Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 87

Sponsored links

Tashi yay ya yaye bedsheet ɗin gadon dan yayi ma kansa alkawarin gyara sirrinsa da kansa. Gudun karma ya barsu a gani closed dinsa ya wuce da su ya adana. Sai kuma yama ga su bar ɗakin kawai, dan haka ya zo ya ɗauketa zuwa ɗakin kusa da wannan ɗin ya rufe wannan…

Cikin abinda baifi mintuna goma ba sai ga kira da ga amintaccensa. Bayan gaisuwa da yay masa cike da tsantsar girmamawa ya nema wa su Daneen Ammarah iso. Duk da yaji mamakin jin kamar su biyu ake nufi kai tsaye ya bada umarnin ya shigo da su room 3. Karo na farko kenan bayan ita da ke matsayin matarsa da wani zai shigo jerin bedrooms ɗin sa na saman nan gaba ɗaya. Dan ko su matansa da duk aka kawo nan suka rasa ransu a hawa na huɗu ake ajiyesu. Iffah ce ta farko da ta taɓa hawowa hawan ƙarshen nan.

Ba shi kawai ba, hatta da Iffah da tayo gayyar sai da ta daburce da jin sautin muryar Malikat Haseenat na sallama. Amma jarumin naku sai yay ɗam da fuska daɗa duniya bai aikata komai ba babu alamar ko gezau tattare da shi. Sai dai kasancewar sa mutum mai tsananin kunya sai ya kasa yarda ya haɗa ido da Malikat Haseenat ɗin. Dan ita kaɗai ta shigo Daneen Ammarah na falo ta kasa shigowa. Bata san dalili ba kawai taji bazata iya ba, dan zuwan ma sai da Mammah ta tilasta mata harma yanda ta nuna ya bama Malikat Haseenat ɗin mamaki matuƙa dan kunya ce a bayyane kamar wadda zatai gamo da surukinta.

A hankali ta cigaba da gara kekenta cikin ɗakin idanunta na yawo kan Tajwar Eshaan da tun kallo guda da yay mata bai sake ba da Iffah da ke duƙunƙune a gado cikin bargon da ta sashi ya lulluɓa mata saboda rawar sanyi da takeyi. A gaban Iffahn ta dakata, a hankali cikin dattakonta da ƙasaita ta kira sunanta da kai hannu ta janye bargon data lulluɓe har kanta da shi. Ɗan zabura Iffah tayi, sai kuma tai saurin maida kanta tana hawaye. Tausayi yarinyar ta bata, dan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin wani halli. Batace komai ba ta juya kallonta ga Tajwar Eshaan da ke ɗan satar kallonsu…

“Barka da safiya Jaddah”.

Ya faɗa a taƙaice yana wani ƙara fuskewa abinsa. Itama sai tai kamar bata fahimci komai ba ta ce, “Barkan ka dai. Mike damunta haka jikinta zafi zau ga fuska duk ta kumbura idanu sun ɗashe yarinya duk ta fita a hayyacinta”.

Wayyo shikam ina ƙasa ya ɓuya ciki ko zai kuɓuta da ga bata amsar da bai ma san ta ina zai fara ba. Amma sai ya dake yana ƙara ɗan kauda kai gefe tsahon sakkani kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya motsa lips a hankali a gaɓar da ma ta gama fidda rai da samun amsa.

Kallonsa kawai Malikat Haseenat keyi, da jinjina murɗaɗɗen hali irin nashi mai cike da shegen miskilancin tsiya. Sai kuma ta janye a hankali ta maida kan Iffah dake raira kuka a hankali. “Niger (Sweetheart)” ta kirata a hankali. Da ƙyar Iffah ta iya amsa mata murya a ɗashe.

 

“Daure ki tashi zaune muga”.

 

Kwatanta tashin tai har sau biyu amma ta kasa, sai ma wani wahallen kuka da take saki saboda yanda zafi mai azaba ke ratsata. Ta shiga jujjuya kai da faɗin, “Jaddah bazan iya ba. Zafi kamar zan mutu”.

 

Idanu ya lumshe a hankali. Ji yake kukanta na wani irin sukar masa zuciya. Itama kanta malikat Haseenat ɗin wani irin tausayin Iffah’r ne ke ratsata. Ita tasan ba lalaci bane ko raki kawai. Dan zuri’ar su Tajwar Eshaan ɗin fitinannun mutane ne da indai mace taje hannunsu basa iya mata ta sauƙi. Shiyyasa mafi yawansu basa iya zama da mace ɗaya, sannan suna aure da wuri gudun faɗawa halakar zina duk da akwai bijirarru a cikinsu da kan ringa aikatawar. Amma ita a karan kanta ta daɗe tana mamaki akan Tajwar Eshaan da ya nuna baya buƙatar aure tun a shekaru fara girmansa, hakama yanda ya kai har shekarun da aka masa auren fari na sata jin waswasin ko yana neman matan banza ne ko baida isasshen lafiya. Dan tasan duk wanda ya kasance jinin zuri’ar wannan daula baya iya kauda kai ga mace irin hakan da ya nuna shi..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button