Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 72

Sponsored links

Ji kawai yay ɗan sauran ƙarfin da ya rage masa ya ƙarasa guduwa. Gaba ɗaya jikinsa da yay mata runfa shima ya ƙarasa saki. Miya rage kuma? Miya rage masa da zai faɗa akan wannan aljanar yarinyar yanzu kam? Taci nasara, kawai taci nasara…..

🥱 Iffah! Iffah! Anya ke ba aljanar da Shahan-shan ɗin yake ambata bace. Ni ma dai ƴar koran taki na sallama a wannan gaɓar.🚶

“Ashe abin kunyar da wancan wawan yayan naka ya aikata mana kenan yau a gidan nan?. Wai shi sai yaushe zai san ya girma ne? A haka yake tunanin mulkar jama’a ko gidansa bai iya adalci ba mtsowww!!”.

 

Fuska Miran Arshaan ya yatsine cike da rashin damuwar zagin da Ameera Haifah ɗin kema ɗan uwansa Miran Jasim. A hankali ya zuƙa karan haɗaɗɗiyar tabar da sai lokaci-lokaci yake ɗan sha shima ya fesar. “Kin kirani nan ne domin zagin wani ko yin abinda ya dace?”.

 

Tsaki ta ɗan ja tana balla masa harara, “Naga kaima zagin nasa kake ai. Abinda ya dace ɗin kuma ai duk dai a kansa ne. Dan kasan tunda wannan tsohon munafukin Sayeed Fayzul-haq ya sani shi da tsohuwar can sai wannan maganar taje gaban wancan ɗan ALLAH bani in raya gorin (Tajwar Eshaan take nufi🤭), yana sani kuwa kowa kamar ya sani ne, ga shegen yaron nan da kaifin basirar tsiya matsiyacin wlhy zai iya bin ta hanyar ya gano abinda yake fafitikar son ganowa dare da rana. Wlhy na tsani yaron nan shi da uwarsa, dan duk abinda ubansa yamun a kansa zan rama har sai naga baya numfashi a duniya zan huta”.

Saurin kallonta yay, Dan shi fa wannan tunanin ma baizo kansa ba yanzu tsabar abubuwa sun ma kansa yawa

 

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (35)

………Karan sigarin hannunsa ya ajiye a ƙyakykyawan ƙaramin bowl ɗin gabansa na glass “Ya akai banyi wannan tunanin ba, ya ALLAH”. Yay maganar yana miƙewa hannunsa duka kan sumarsa ya shiga cakuɗata. Shi dama akwai ruɗewa idan

 

abubuwa suka masa yawa. Harara Ameera Haifah ta balla masa tana faɗin, (Kai dama ai jaki ba komai kake fahimta ba, shegu biyu burina na cika na kawar da shegen yaron nan kuma bazaku sha ba ai, kubar ganin da taimakonku na shigo masarautar nan, bazaku sha da ga maidani abinda na za na yanzun). A zahiri kam sai ta saki murmushin yaudara. “Kaga zauna Shahan-shan ɗin gobe, kai daɗina da kai ruɗiyar masifa”.

“Bazaki gane ba Haifah, duk yanda kike zato da tsammanin hatsabibanci shegen yaron nan ya wuce nan. Wlhy yace ubansa bai iya komai ba akan taurin kai da shegen kaifi”.

 

“Duk kaifinsa da taurinsa mune ajalinsa shi da wannan ƴar iskar yarinyar mai bakin reza. Na rasa gidan ubanda suka samota sai kace ƴar ifiritan aljanu”. (Iffah 😂).

 

“To dama micece inba ƴar ifiritan aljanun ba. Kina gani har yanzu iya bincikenmu mun gagara gano inda tsinannun mutanen nan suke. Wai mu Barrister Akeem zaici ma amana bayan mun yarda da shi”.

 

“Nifa gaskiya bana tunanin haka, nasan waye Barrister Akeem batun yanzu ba, zaka tabbatar da yana da hujjar ɓoye kansa shima a duk randa ya bayyana kansa garemu. Ai tunda har ya bamu haɗin kan salwantar da iyalan Barrister Abdallah Aas da yake abokinsa dolene ya bada ƙafa. Kai dai mu cigaba da jiransa ɗin, Ni yanzu duk bama wannan ke gabana ba, wannan haukan yayan naka ne, sai kuma ita waccan kuna bibiyar lamarinta da gaske har yanzu shegen bakin nata na kulle dai ko?”.

 

Nannauyan numfashi Miran Arshaan ya saki, “Boka Barbushi baya aiki ya warware sai in da kansa ya warwaresa, amma duk da haka Inaga zan jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Zan ziyarce a safiyar gobe da safe”.

“Hakan ma yayi, ni bara na wuce dan naga asuba ma na gabatowa.” ɗan riƙota ya sakeyi yana wani ɗan murmushin da kai hancinsa jikinta, murya can ƙasan maƙoshi ya ce, “Ki ɗan ƙaramin lokaci mana, kwana nawa bamma sakaki a idona ba”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button