Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 8

Sponsored links

★A yanda dokin ya cika bargar da haniniya da fisge-fisge ya matuƙar tada hankalin masu kula da su. Iya kokari yi suke na ganin sun dakatar da shi daga ballewa saboda saninsa amma hakan ya gagara. Da yay wata irin mahaukaciyar girgiza sai ga zaratan mazan su biyar a ƙasa wanwar. Darewa a ka dingayi duk inda ya keta a cikin masarautar, yayinda hankalin mafi yawan hadimai ya tashi sanin babu mai iya dakatar da shi sai mai shi……

Cak ya tsaya daga yunƙurin shiga motar da aka tanada domin zuwansa falon da zaiyi zaman tattaunawa da yan jaridar duk da kuwa a cikin masarautar ne. Ko’a cikin barci yaji takun waɗan nan kofatan bazai iya manta mai su ba. A zabure jami’ai Da Gazi dake zagaye da shi suka zabura domin dakatar da ingarman farin doki da ko ga mai kallo ya san ya wuce tara irin ta gaba-da-gaba. Amma domin kare shugabansu a gare su tunkararsa dole ne koda tasu lafiyar bazata samu kariya ba. Ai girgiza ɗaya yay ya zubar da kusan uku da suka tunkaresa, wasu na ƙoƙarin sake tunkararsa yay wata irin turjiya, ya kwafuci ƙasa ya sake ƙwafuta yay girgiza mai haɗe da haniniya sai gashi gaban Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed.

 

Dole kowa ya dakata wajen ya ɗauki shiru na wucin gadi duk suna kallon ikon ALLAH. A hankali ya kai tattausan hannunsa a fuskar dokin ya shafa, haniniya ya sakeyi da ƙwafutar ƙasa ya girgiza jikinsa. Wannan al’amari ya matuƙar ƙayatar ga duk wanda ke wajen, duk da kuwa ba’a yau suka saba ganin irin haka ga dokin ba a duk lokacin da ya kasance tare da Tajwar Eshaan ɗin..

 

Cikin muryarsa mai tausasawa da tarin nutsuwa ya kema dokin magana yana shafasa a hankali fuskarsa da ƴar sakewa kaɗan sai dai ba murmushi ya ke ba. Hasalima sai mai lurane zai fahimci sassaucin fuskar tasa a zahiri. Ya kwashe tsahon mintuna huɗu da dokin, hakan ya bama duk wanda ke a wajen damar cigaba da satar kallonsa, wanda kuma aka kaima gulma na ƙoƙarin tururuwar fitowa da leƙe a maƙe. Cike da ƙasaitarsa ya damƙa dokin a hannun Sayeed Fayzul-haq, shi kuma ya shige motar da ke buɗe har yanzu. Da sauri hadimin ya maida ya rufe murfin kansa a rissine. Da ga haka motocin suka nufi inda za’ai zaman.

★Isar da saƙon shigowarsa katafaren falon ya saka duk wani mahaluki mai numfashi yin ƙasa da kansa. Daddaɗan ƙamshinsa shine abu mafi ɗaukar hankali a garesu da saka nutsuwar zuciya. Yayinda takun sawayensa masu tabbatar da ƙasaitarsa ke ɗauka da sauka da bugun zukatansu. A zahiri da baɗininsu cike suke da ɗokin kasancewa a tare da shi koda bazasuga fuskar tasa ba. Duk da kasancewar sa Shahan-shan mafi ƙarancin shekaru a cikin duk Shahan-shan da suka gabata a daular ruman kwarjininsa na razanar da su, dan ko makaho ya laluba zai bada amsar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed cikin jerin jaruman maza zaratan gaske koda basu ganin ainahin zahirinsa kuwa.

A hankali ya kai zaune saman kujerar da aka tanada dominsa cikin nutsuwarsa da sanyin da rashin ƙarfin jiki ya haddasa masa. Kallo ya dinga binsu da shi cike da nazarinsu kafin ya lumshe idanu da buɗewa yana jan ƙaramar iska ya fesar. Su Miran Jasim da ke biye da shi bayan an kai musu labarin fitowarsa babu shamakin da ke ɓoye zahirinsa suma duk zaman sukayi ransu yana ƙuna matuƙa, wasu kam ransu fari ƙal da abinda Tajwar Eshaan ɗin yayi. Kasancewar sun tsara abin a yanda sukazo bisa jagorancin wakilai ɗai-ɗai daga kowace jiha sai zaman ya kasance a tsare. Ko sau ɗaya a cikinsu babu wanda ya gwada iya ɗaga kansa ɗan kwarjininsa ya gama mamayesu tun kan su gansa, sai dai tabbatar da kammalawar zamansa ya sakasu sake gurfana gaishesa. An amsa musu da yawun Shahan-shan batare da shi yako motsa ba daga zaman ƙasaitar da yayi har sai da falon yay shiru.

Umarnin da aka basu na shiryawa ya saka su miƙewa musamman masu gyara camaras da tabbatar da abin ɗaukar maganarsu ya zauna yanda ya kamata a inda aka jerasu reras gabansa kaɗan. Kaɗan ya rage zukatan wasu su wantsalo da gasken gaske. Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed a zahirinsa, wannan fuskar da suka jima da mafarki da kulafucin son gani a bayyane ce a zahiri babu shamaki yau. Duk da kowa yay masa kallo ɗaya baya sake maimaitawa a ransu ayyanawa suke dole ya dinga kasancewa a ɓoye kam duk da cewa hakan al’adarsu ce, dan zasu iya cewa shine na farko a tarihi cikin duk Shahan-shan da suka gabata daya bayyana fuskarsa a zahiri. Abune da bai taɓa faruwa ba. Mafi yawancin al’ummar ƙasar ruman ƙyawawane duniya ma ta shaida hakan, sai dai fa a yau kam sunga inda ƙyawu yake na zahiri, ƙyawu irin wanda ko’a ƙasar ruman ɗin zasu ambacesa da ƙyawu ɗan gaske da ba’a iya ɗauke ido a kallo ɗaya ga mai shi…

Wannan firgici ba’a iya falon kawai ya kasance ba. A duk lungu da saƙo na ƙasar ruman ne dan tunda aka ɗora Camara ga Tajwar Eshaan komai ya koma live ga masu kallo da saurare kamar yanda ya bada umarni..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button