Daudar Gora Book 2 Page 86
…….Sai da ya tabbatar ta samu isasshen gashi sannan ya taimaka mata tayi wanka, har lokacin bata daina hawaye ba. Idan kuma ya ɗan motsata da ƙarfi ko yaya ne sai ta saki siririyar ƙara da ƙara ƙarfin kukanta. Babu abinda ya ke iya jera mata sai kalmar “Sorry, I am sorry”. Bai san tunzura mata zuciya
kalmar haƙurin nan take sake yi ba. Koda ya saka mata bathrobe shima sai da ya cire kayan jikinsa dan duk sun jiƙe. Yanzu ma cak ya ɗagota zuwa ɗaƙi, ganin lokacin salla ya ƙwace da yawa ya ɗakko mata rigar jallabiyarsa ya saka mata, veil ɗin ta na jiya ya naɗa mata sannan ya saka mata sallaya ya sake ɗakkota da ga kan sofar da take kwance ya ajiye kan sallayar. Ta kasa tsaiwa yanda ya kamata tsabar yanda ƙafafunta kansu sukai mata tsami, sai da ya dinga lallaɓata sannan tai dauriya da ƙyar, lokacin da take kaiwa ruku’u da sujida yana jin yanda kukanta ke ƙara ƙarfi alamar a wahalce take, zaman tahiya kam ta kasa zama da ƙyau. Duk sai hankalinsa ya ƙara tashi, dan ya fahimci lallai akwai matsala. Tana yin sallama ta zame kwance tana rusar kuka da kiran Ummu ta zo ta taimaketa. A gabanta yazo ya durƙuso tare da kamota jikinsa, yanda ya motsatan yasa ta ƙanƙamesa sosai.
Har zabura take tana girgiza masa kai wani sabon kuka na taso mata, amma sai tai saurin danne bakinta da hannayenta duka biyu tana ƙoƙarin haɗiyewa. Tausayi ta bashi da dariya, amma sai ya dake abinsa yana yi a cikin rai. Dan da gaske badan kar ya kashe musu yarinya ba babu abinda zai hanashi sake kai mata ziyara. Shi kaɗai yasan mi yake yaƙin dannewa da ga safiya zuwa yanzu, kawai dai abar kaza cikin gashinta. Ɗan kwantar da ita yay da ga zaman karkacewar da tayi, ya miƙe ya ɗauko ɗaya da ga cikin wayoyinsa. Gabanta ya sake zuwa ya dirƙusa ɗin dai maimakon zama da ya saba yi, ita inba a gaban UBANGIJINSA ba yayin bauta masa bata taɓa ganinsa durƙushe haka gaban wani ba. Duk da bawai yayi wani durƙuso bane na ƙasƙanci. Hasalima yanda yay ɗin sai ya ƙawatar irin masoyi a gaban masoyiyyarsa ɗin nan da suke cikin tsananin shauƙi ma juna. Contact ɗinsa ya shiga sannan ya miƙa mata wayar. Karɓa tai tana sake kumbura fuskar nan da tai jazur duk a suntume musamman idanunta. Kalmarsa ta zai ƙara ne ya sata danne hawayen tilas badan ta gaji da kukan ba. Number Mammy ta lalubo, taja wasu sakkani kamar mai tunani ko tsoron kiran sannan tai dialing. Bugu biyu zuwa na uku kuwa aka ɗaga. Da sauri ta rumtse idanunta hawayen da take riƙewa na ɓulɓulowa. Da ga can jin anyi shiru Malikat Haseenat da ta ɗauka wayar kasancewar Daneen Ammarah ta shiga wajenta sanar mata Malikat Bushirat babu lafiya tace ta haɗa mata ruwan wanka shine ta bar wayar gefenta, ita kuma ganin number Tajwar Eshaan yasa ta ɗauka da tunanin ko shima zancen Malikat Bushirat ɗin ne. Amma sai kuma taji anyi shiru ga kuma kamar ana jan ajiyar zuciyar kuka da ake ƙoƙarin dannewa yana son fita.
Ta faɗa a nutse cike da dattakonta. Kamar an ƙwalama Iffah farantin silver saman kai da sauri ta ɗauke wayar a kunnenta ta miƙa masa kukan da take dannewa na kufce mata. Bashi da zaɓin amsar wayar shi ya kai nasa kunnen, tunda har aka riga aka ɗaga bashi da hurumin cewa zai yanke sai ya sakata a tashin hankali. Wayar ya kai kunnensa yana mikewa da yin sallama cikin sassanyar muryar nan tasa mai cike da nutsuwa da kame kai. Malikat Haseenat ta lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya ta amsa masa. Cikin mamaki yace, “Jaddah ke ce? Ina Mammyn?”.
“Tana haɗamin ruwan wanka ne. Ina fatan lafiya dai ko naji kamar ana kuka da farko?”.
Ji yay duk yama kasa cewa komai, a karo na farko na rayuwarsa yaji yana jin nauyin kakar tasa. Amma sai ya daure da ƙyar acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Fhareedah ce Jaddah. Dama muna buƙatar Mammyn ne anan”.
Malikat Haseenat tsohuwar ƙwarai mai ran ƙarfe da cikar kamala. Sai kawai ta saki murmushi batare da ta nuna ma ta fahimcesa ba tace, “Oh to bara ta fito sai a sanar mata”.
“Uhum”.
Ya faɗa ciki-ciki. Bata sake cewa komai ba itama ta yanke wayar… Nannauyan numfashi ya sauke yana ɗan murza goshinsa. Sai kuma ya kalli Iffah da ta rufe idanu hawaye na cigaba da tsiyaya. Shi kam yama rasa gane kan wannan kuka, amma ya fahimci harda shagwaɓa da ragwantakar tsiya sai shegen tsiwa bakinta babu mai iya kadata a zance. Amma gashi a ɗan tabatan da yay da bai wuce ko ƙwayar zarra da ga abinda ke tattare da shi ba ya sauke take wannan rakin. Lallai ashe akwai aiki gabansa dan ba’a fara komai ba wannan sharar gona ce. (🚴🚴Taɓɗi).