (matar Abu Moosa datazo har gida da ƴan sanda aka kama su Babiy. ALLAH yasa kun gane🥱). Duk da yasan zata iya ƙin aikata abinda ta faɗa na haɗuwar tasu a garin Jimna ya zaɓi barinta su haɗun can bisa lumana. A cikin Hubab ya tsaya yaci abinci tare da sallar azhar. Ya fito masallaci idanunsa suka sake sauka akan wata mota da tun fitowarsa ƙauyen su Farishta ya lura da ita tana biye da shi, sai dai duk da ya ganta suna tafiya kafaɗa da kafaɗa bai kawo komai a zuciyarsa ba. Janyewa yay cike da rashin bama abin muhimmanci ya shige motarsa da zummar zai cigaba da tafiya kawai yaga an zagaye motarsa da bindigu…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button